A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Muka fara revising ya junanmu gami da tambayoyi game da abubuwan da muka karanta, har zuwa lokacin da masu tsaron jarabawar suka shigo. Da misalin karfe tara kenan.
Jarabawar ta daukemu awanni biyu da rabi cur, kusan tare muka gama ni da Janan amma ta riga ni fita. Na mika takardar bakina dauke da addu’o’i iri-iri, idan nayi rashin sa’a jarabawar nan ta dawo min ban san ya zamu karge da Baba ba.

A bakin kofar wajen na sameta tana jirana, na amshi wayar hannuna, muka jera ni da ita hannu da hannu har zuwa cikin hostel. Allah ya taimaka yau sun daga mana shiga cikin asibiti har sai zuwa gobe. Muna ta tattaunawa game da jarabawar har muka shiga hostel din.
Muna shiga ta cire uniform din jikinta, nima na cire nawa. Na ciro mata rigar shan iska, doguwa mai wadataccen fadi, nima na saka shigenta, muka kwanta akan katifata, sai a lokacin na bata labarin Anty Sailu fa tana asibiti, ta jinjina lamarin tare da cewa zata kira ta mata sannu.

Ba karamin dadi naji ba da bata kara tado min zancen Yaya Bilal ba. Again, nan ma ta bani mamaki. Janan ba irin mutanen nan bane masu saurin sakin abu ba, idan ta sako abu a gaba ko kuma wata magana, bata saki don wasa har sai ta cimma nasara. Shi yasa yanzun nake ta kaffa-kaffa da ita, ban san ko me take tunani ba a cikin ranta.

Sai da muka yi sallar azuhur bayan mun koma mun kwanta, sannan na bi bayan sakonnin da Yaya ya turo min dazu, hannuna har rawa yake yi.
Na farkon cewa yayi; ‘Hey, you okay?’

Na biyun kuma: ‘Nasan cewa ba ta haka ya kamata in tunkare ki ba, nayi kuskure. Should’ve thought about it more kafin in tunkare ki ta wannan hanyar, saboda haka ne nake baki hakuri!’.

Sai kuma, ‘Baby, na san cewa kina ji a cikin ranki kamar ban kyauta miki ba, ko kuma wasa nake miki da hankali. Ina tabbatar miki da cewa ba haka bane, please let me explain myself!.’

Akwai kuma wanda na kula ya sake turowa nan da mintuna sha biyar da suka wuce: ‘Please baby, da gaske ba zan iya cigaba da zama a haka ba. Nayi kokarin ganin cewa na baki cikakken lokaci domin ki samu kiyi tunani akanmu, I know it’s sudden. But that’s it! I can’t do this anymore.. Let me see you again, please? I promise zan miki bayanin duk abinda kike son ji, kinji baby na?!’

Ina gama karanta wannan naji wani abu mai zafi ya daki zuciyata, idanuna suka fara min zafi alamun kwalla ta fara taruwa. Na lumshe idanuna tare da kwantar da kaina akan pillow. Yaya Bilal ya riga ya bata rawar shi da tsalle, koda yake tun daga farko dama bashi da wani chance a wajena, amma me yasa raina yake kuna idan na tuna cewa zamu rabu dashi har abada?! Me yasa nake jin kamar ina gab da rasa wani muhimmin bigire na jikina ba? Ko dai zan bi shawarar Janan ne, inyi rethinking wannan bakon al’amari?.
Nayi gaggawar girgiza kaina, inaa! Ba zai yiwu ba!.

A hankali na sake bude idanuna, har yanzu hasken kan wayata bai mutu ba. Na dinga scrolling sama ina kara karanta sakonnin da muka dinga canzawa a tsakaninmu, kafin in san ko shi din wanene. A da, da ban san ko shi din wanene ba, kawai ina jinshi acan kasan raina ne, yeah, ina son shi, kuma ina kaunar shi, amma yanzu dana san ko shi din wanene finally, sai nake ganin komi daban, at least yanzu idan ina tunaninshi zan ga fuska kuma zan ji murya sosai. Sai dai nasan koma menene nake ji game dashi, dole ne in manta dashi. Ko za’a yi me, nasan cewa ba zan taba amincewa da Yaya Bilal ba.

Saboda haka na kashe hasken wayar, na ajiyeta a kusa dani na rufe idanuna cike da fatan barci ya dauke ni a lokacin.

                         ***

“… Na’ilah?!”.

Da sauri na bude idanuna, Janan na zaune kusa dani tana kallona cike da yar damuwa a fuskarta. Na sauke idanuna akan agogo, naga har karfe hudu da rabi tayi. Na tashi zaune ina salati. Tace “har an kira sallah, ki tashi muyi mu leka waje mu ga abinda zamu lalubo na shan ruwa, yau anan zan sha ruwa”.

Na mike tsaye, ko don barcin da nayi ne? Jikina naji yayi min wani nauyi. Na tashi na dauki hulata na fita, idanun Janan a kaina. Nasan dalili, mafarkin da nayi ne wanda ta tashe ni a daidai lokacin da bana son tashi, daidai lokacin da nake kwadayi, kuma nake marmarin ganin wannan mutumi da duk duniya babu wani mahaluki da yake kada min sassan jiki kamar shi ba. Amma kullum anan nake tsayawa, ban taba ganin fuskarshi, muryarshi ma haka nan nake jinta sama-sama kamar ba a kusa dani yake ba. Wani lokacin ni nake tashi a karan kaina, watarana kuma sai ayi arashi wani ne a kusa dani zai tashe ni. Koma dai menene, na zubawa sarautar Allah ido ne kawai domin ni kam na kasa gane wannan abu.

Bayan munyi sallah, muka fita zuwa kasuwa muka sayo abubuwan da zamu bukata, muka dawo muka yi yam balls da kunun aya. Har muka gama shan ruwa da ita bata yi alamun sake tado maganar jiya ba, don haka naji na fara relaxing. Cikin annashuwa kamar yadda muka saba muka sha ruwanmu, na tashi na rakata ta hau mota na dawo, na tattare kayan da muka bata na ajiye a inda nake tara kayan wanke-wanke, nayi sallar isha’i.

Daga nan common naje nayi kallo. Karfe goma na dawo daki. Na samu Maimuna da Esther a daki, na musu sannu suka amsa nayi shirin kwanciya barci na kwanta.
Wani irin sad feeling da naji ya rufe ni a lokacin, da ace da ne, da yanzu muna nan muna zuba soyayyarmu ni da Muhammadu na. Me yasa Yaya Bilal ne zai zama Muhammad? Mai yasa ba wani mutum ne daban ba, wanda bashi da mata daya balle mata har biyu? Me yasa? Wai me yasa abubuwa suke zo min ne a hagunce?
Daren ranar yau dai da kuka shabe-shabe nayi barci.

☆⋆24⋆☆

Ni a karan kaina nasan cewa idan nace bana yin kewar Yaya Bilal to karya nake yi, ina kewar shi fiye da tunanina. Sai dai wani sashe na zuciyata yasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi. Ko zan mutu, ko zuciyata zata tsattsage saboda damuwa, zama da Yaya Bilal ba zai taba zama maganin hakan ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin na danne duk ma wata kewa, so da bege da nake ji game dashi. Nasan cewa na dan lokaci ne, nan da lokaci kadan zan daina.

Sai dai duk wanda ya ganni, yasan cewa ina cikin damuwa. Idanuna kadai sun isa shaida, saboda bana samun barci mai yawa. Ko nayi, saboda tsananin sanya maganar Yaya Bilal da matanshi a cikin raina, haka zanyi ta mafarkinshi. Watarana ma har da matanshi, wani lokacin kuma barcin ne ma gabadaya baya zuwa.

Yanzu ma muna zaune a cikin ward ni da Janan da wata Aisha, a ranar alhamis kenan. Janan da Aisha ne suke ta hirar su, ni kuwa hankalina yana kan wata calender dake rataye a wajen. A zahiri idan ka kalleni, zaka yi tunanin jerin magungunan dake cikin takardar nake karantawa ko kirgawa, amma a hakikanin gaskiya hankalina ma kwata-kwata baya tare dasu. Tunani nake, tun wannan text din da Yaya Bilal yayi min ranar litinin, har yau bai sake kirana ba, kuma bai sake turo min wani sakon ba. Ta wani bangaren naji dadin hakan, so nake ya barni, ya kyaleni, idan ma da hali ya manta dani. Duk da cewa nasan har abada zan dinga kallonshi da wannan maganar, ba zan taba mantawa ba, sai dai in binne abin acan karshen bangon zuciyata.
Ta wani bangaren kuma tunani nake, dama kirarin da yake akan cewa yana sona duk kuri ne da cika baki? Har ya manta dani kenan? A yadda yake nunawa dinnan, nayi zaton zai zage damtsensa ne har sai inda karfinsa ya kare. Amma dana fara irin wannan tunanin, sai inyi gaggawar katse kaina, idan ma ya ci gaba da bibiyata babu abinda hakan zai sa sai ma kara min ciwon kai da damuwa da hakan zai yi. Don haka gara ma yaje can ya karata da matanshi ya fiye min alkhairi. Shima wannan kuri ne kawai da zuciyata take yi, can can kasanta, tana fatan ace ba haka bane.
Kai wasu lokutan sai inji da ace ana cire zuciyata a sake sabuwa, da na garzaya zuwa ko’ina ne na canza tawa. Komi nisan wajen kuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button