A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

“Lafiya?”. Na tambayeshi a sanyaye. Yanayinshi bai yi kama da wanda yayi tattaunawar arziki da surukin nashi ba.

Ya girgiza kanshi kafin ya dago kai ya kalleni, “ban sani ba nima, kawai dai Ameerah taje musu gidan da safiyar yau, wai tunda taje take kuka bata ce komi ba. Yanzu dai Babanta yace zai zo nan ya sameni, zamu hadu anjima kadan a Will’s Park”.
Na dan zaro ido, kafin na gyada mishi kai.

Nasan ko na koma na kwanta ma babu wani barci da zanyi. Don haka na tashi kawai na shiga bandaki na dauraye bakina. Na tafi na dora girkin safe.

Abincin sai tsakurar shi kawai aka yi. Karfe daya Yaya ya tafi ganin mahaifin Ameerah. Bai dawo ba sai gab da magriba. Fuska babu yabo babu fallasa haka ya shigo gidan. Ameerah da take girki, ta mishi sannu da zuwa ta bishi zuwa dakinshi.

Sai da dare muna falonshi mu duka, sannan yake bamu labarin abinda ya faru.
Mahaifin Ameerah dai yaki yarda, ko kuma ince yaki daukar laifin da diyar tashi tayi. Daga karshe ma sai ya koma accusing din Yaya kan cewa dama baya kula mishi da diyarshi yadda yakamata, ya maidata ta zama koma baya a cikin dangi. Tafi-tafiya ma sai yace yana bukatar takardar sakinta kawai. Duk yadda Yaya yayi wajen ganin cewa ya fahimtar dashi, abin yaki yiwuwa. Shi a ganinshi abin bai kai ga haka ba, sai ya gangaro yace idan bai sakar mishi diyarshi ba zai iya maka shi a kotu. Sai da ya rubuta mata saki daya sannan ya warci takardar ya kara gaba.

Daga ni har Raheemah babu wanda bai jijjiga da jin haka ba. Muka jinjina maganar sosai, daga karshe nayi fatan Allah yasa hakan shi yafi alheri.

*

Kwana biyu gidan shiru, ita kanta Raheemah ta kame kanta ta kai gefe. A hankali komi yazo ya wuce, ya zama tarihi a wajenmu. Rigima bata kuma tashi ba, kamar hakan ya zamewa Raheemah abin tunatarwa da darasi. Tsakanina da ita sai kallo kawai, ba uhm ba uhm uhm. Habaice-habaice da bakaken maganganu da take yawan jifa na dashi a kullum rana ta Allah babu gajiya, muddin muka hadu sau daya ko sau goma a rana sai an jefo shi kamar wani abin arziki, yanzu ta daina kamar anyi ruwan sama an dauke.

Ko lokacin da tafiyarmu umara yayi, bayan sati biyu da tafiyar Ameerah kenan. Lokacin mun kai azumi na hudu kenan. Yaya yayi mata maganar zamu tafi ranar da aka dauki azumi na takwas, mu tsaya mu kwana a Kaduna, washegari mu wuce Katsina mu kwana. Ranar da aka kai azumi na goma zamu wuce Umra. Daga fari nayi zaton zata hau yin kalar dibar arzikin da tayi kamar da, amma ga mamakina maimakon tayi wani abu, kawai sai gyada kai da tayi ta mana fatan a dawo lafiya.
Shi kanshi Yaya sai da ya nuna alamun yayi mamaki, kafin ya girgije. Yace to tayi list din abubuwan da zata bukata kafin mu dawo. Nan ma tace babu komi.

Wannan karon kam sai da mamakinshi ya fito fili, yace “babu?”.
Tace “to duka-duka ko sati daya fa ba’a yi da kawo kayan provision ba. Bamu yi wani amfanin azo a gani da kayan ba”.
Yaya yace “to shikenan”.

Ranar da zamu tafi, haka ya dauko naira dubu dari cif ya dire mata a gaba. Yace tayi hidimar sallah. Tuni dama tare aka kawo mana kayan sallah da kayan kamun azumi. Manyan atamfofi da leshina, ya kuma hado mana da kudin dinki. Iyayenmu suma haka ya aika musu atamfofi da shaddoji har da kudin dinki. Hatta su Malam ma sai daya aika musu.
Duk da nima sai dana aika musu, da su kayan kamun azumi. Suka yi ta mana godiya da sanya albarka kuwa.

Kamar yadda yace, Kaduna muka tsaya muka musu shan ruwa. Janan ma ranar a gidan ta sha ruwa da yake Almunta baya gari. Muka yini muna hirar yaushe gamo. Da dan yaron cikinta ma kuwa, duk da taki yarda da zancen tana ta min kwana-kwana.
Su dukansu sunyi mamakin abinda ya faru da Ameerah. Abu ne na Ala wadai, amma su dukansu babu wanda yayi mata addu’ar banza ko yayi wata maganar da bata dace ba, sun dai jinjina abin, kafin suka yi addu’ar Allah ya kara shiryata da duk sauran ire-irenta.
Da yake da kayan sallah ta na taho, washegari kafin mu wuce zuwa Katsina, muka je wajen telarta ta auna ni, muka bar kayan dinkin anan.
Muna komawa gida muka wuce Katsina.

                         *☆⋆48⋆☆*

A gida muka sauka, da yake tare da Balarabe muke, Yaya ya tsaya suka gaisa da Baba, anan ma suka sha ruwa tare da Baban da Balarabe, sannan suka wuce masauki.
Tarba mai kyau muka samu wadda ban yi zatonta ba, ba daga Baban ba, ba daga matan nashi ba, ba daga yaran ba, kowa ya nuna farincikinshi da ganinmu har abin ya bani mamaki.

Sai bayan tafiyar Yaya sannan na fahimci cewa da wani abu a kasa. Tunda muka je, Aliyu da Ramata suna daki, tun lekowar da suka yi suka mana sannu da zuwa suka koma daki, basu kara lekowa ba.
Yanayin yadda na ganta ya tsorata ni, tayi wata irin rama, sai girman shekarunta ya kara fitowa.
Bayan mun kebe a dakin Maryam inda nan na saba sauka, na tambayata abinda yake faruwa da masu gidan. Abinda ta fada min ya girgiza ni.
Wai Aliyu aka kama yana saida ganyen Iblis. Jiya yan sanda suka zo unguwar aka kama gungun yan unguwar da suke shaye-shaye, ga namakinsu sai aka hada dashi. Har wajen karfe ukun dare suna police office din wai, da kyar aka bada shi.
Na kama baki ina jinjina kai kamar zanyi ihu, “garin yaya haka?”, na tambayeta, “ban sani ba”, itace amsar data bani.

Muna nan a dakin nata muna maida magana, Awwal ya leko yace in je dakin Baba yana kirana. Na dauki hijabita na saka na tafi. Shi kadai na samu a dakin nashi. Na zauna a kasan kujera, muka sake gaisawa dashi a nutse ba kamar ta dazu ba da aka yi ta a tsaitsaye.

Kafin ya daga baki ya sake magana, sai ga Alawiyya da Ramata sun shigo dakin kusan a lokaci guda, duk suka samu waje suka zauna. Na kurawa matar da tunda na mallaki hankalin kaina ta hana ni shakar numfashi mai dadi a rayuwata. Akwai wani lokaci a can baya, da ko sautin muryarta naji tana tashi, sai naji faduwar gaba ta ziyarceni. Akwai wani lokaci da zan mata kallo daya, inji babu abinda nake so da kaunar sake gani kamar in daga idanuna in ga gawarta shimfide a kasan.

Sai dai a yanzu da nake sake dubanta sai naji babu wannan tsoron, babu wannan tsanar, sai tsananin tausayinta daya lullube ni. Hakan kuma baya rasa nasaba da yadda naga ta makure a gefe kamar bera a gaban mage, kanta a kasa yake tunda ta shiga dakin, bata yi gigin daga ido ta kalli kowa ba.
Ba’a jima ba, sai ga Aliyu ya shigo shima, ya nemi waje can kusa da Ramata shima ya makure.

Sai da kowa ya nutsu sannan Baba yayi gyaran murya. Hakan yasa duk muka maida hankulanmu gare shi.
Ya fara da cewa “Ke Na’ilah ke da baki gida, ke kadai ce anan da baki san abinda yake faruwa ba…”, nan ya zayyane min duk abinda Maryam ta sanar dani.
Baba ya cigaba da cewa, “saboda haka na yanke shawara, ba zan cigaba da zama da tantirin yaro kamar Aliyu a gidan nan ba. Ba zai lalace ba, kuma daga baya yazo ya lalata min yara, ba zai yiwu ba. Don haka nace mishi ya fita ya bar min gida na tun a jiyan. Ban fada maka kada ka kuskura in dawo gidannan in gan ka ba?”.

Aliyun bai ce komi ba sai kara lafewa da yayi a jikin Mamanshi yana shesshekara kuka, yayin da Ramata din take share hawaye itama.

Alawiyya ta wurwusa ta matsa kusa da Baba, tace “Alhaji kayi hakuri da wannan magana da zanyi, amma matakin daka yanke kwata-kwata bai dace ba, ina ga da dai ka sake shawara”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button