A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Washegari muka je asibiti muka yi bankwana dasu. Daga nan muka yi bankwana da Janan, itama ranar Lahdi zata tafi Kaduna wajen Umma. Ni da ita kuma sai idan mun dawo hutu.
Na dawo hostel na karasa shirya kayana, wadanda zan bari anan kuma na hade su waje daya tsaf na rufe da mayafai saboda kura. Na share waje na zauna ina jiran kudin mota.

            NA'ILAH!

Mahaifana su duka biyun, asalin yan garin Gashua ne. Mahaifina, Alhaji Al-Hassan Hannafi, cikakken haifaffen garin Gashua ne. Iyayenshi hausa/fulanin dake cikin garin ne, duk da cewa sun rasu tun ma kafin a haifeni, sai sauran dangi na nesa-nesa kawai. Yayin da mahaifiyata, Yana, ta kasance ruwa biyu. Mahaifinta Barebari ne, mahaifiyarta kuma Shuwa Arab.
Kakana Bako Audu, shahararren malami ne, Kakata Fatima da muke kira da Fatsu, ta kasance mai sana’ar sake-saken kaya, a cewarta tun tana budurwa.

Mahaifiyata ta kasance kyakkyawar mata, fara, doguwa, mai dogon hanci da dogon gashi da dara-daran idanu masu tsari. Babu abinda ta bari na Fatsu. Allah Ya hore mata hakuri, Kawaici da kawar da kai. Aurenta da mahaifina ya kawo yar matsala a tsakanin danginsu ta fannin mahaifiyarta, su a sonsu ta auri dan uwanta ta fannin uwa, ko Barebari, amma ta kafe. Sai kuma matsalar rashin aiki, don a lokacin da suka yi aure, ya gama kammala degree dinshi akan banking and finance, amma bai samu aiki ba. Jajircewar Bako ce kawai tasa aka yi auren, suma kuma dangin nata suka hakura.

Bayan auren nasu da kadan, ya samu aiki da bankin GT, anan cikin Gashua din, ya fara zuwa aikinshi.

Yaya Mudatthir shine ‘Da na farko a wajen iyayenmu. Shekaru biyar cur ya bani.
Yawancin rayuwar yarintata a gaban su Fatsu da Bako nayi ta. Ba kamar Ya Mudatthir daya dauko kamanni da suffofi da halayen Mama kamar tayi kaki ta tofar, ni babu abinda na dauko nata sai yanayin idanuwanta da kuma dogon sassalkan bakin gashinta. Bayan haka, gabadayana Bako Audu ce. Ina da tsayi na daidai-wa-daida, da zubin halitta mai daukar hankali. Shi yasa bana shiga mai fitar da surar jiki. Kalar fatata baka ce, wasu kuma su kan ce wankan tarwada. Ko ma dai wace iri ce, ina jin dadi da alfahari da kalar fatata. Kalata mai sheki ce, sannan fatata mai taushi ce.

A halayen Mama kam, zan iya cewa tsafta da wasu halayen na dauko nata. Hakuri na kadan ne, sannan bana daukar wulakanci ko kadan, ko daga wajen waye kuwa. Bako ya kan ce shi duk cikin danginsu bai ga mai hali na ba, zafin kai, kafiya da taurin kai. Ina da rikakken ra’ayi, idan nace zan yi abu, to zanyi. Idan kuwa nace ba zan yi ba, mai canza min wannan magana kam sai ikon Allah.

Munyi zama mai dadi da iyayenmu, a dan abinda zan iya tunawa na rayuwarmu da wanda Mama ko Ya Mudatthir suke bani labari, Babanmu ya so mu, mutum ne mai son iyalanshi da kuma kyautata musu. Duk da cewa bashi da wani hali na azo a gani, amma rayuwarmu Alhamdulillah, babu abinda muka nema muka rasa.

Wannan kafin ya auro bakar ashana Ramata kenan. Lokacin da aka yi auren, Ya Mudatthir yana makarantar maza ta kwana a cikin Yobe. Ni kadai ce a cikin gidan, sai su Mama.

Tunda aka yi auren wannan, muka nemi walwala da kwanciyar hankalinmu muka rasa. Muka nemi Babanmu, Mama ta nemi mijinta, duk muka rasa. Rayuwar gidan ta koma kadaran-kadahan, yau daci gobe b’auri. Babu wani armashi. Ance wai ba’a kure mai hakuri, amma ni na gani akan idanu na, ranar da aka kure hakurin Mama a gidan nan, ranar da ta daga baki tace hakurinta ya kare.
Ranar ce Baba yasa belt ya zane mu ni da ita a tsakiyar gidanshi, akan naman kaji.
Ya kai mata nama ta soya, aka nemi naman a dakinta aka rasa. A cewarshi, satar nama take mishi idan ya kawo, dama kullum idan ya kai nama a soya sai ya ga babu wani bangare.

Mama tace “haba Malam, in rasa abinda zan daukar maka a gida sai nama? Tunda muke zaune da kai, na taba daukar maka abu ba tare da saninka ba?”.

Budar bakin amaryar Baba sai cewa tayi, “kenan kina nufin ni na dauki naman ko kuwa me?”.
Mama tace “ni ban ce ba, amma haka bai taba faruwa tsakanina da mijina ba, sai da kika zo!”.
Kawai ba sai mata ta dora hannu aka ba? Ta hau ihu, tana kururuwa, ita wallahi ba zata yarda ba, ance mata barauniya, zata bar wa Babanmu gida, sai yaci gaba da zama damu tunda yana zaune a gabanshi aka zageta bai ce komi ba.
Daga nan sai saukar duka kawai Mama taji, nayi tsalle na rungumota. Bai damu ba, ya hada mu mu duka ya mana lilis, kuka ranar haka muka shiga daki muka sha, babu mai lallashi.

Daga ranar dai bamu kara ganin nama a idanunmu ba, an haramta mana shi, duk wannan bai dameni ba, sai ganin an fiddo kwanon da Mama ta zuba naman da aka nema aka rasa daga dakin matar Baba, da tsakiyar ranar Allah Ta’ala. Babu kunya balle tsoron Allah. Wani karin abin haushi ma, da naje na yiwa Baba maganar, saboda Mama taki zuwa ta fada mishi, wai bata son wata rigimar ta sake tasowa, sai ya hau fadace-fadace, abinda na kira borin kunya.

Daga ranar muka kullata da ita. Ban kara ganin idanunta da kwalli ba, ban sake kallon kanta da gashi ba, ban kara mata magana cike da ladabi ko girmamawa ba.

Shekaru shida da karin auren da Baba yayi, shekaru uku da muka rasa walwalarmu. Muka yi rashin da har yau bamu samu mun cike wannan gurbi ba. Mama ta rasu wajen haihuwa. Nakuda ta kamata, cikin dake jikinta yana wata takwas da yan satika a lokacin, haka ta rasu, bata kai ga haihuwar abinda yake cikin nata ba, Allah ya karbi ranta. Munyi kuka, kuka ba kadan ba, Allah kadai yasan tashin hankalin da muka shiga ciki a lokacin.

Muna tsakiyar karbar ta’aziyar Mama, muna cikin wannan yanayi na jimami, tashin hankali da kunar zuciya, kwana biyu kenan da rasuwar mahaifiyata, har zuwa lokacin ina jin zafin rashinta kamar a lokacin ne hannunta ya silale daga cikin nawa, babu rai. Sai ga Ramata ta fito daga dakinta, taci kwalliya ta sha gyale sai zuba kamshi take yi, tana rike da hannun Aliyu dan data haifa dan kimanin shekaru biyu, Yayarshi Maryam mai kimanin shekaru biyar tana binta a baya. Babu wanda ta kalla a cikin yan karbar gaisuwa, ta tafi wajen bikin kanwarta. Da yake duk dai anan cikin unguwarmu suke dama, layi daya ne a tsakaninmu, muna iya jiyo sautin karar kidan da suka saka na biki kamar a tsakiyar gidanmu aka sa kayan.
Har yau dake motsi, matar nan bata yi min gaisuwar rasuwar Mama ba.
Har yau kuma, ina jin zafin hakan, sai dai idan ban kalleta ba.

Ita ta gwada min cewa kishiya ba karamar masifa bace, kuma kishiya, ba mutuniyar arziki bace, shi kanshi kishin, ba abu bane mai dadi. Na fara neman tsari da kishi irin nata, a ganina bashi da amfani. Da wannan tunanin, na girma na tashi.

Rayuwar dai gata nan sai godiyar Allah. Bayan yan gaisuwa sun watse, gida ya koma sai ni sai ita don Yaya ma ya koma makaranta saboda jarabawa, sai na kasa zama a gidan. Saboda haka na kwashi kayayyakina na koma wajen Fatsu. Na dauki lokaci mai tsayi a wajensu, kafin in koma gida.
Kafin in saba da sabuwar rayuwar wannan na jima.

Da rayuwa nayi mai dadi, ruwan wanka sai an kai min bandaki, abinci sai an zo ance min in ci, makaranta sai an zo an ce min in tafi, kayan makaranta sai an wanke an goge min. Amma yanzu wadannan duk sun zama tsohon tarihi. Abinci sai na je na nema, an wulakanta ni kamar ba gidan uba na ba. Kai sai da ta kai ta kawo, sai kannenta sun je gidan sun ci abinci, sannan za’a bani sauran inci.
Kullum ina hanyar gidan su Bako, cin abinci, kullum. Na fadawa Baba ya fi sau shurin masaki, ko maganar bai taba mata ba. Ni kuma na gaji.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button