A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ummah ta shigo dakin da sauri, su Yaya Hafiz sune manyan mazan gidan. Shine na farko, suna ce mishi Babba saboda sunan mahaifin Baban Yara gareshi, sai Yaya Auwal, Yaya Haneef da Yaya Kabeer. Janan itace take bi musu, sai Harira, Firdausi da kuma auta Faisal, kanin Janan ne. Shekarunshi sha daya yanzu. Yaje gidan Yaya Hafiz hutunshi na sallah Abuja shi yasa bamu hadu dashi ba.
Karamar walima ce suke hadawa, a lokaci irin wannan, duk suna taruwa a gidan duk da kasancewar suna garuruwa mabanbanta wajen aikinsu duk cikinsu Yaya Haneef ne kadai yake zaune a Kaduna. Ina ga saboda kara karfafa zumuncinsu ne. Ummah ce akan hidimar hada musu abincin da zasu ci, shi yasa tun dazu ta kasa zaune tsaye ita da Yaya, mu kanmu tare damu aka yi aikin abincin da rana, sai bayan mun gama ne sannan muka yi wanka muka shirya.

Tace “wai dama kuna nan a zaune kuka barmu da aiki? Ku taso maza-maza aje a shirya wajen can, har sun fara zuwa”.
Firdausi tace “Ummah ai kece da kin daukar shawara wallahi, sai da Yaya Babba yace za’a dauko wadanda zasu kula da hidimar nan, kika ce a’ah, sai anjima kuma kizo kina ta jajen ciwon kafa da baya!”. Su Janan suka kwashe da dariya, nayi dan murmushi ina girgiza kai.

Ummah ma dariyar tayi, ta wa Firdausi dakuwa, “karbi nan ja’irar yarinya kawai. Da karfina da lafiyata sai in ki hidimtawa diyana? Idan suka dauko yan aiki ni ina zaune, to meye amfanina kenan?”.
Harira tace “ki huta mana Ummah, muma kinga da yanzu ai bamu tashi daga zaman nan ba!”.
Ummah tace “wai zaku taso ko kuma sai na zo na tada ku?”. Babu shiri muka tashi gabadayanmu, muka bar Umaimah a falon.

Can bayan gidan inda aka ware musu kicin dinsu na gargajiya muka wuce tunda acan ake aikin. Akwai makeken kicin daya sha kayan zamani na yayi, amma ya zama na kwalliya kawai. Saboda basu cika amfani dashi ba, idan kaga matan gidan a ciki sai dai idan karamin abu ya kaisu, dafa ruwan zafi ko kuma wani abu dai. Yaran gidan ne ma suke amfani dashi.

Tuni an riga an zuzzuba komi a cikin abinda ya dace, saboda haka muka fara daukar kayan tare da wasu daga cikin yan aikin zuwa sashen maza. Babban falo ne sosai daya saitin manyan kujeru, dinning room shima babba, sai kuma dakuna. A dinning room din muka shirya komi, wasu daga cikinsu suna falo suna hira, wasu kuma suna waje yayin da wasu suke can kofar gida.
Muka shirya komi da zasu bukata, hatta da cokali, drinks da ruwan sha sai da muka ajiye komi sannan muka bar wajen.
A cikin yan hirar falon muka hango Yaya Bilal da Yaya Jameel a zaune, suna ta hirar sports da Yaya Auwal. Yawan zuwa yasa suka saba da yan gidan musamman mazan kasan zumunci irin na maza, shi yasa in ka gansu kamar yan uwa.
Zamu wuce Yaya Jameel ya kira Janan, mu kuma muka yi gaba. Can ta biyo bayanmu da kudin barka da sallah wai inji shi. Yau kam barka da sallah da muka samu daga yan gidan, da baki masu zuwa gidan Allah kadai yasan iyakarta. Ban taba zuwa sallah gidan ba sai wannan karon, shi yasa abubuwan duk suke zuwa min a mamakance.

Daga nan makotan su Ummah muka wuce, kannen Al-Mustafa suka zo muka hadu dasu ana ta cafta da kashe flashes din hotuna, kamar kada yinin ranar ya kare. Bamu samu kanmu ba sai da dare.

Muna falon Yaya da dare, hayaniyar gidan ta ragu kowa ya tafi gida, wasu kuma sun nemi makwanci. An gyara ko’ina ya fito fes, yana ta kamshi.
Janan ta ritsa ni da tambaya akan abinda yake damuna, nace mata babu komi.
Tace “wai karamar yarinya kike son maida ni ne? Tun da safe fa a haka kike, kina da wanda zaki gayawa matsalar ki ne bayan ni?”. Ina shirin bata amsa da wata babu komi din, Firdausi ta shigo falo hannu dauke da babban tray da aka hada fruit salad a ciki. Dama shi muke jira, don haka duk muka sauka kasan carpet din dakin muka zauna.

Shiru babu wanda yayi magana tunda muka fara ci, sai talabijin da take ta faman aiki kawai duk da ba kallon ba muke yi. Firdausi ce ta fara sako hirar, cikin alamun gulma tace “ni fa nayi zaton Anty Ameerah zata tsaya ne anan, ko kuma tazo yau”.
Da yake ta Kaduna suka sauka, sai da suka fara biyowa ta nan a jiyan. Gabadayanmu munyi zaton anan zasu zauna, har Ummah ta fara maganar azo a gyara musu daki, sai kuma suka ce wucewa zasu yi, amma shi Yayan zai dawo yau. Babu wanda ya tambayesu dalili.

Janan tace “lallai ma, wasa kuke yi da Anty Ameerah wallahi. Jiyan ma ganin idon Yaya ne yasa tazo, da ita kadai ce wallahi ko yace tazo ba zata zo ba”.
Firdausi tace “amma dai kinsan tafi Anty Raheemah ko? Na tabbata ko tare suke da Yaya ba lallai tazo nan ba”.
Harira tace “kinsan ai tunda Ummah ta hana aurensu da Yaya Bilal daga farko, take kulle da ita. Amma ni nafi son ta akan Anty Ameerah wallahi, bata da kirki ko kadan!”.

Janan ta gyada kai cikin amincewa, yayin da Firdausi ta jefa mata harara, da yake shekara daya ce a tsakaninsu, kusan kansu tsaya, zasu iya yin sa’a da Maryam. Tace “Lallai ma baki san kirki ba, ke ni fa da mutum ya dinga gwada min mutunci saboda ganin ido, gwanda muyi ta zuba rashin mutunci dashi nasan dama can ba so na yake yi ba!”. Kafin kace me! Muhawarar ta koma kan wanda aka fi so tsakanin matan Yayan. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya. Ni kam ina gefe, ina zuba musu dariya idan wata ta fadi abin ban dariya.

Yaya ta shigo falon, muka yi tsit muna kallonta. Tace “idan kuka kuskura daya daga cikin Yayanku yaji wannan magana sai ya bata muku rai. Ina ruwanku da rayuwarsu? Ba tasu bace ba? Kuma kuji da taku mana!”. Ta shige dakin barcinta.
Muka bita da kallo har ta shige, hirar dai ba’a daina ba, dorawa aka yi daga inda aka tsaya sai dai wannan karon cikin yin kasa-kasa da murya.

Firdausi ce mai cewa “ni wallahi wani lokacin har tausayi yake bani, kamata yayi ace zuwa yanzu ya samu yayi settling a waje daya, da matanshi da ‘ya’yanshi. Amma ace kullum yana hanyar Abuja, Kaduna da Zaria? Baya gajiya ne wai?”. Duk maganar da suke yi sai lokacin na gyada kai cikin nuna amincewa, ni kaina ina mishi wannan tunani. Sai dai a ganina, hakan duk shi yaso. Kasan cewa matan nan a karkashinka suke, to meye na zama kana rara-gefe akan tituna kamar wani mara galihu? A ganina idan ya nuna musu karfin ikonshi na mijin da yake aurensu, a sukwane zasu bishi.

Harira tace “ni kaina wallahi ina tausaya mishi, ko meye mafita a rayuwar aurenshi?”.
Janan tace “aure kawai ya kamata yayi. Ya samu wata rikakkiya da tasan sirrin rayuwa ya aura”. Suka fara gyada kai da sauri.

Kofar da aka turo aka shigo yasa muka maida kanmu can. Yaya Bilal da Yaya Jameel suka fado falon, jin mu kake yi munyi kus, kamar ruwa yaci mu. Har suka zauna akan kujerun falon. Yaya Jameel ya kallemu cikin murmushi, “gulmar me ake yi ne?”.
Da sauri muka hau girgiza kai, Firdausi tace “laa, babu komi Yaya. Kawai hira ce muke yi!”. Yaya Jameel ya kwashe da dariya.

Cikin yayun biyu, shine mai fara’a da faram-faram, yafi Yaya Bilal sakin fuska nesa ba kusa ba. A sauran halayya ma suna da banbancinsu, duk da ko a kamanni ma suna da banbanci. Shi Yaya Jameel yafi kama da Ummah da Janan, daka gansu shi da Janan kasan kaga yan’uwa. Shi kuwa Yaya Bilal ina tunanin ko mahaifinsu ya dauko, saboda kamanninsu da Ummah ba wai wani can bane. Sai dai kawai abubuwan da ba’a rasa ba, wanda haduwar jini yake haddasawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button