A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Da ranar girkinta ta zagayo, sai naci kwalliyata ta gani ta fada da safe, English wears mini skirt da wata vest, na gyara gashin kaina ranar ko hula ban saka ba, na yiwa dakin Yaya tsinke. Na samu gefen gado nayi daya kan daya, har tazo ta sameni anan, abin ya bata mamaki, amma bata yi magana ba.
Da dare ma da ya dawo haka ta faru, naje na musu zaune har dare ya tsala yadda ta saba yi min.
Zuwa karfe goma ta wani tashi tana mika, cibiyarta tana nunawa ta cikin half vest din data saka, tana wani fari da idanu da rangwada, tace “baby, muje mu kwanta ko?”.

Yaya da yake shan dariyar hirar da nake mishi akan kiriniyar dasu Auwal suka sha lokacin da suna yara, ya kalleta yace “kiyi gaba, gani nan”.
Ta turo baki cikin jin haushi, amma bata ce komi ba, ta shige uwar daka.
Muka kuwa cigaba da hirarmu, har sai da ta sake lekowa ta mishi magana, wai ai ita ta kasa yin barci saboda baya kusa da ita, lokacin karfe sha daya ta kusa.

Ina dariyar mugunta a ciki, nace “Yaya kaje ka kwanta mana, kasan fa gobe akwai aiki”.
Yace “ke fa?”.
Na girgiza kai, “bana jin barci, kaje ka kwanta abinka, idan na gama barcina zan je in kwanta. Sai da safe…”, na dan juya ina kallon Ameerah da take tsaye a jikin kofa har lokacin, nace “sai da safe Anty Ameerah!”.
Ta hadiye wani yawu da nafi kyautata zaton na takaici ne da bakin ciki tace “Allah ya tashe mu lafiya”, ta juya cikin dakin. Yaya ya bani peck a kumatu tare da dukawa ya shafa cikina, sannan ya min sai da safe ya bi bayan matarshi. Na bishi da kallo ina murmushin mugunta. Matarshi tayi tsamnanin taci bulus ne? Ashe kuwa tana da sauran aiki a gabanta, domin kuwa ba’a buga irin wannan wasan da ni.

Washegari ma abinda ya faru kenan, hakan kuma yaci gaba da faruwa na wani dan lokaci.

Ranar Alhamis girki a hannuna yake. Tun da na dawo daga wajen aiki, nake shirya abincin dare. Dambun shinkafa nayi, mai kyau, na yanka hanta, carrots, kabeji, da sauran tarkacen veggies a ciki. Nayi sauce itama da na wadatata da su nama da kifi. Nayi lemun kankana da lemun zaki wanda na dan diga lemun tsami da zuma a ciki.
Lokacin dana gama girkin, yamma tayi. Don haka na bar miyar akan wuta domin ta karasa yi, na tafi dakina inyi wanka.
Ina cikin yin wankan naji dawowar Yaya daga wajen aiki, jin ina yin wanka yasa ya wuce dakinshi.

Daga bandakin na dauro alwala saboda lokacin sallah yayi. Na koma duba miyar, na ga har yanzu da sauran ruwa a cikinta, abin ya bani mamaki kwarai. Zan iya rantsewa akan cewa ruwan da na bari dazu bai kai haka yawa ba. Amma sai ban kawo komi a cikin raina ba, na kara rage wutar na koma daki domin inyi sallah.

Ina kan abin sallar, Yaya ya dawo daga masallaci, daga ganinshi kai tsaye dakina ya shigo. Na dago ina kallonshi cikin murmushi, “baby abinci… Abinci baby…”. Ya fada a dan gaggauce, ya juya ya fita.
Na tashi tsaye ina dan murmushi, wato yau da yunwa ya dawo kenan. Na cire hijabin jikina na tafi kicin da niyar zuba mishi abincin.

Miyar dazu, ta koma kamar miyar tanade, ruwa tsululu kamar lokacin na fara dafa ta. Ban san lokacin da naji kwalla ta cika min idanu ba, na maida murfin tukunyar na rufe tare da kashe gas din. Na jingina da counter din kicin ina tunanin abu mai sauki da zan dafawa Yaya wanda ba zai dauki lokaci ba, sai dai duk abinda nayi tunani, sai in ga sam ba zai yiwu ba. Gabadaya duk wata idea ta dauke min, daga karshe dai na yanke shawarar kai mishi dambun a haka, tunda akwai komi a ciki, har maggi da mai sai dana saka a ciki, dama miyar don dai garnishing ne kawai.

Na ciccibi kayan na tafi falon Yaya dasu.

Tunda na fara zuba mishi yake kallona yana murmushi kwanannan abinda yake min kenan, idan na mishi magana yace ai cikin jikina ya canza ni ne shi yasa. Na tura mishi plate din gabanshi tare da tsiyaya mishi lemun a cikin kofi.

Ya ja plate din gabanshi, “yau kuma a haka zamu ci dambun?”. Ya tambaya cikin alamun tsokana.
Na dan yi murmushi cike da fargaba, “uhmm, wani lokacin komi yana bukatar canji ai”.
Yace “haka ne baby na”. Yayi bismillah tare da kai cokalin farko bakinshi, take yanayin fuskarshi ya canza, da kyar ya hadiya. Naji gabana ya fadi cikin fargaba, nace “me ya faru?”. Ban jira ya amsa ba na dauki cokali na kai bakina, yaji ya fara ziyartata kafin wani masifaffen gishiri mai rikita kwalwa ya biyo baya. Da sauri na kai lemun dana zuba mishi cikin bakina da niyar kora abincin dashi, domin ba zan iya hadiya shi ba. Nan kuma wani matsanancin tsamin lemun tsami daya min bismillah.

Ban san na tara kwalla a cikin idanuna ba, sai dana ji tana bin kumatuna. Da sauri Yaya ya kai hannu yana dauke min kwallar, yace “menene abin kuka kuma? Kada ki damu kanki, girki ai ya gaji haka. Bari yanzu in aika a sayo mana wani abincin”.
Ban ce mishi komi ba, naci gaba da share kwallata. Yanzu duk wahalar wannan da naci ta tashi a banza kenan? Babu abin ban haushi da takaici ga matar aure, ace mijinta bai ci abincinta ba ya tafi neman na waje yaci.
Cikin kwallar da nake yi, nace “a’ah, bari in shiga in yi wani abu mai sauki”.
Yace “inaa, ba zaki wahalar min da baby ba. Baki ji ance miki ba’a son ki cika yin aikin wahala ba? Maza daina kukan, kada ki sanya min baby kuka”.
Duk yadda yaso inyi shiru, abin gagara yayi. Har aka kira sallah ya koma masallaci, raina a jagule yake.

Daya dawo sai gashi da ledar take away, har daki ya kaiwa kowa nata. Daya kawo min nawa ko kallonshi banyi ba saboda masifar bacin rai. Allah ya isa kadai nake ja ina karawa a cikin raina.
Muna zaune yana cin nashi abincin, nawa kuma yana gefe, sai ga Raheemah ta shigo falon. Ta kallemu ta tabe baki, “uhhum! Su yan gaban goshi masu juna biyu manya, wato yanzu abincin ma an daina yi sai dai a tafi a siyo na waje? Kwarai kuwa, Allah muma ya azurtamu da namu cikin dai!”.

Kwata-kwata yau bana cikin jin zama in saurari korafe-korafen data saba, don haka na mike na wuce dakina, ban san yadda suka kare da ita ba. Sai wajen karfe goma sannan naje na kwashe kayan da muka bari. Ranar haka na kwanta zuciya a cunkushe.

Cikin dare fa barci ya gagareni, yunwa kamar zata kashe ni. Allah yasa na sanya abincin da Yaya ya kawo min cikin microwave, na zame jikina daga na Yaya a hankali na fita daga dakin. Kusan karfe biyu da rabi na dare lokacin. Shiru gidan, baka jin motsin komi.
Na shiga kicin, maimakon in kunna wuta, sai nayi amfani da hasken fitilar wayata. Na kunna microwave din, na koma falo na zauna akan dinning ina jiran abincin ya dumama. Fitilar na kashe, naci gaba da zama a cikin duhu, a zuciyata ina ta saka da warwara akan wannan sabuwar matsala data tunkaro ni.
Zato zunubi, amma da sai ince ga wadda ta aikata min wannan danyen aiki, sai dai shi zargi bashi da kyau. Kawai dai yanzu zan dinga yin takatsantsan ranar girkina kawai, shine mafita.

A hankali naji an turo kofar daki an fito, na daga kaina daga zuzzurfan tunanin dana fada. Raheemah ta fito itama tana haska fitilar wayarta tana taku sadaf-sadaf kamar barauniya, ganin ta wuce kicin kai tsaye yasa na dan yi murmushi. Da alama itama yunwar ce ta korota.

Ban yi motsin kirki ba balle ta ganni, na kara yin kasa da kaina ina wasa da yatsun hannuna.

Dare da baya raina abin ji komi kankantarshi, duk wani dan karamin motsi da zata yi ina jin shi, zuwa can naji tashin murya kasa-kasa alamun tana waya, hatta da daya bangaren data kira ina ji.
Cikin barci wadda ta kira din ta fara cewa, “ke wani irin shashanci ne haka zaki wani hau kiran mutane da tsakiyar daren wannan?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button