A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Yace “madam, barka da war haka”.
Murya a sanyaye nace “sannu da zuwa, ya aiki?”.
Yadda ya kalleni cike da mamaki yasa nima na kalleshi cike da mamakin, ko bai yi zaton zan amsa mishi bane? Yace “uhmm, lafiya lau. Ya asibitin?”.
Na gyada mishi kai.

Muka yi shiru daga ni har shi, kafin yace “Baby, don Allah ki fara saurarata kiji abinda zan ce”. Yayi shiru yana kallona yaga ta yadda zan karbi zancen, ban nuna komi ba, sai idanu dana zuba mishi alamun ina saurarenshi.
Yace “Hajara, diyar Alhaji Musbahu ce, abokin baban nan nawa da naje dubawa a Zaria kwanaki. Cewa yayi kawai ya bani ita, zai aura min ita, ni kuma ban san ta yadda zan yi in ce mishi bana son diyarshi ko kuma ba zan iya aurenta ba. Yayi mana halacci matuka a lokacin da muka bukaci taimako. Don Allah kiyi hakuri, amma idan har ba zaki iya ba, wallahi zan iya cewa na fasa”.

A raina nace ‘kamar gaske!’.
Na kauda kaina gefe ina jin kwalla na ciko min idanu, nace “ni har na isa in hana ka kara aure? Wacece ni?”.

Ban san cewa ya tashi daga inda yake ba, sai da naji ya kamo tafin hannuna, yace “saboda kin isa baby, kin kuma kai matsayin da zaki hana ni din in hanu”.
Wata yar siririyar kwalla ta zubo min a kan kumatu ya kai yatsa ya dauketa. Sai na fashe da kuka na fada jikinshi, cikin kukan nake cewa “nasan cewa fada kawai kake yi, amma ba zaka fasa ba!”.

Yana shafa bayana a hankali, cike da alamun lallashi yake cewa “try me baby, da gaske nake”.
Sai dana lafa da kukan, sannan yaci gaba da cewa, “zata zo ta ganki, idan kika ji bata kwanta miki a rai ba, to sai dai suyi hakuri”.
Na dan jefa mishi harara, “ni bana wani son ganinta!”.
Yayi murmushi a sanyaye, “I’m sorry baby, I love you!”.
Ban ce mishi komi ba, don a lokacin wani sashe na zuciyata rada min yake, ‘ya daina sonki yanzu!’.

**

Ranar Lahdi da rana, ina falo ina duba wasu manyan textbooks akan midwifery, duk da karatu dana gama hakan bai hana ni cigaba da neman ilimi ta textbooks ba, idan ma Allah ya bani dama so nake in cigaba da masters dina. Kofa naji ana knocking. Cikin mamakin wanda zai zo a daidai wannan lokaci na tashi na nufi kofar. Yaya ya fita dazu da safe, kan cewa zai je wani waje ya dawo, nasan ma bashi bane tunda da shine da ba zai tsaya yin knocking ba.

Wasu matasan yan mata biyu naci karo dasu, ba laifi dukansu kyawawa ne. Dayar zata yi sa’ata, fara ce ba can ba, doguwa mai dan jiki, yayin da dayar kuma daga ganinta kasan kanwar dayar ce, yanayin kamanninsu da surarsu kusan daya ce, kawai dai karamar tafi babbar kiba da fari.
Nayi yar fara’a duk da cewa ban san su ba, na musu iso zuwa ciki. Sai da suka zauna akan kujera, sannan naje na dauko lemu da ruwa na kawo musu.
Na zauna muka gaisa dasu, nace “ko kuna neman wani gida ne?”.

Karamar ce tayi saurin cewa “a’ah, Yaya Bilal ne ya kawo mu nan!”.

Na karkata kai ina kallonsu cikin mamaki, me zai hadinsu da Bilal? Na gyada kai a hankali nace “Allah sarki!”.

Karamar ta sake cewa “ni sunana Zainab, wannan kuma Hajara”. Ta nuna babbar.
Sai lokacin na kula da yadda babbar take ta sunke kai tunda suka shigo. Wow!! Sai lokacin na fahimci komi. Ita ce Hajarar dama? What a nerve she has! Da har ta iya kwaso kafafu tazo min gida.

Kafin in iya daga baki in ce wani abu, Yaya ya shigo cikin falon. Ya zauna a gefena, Allah ne ya iya bani ikon samun dauriya, na cije ban dankara mishi harara ba.
Yace “Madam, ga Hajara na kawo miki”.
Na gyada kai ina dan murmushin yake, “aikuwa na ga Hajara”…

Shi ya zama jagorar hirar tamu, ga mamakina cikin dan lokaci kankani muka saki jiki daga ni har su. Ko lokacin da lokacin sallah yayi, tafiya yayi ya barmu. Na kaisu dakina suka yi sallah, muka koma falo. Dana shiga kicin haka suka biyo ni, duk da magiyar dana musu akan su koma falo suyi kallo ko wani abu, fir suka ki. Duk wannan abin da ake yi, Muhaaseen na bayan Hajara a goye.
Kafin Yaya ya dawo mun gama girki. Muka zauna mu duka muka ci ana ta hira.

Anan na fahimci cewa dukansu a Abuja suka tashi, shima Babansu matanshi biyu, in fact, Zainab step sister din Hajarar ce. Ita Zainab tana Abuja uni tana karantar mass com, tana aji daya. Ita kuma Hajara wannan shekarar ta gama degree dinta akan architecture a jami’ar Tafawa ‘Balewa, Bauchi.
A abinda na karanta a cikin dan lokacin, shine suna da wani irin sanyin hali da hangen nesa, haka iliminsu ya tabo ta kowane fanni.

Zuwa lokacin da yamma tayi, suka mana sallama akan zasu tafi, sai naji kamar kada su tafi. Allah ya gani, naji dadin zuwansu sosai. Suma daga ganin yadda suka mike din zasu tafi, hakan take. Shima sai da direban da aka turo ya daukesu yazo, sannan suka tashi.

Na shiga daki cikin drawers dina da nake ajiyar abubuwa saboda bakin ba zata, na ciro musu turaruka masu kamshi, chocolates, kayan kwalliya, cike da leda na fito. Muka musu rakiya har gaban motarsu ni da Yaya. Sai da zasu shiga sannan Yaya ya karbi Muhasseen a hannun Hajara, na kula Allah ya hada jininsu sosai.

Na mikawa Zainab ledar hannuna, da taki karba, na harareta cikin wasa, “ko dai kin raina ne?”.
Ta zaro ido da sauri, a lokaci guda kuma ta sanya hannu ta karba, “haba dai Anty! Mungode sosai, Allah ya amfana!”. Wani halin nasu mai burgewa kenan, akwai godiya. Daidai da abinci wannan dana zuba mana, sai da suka biyo mu da godiya da addu’a.
Nace “babu komi wallahi, ku gaida su Mama Sai mun zo ziyara”.
Hajara tace “sai mun ganku!”. Daga haka direban yaja mota suka fita daga cikin farfajiyar gidan.

Yaya ya sakalo hannunshi daya akan kafadata, dayan kuma yana rike da Muhaaseen. Yace “ya?”.

Na daga kai na kalleshi ina dan murmushi, “uhmm, ba laifi. She doesn’t look that bad!”.
Yaya yayi murmushi a hankali, ya shafo hancinshi da nawa, “haka ne?”.
Na gyada kai ina murmushi. Da gaske ne kuma, haka kawai naji hankalina ya kwanta da ita sosai. Kai duk da cewa tun kafin zuwansu dama na saddakar, amma hankalina bai kwanta ba.
Yanzu kuwa dana ganta, sai naji hankalina ya kwanta da ita sosai, shima auren hankalina ya kwanta dashi.

Watakila maybe, just maybe, ba zata yi halin Ramata, Ameerah ko Raheemah ba. Kila ita za ayi zaman mutunci da ita!.

                      K'arshe!

‘THE GREATEST HAPPINESS OF LIFE IS THE CONVICTION THAT WE ARE LOVED; LOVED FOR OURSELVES, OR RATHER, LOVED IN SPITE OF OULSELVES!’.
VICTOR HUGO

              *☆⋆Epilogue⋆☆*





           Bayan Shekaru Biyar...

“Ni abinda yake daure min kai shine, babu fa abinda na mishi, kawai daga sama kamar saukar aradu naji maganar, ya sakar min ita aka kamar tashin bomb!”.
Janan take fada cikin tsananin kunar zuci.
Ni kuwa me zanyi in ba shekewa da dariya ba? Na dinga kya-kyatata kamar ba zan daina ba. Tana gefena tana jefo min bama-baman harara ita kuma. Sai da nayi ta isheni, na gyara zamana ina kwashe kwallar data zubo min.

Tayi kwafa, “baki da kirki wallahi Na’ilah. Saboda ke kina da kishiya, shi yasa kike sheka min dariyar mugunta nima don za’a min?”.

Na daga kafada, “tunda na dandana, kowa ma ya dandana mana. Ke dalla ki kwantar da hankalinki, ki daina wani daga hankalinki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Ita fa kishiyar nan, wallahi gane mata ne mutane basu yi ba saboda kawai sun riga sun fadawa kansu ba abokiyar zama bace, amma da gaske abokiyar zama ce. Ke ni yanzu wallahi Abban Maama ko ta uku da hudu yace zai karo, zamana zan gyara kawai ince Allah ya shigo dasu gidan lafiya. Ga fili ga mai doki, to ma wai, a kaina zasu zauna ne? Wasu ayyukan ma zasu rage min karewa. Ko ba komi, kin samu rarar kwanakin girki, kin samu abokiyar tayin ayyuka da hira, kin samu yar tayin raino da hidimar gida, sannan at least, wulakancin namiji ba sai kare a kanki ke kadai ba, ya dinga rabawa biyu yana bata rabi itama”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button