A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na silala jikina cikin motar ina murmushi, “tafiyar merely awa hudu ba zata gajiyar dani haka ba, Umar”.
Ya maida murfin motar ya rufe tare da ciccibar akwatina da jakata yasa a bayan booth, ya zagayo ya shiga yayi wa motar key, sai a lokacin ya juyo ya kalleni, “sai ina?”.
Nace “gidan su Janan”. Yayi jim, kafin ya juyo ya kalleni, fuskarshi na nuna alamun tambaya, cike kuma da mamaki. Na ajiye ajiyar zuciya, cikin alamun bayani nace “a can zan zauna zuwa lokacin da zan samu wajen zama”.
Yace “shine baki fada min da wuri ba? Da baki je wajen Mommy kin zauna ba?!”.

Na daga baki ina kallonshi kamar wani wanda ya fitar da sabon kai, ya kyalkyale da dariya yana dukan sitiyari, “just kidding!”.
Kai kawai na iya girgizawa. Abin ma sai ya bani dariya. Kawai sai aga budurwa taje gidan su saurayi zama, babu aure kuma babu komi. A can kasan zuciyata ina tunanin ai ko da ace Mommynsu da sauran kannenshi suna so na, ba zan iya wannan danyen aikin ba. Har yau bamu gama clicking waje daya da yan’uwanshi ba, ban san dalili ba. Amma na fi danganta hakan a rashin sanin juna sosai da muka yi.

Ya juya baya yana lalube cikin wata leda har ya ciro gwangwanin maltina ya miko min, na amsa, sanyinta na ratsa hannuna. Na fasa na kafa a kai na daddaka, na ajiye numfashi in bliss, “God! Kamar kasan abinda nake bukata kenan!”.
Yayi murmushi kawai tare da jan motar muka tafi.

A kofar gate din gidan Yaya Bilal yayi parking din motar tare da kashewa. A kofar gidan, Halima da Salama kannen Anty Raheemah ne zaune a karkashin inuwar babbar bishiyar mangwaro kofar gidan, da alamu hira ce suke yi ko kuma shan iska kawai.

Na bude murfin motar na zura kafata waje na fita daga ciki, shima Umar din ya fito, duk suka bi mu da kallo. Na gyara zaman gyalena a kafadata ina kallonshi nace, “na gode Umar, bari in karasa ciki”.
Yayi murmushi, “it’s my pleasure!”
Zagayawa yayi ta baya ya bude booth ya ciro min kayana dake ciki, ya sake bude bayan motar ya fito da shopping bag ya miko min, na daga baki zan yi magana yayi saurin katseni, “snacks ne kawai da drinks ba wani abu”.
Nasa hannu biyu na karba ina mishi godiya, ya girgiza kai, “kila zuwa anjima idan na gama abubuwan da nake yi da wuri, zan biyo”.
Nace “Allah ya kaimu anjiman”.
Daga haka ya sake zagayawa ya shige cikin motarshi ya ja ya bar wajen. Na dauki akwatina a hannu daya, dayan kuma na dauki daya jakar da ledar da Umar ya kawo min na tunkari gidan. Strangely, naji bugun zuciyata ya canza, na danganta hakan da nervousness.

Haleemo ta kalleni tana murmushi, “ashe yau kike tafe? Sannu da zuwa, ya hanya?”.
Na dan saki tight murmushi, gajiyar dana kwaso tana kara lullubeni, nace “lafiya kalau, sannunku”. Na gaishe su gabadaya, a lokaci daya. Duk suka amsa min, na wuce cikin gidan.

Duk cikin kannen Anty Raheemah, har ma ita Rahimar, Haleemo ta fi su sanyin hali, shiru-shiru, da kuma rashin rawar kai. Shi yasa tamu tafi zuwa daya da ita. Har wani lokacin idan naje gidan mu kan dan hiranta da ita. Salama kam, tsabar tsiwarta da rashin mutunci yasa ranar farko da muka fara haduwa da ita muka kusa yin baram-baram. Bata da kirki ko kadan, zata iya tsaga tsakiyar idanun mutum, ko ma wanene shi ta yanka mishi rashin mutunci ta kara gaba. To kada kuma Adi taji labari, ita ta damesu ta shanye.
Ni dai fatana daya, in samu in gama dan zaman da zanyi dasu lafiya ba tare da wani rikici ba. Shi yasa na taho da kudiri, kuma da burin kai zuciyata nesa, kauda kai daga lamarinsu koda zasu taka ni ne, da kuma maida komi ba komi ba. A takaice dai, naci damarar ba banza ajiyarsu.

Ina bi ta kofar gidan, maigadin gidan, Ahmad. Dan matashine, kuma buzu, ya fito daga dan dakinshi da sauri yana min oyoyo. Murmushi nayi a gajiye na amsa, ya karbi akwatin hannuna da jakar ya biyo ni a baya har sashen Yaya Bilal din.
Na buga kofar falon gidan, jin alamun kofar a bude take yasa na tura kofar na shiga bayan na cire takalmina anan dan corridor din da suka tanada musamman saboda ajiye takalma.
Ahmad ya ajiye min kayana na sake dauka na shiga babban falon nasu bakina dauke da sallama. Raheemah da kawarta Adi na zaune suna kallo, gefensu gwangwanayen lemuka ne da plates wanda nake tunanin suka gama cin abinci daga ciki.

Babu wadda Allah ya bata ikon amsa min sallamar da nayi, sai kallo da dukansu suka fara bi na dashi, dani da kayan hannuna. Duk kokarin da nayi, sai da naji zuciyata ta fara rawa. Wani bangare mai rauni na zuciyata ya fara raya min over and over, zuwana nan gidan was a bad idea. Yana kara gaya min dalilai da dama, masu nuni da cewa gaskiya yake fada min.
Bisa wadannan dalilai dama wasu, yasa naji na fara tantamar anya ba zan juya inda na fito ba kuwa? Musamman tunda Janan bata riga ta san da zuwa na ba, zan iya ce mata wani uziri ne ya taso na gaggawa da yasa na koma gida, ko rashin lafiya, ko…!

Daidai lokacin da kofar dakin Janan din ya bude, ta fito daga ciki. Muna hada ido da ita, ta saki murmushin daya haskake mata fuska baki daya. Ban san dalili ba, naji wani kwarin gwiwa ya shige ni, wani over confidence dana rasa daga inda yake. Da sassarfarta ta karaso wajena, bata yi wata-wata ba, ta janyo ni ta rungume.
Sai data gama murnar ganina sannan ta sake ni, ta ja baya tana kare min kallo tun daga sama har kasa. “ke hutun nan dadi ya miki sosai fa da alama… Taho muje daga ciki dai, kiyi sallah ki huta!”.

Ta kama akwatin hannuna ta fara ja. A hankali na maida kallona ga su Rahima da har lokacin, idanunsu na kanmu kurr. Yadda suka yi yasa na fara tunanin anya sun san da zuwan bakuwar da zata zaune musu a gida na yan kwanaki kuwa? Nayi kokari na danne uneasiness din da naji a jikina, ko ma dai menene, tsakanina da Allah bana son wani abu yaje ya zo, a dinga cewa ta dalilina hakan ya faru.
Don haka na dage tun karfina na kakalo murmushin da ni kaina nasan cewa sun san na yake ne, gajiyar da nayi ta kara worsening abin. Nace “Anty Rahima, Adi, sannunku da gida!”.
Adi ta amsa da ‘lafiya lau’, yayin da Rahimar ta dauke kanta daga gareni ta maida kan Janan.

Cewa tayi wai, “wannan fa?”.
Nayi kwafa a boye, wani ‘wannan fa!’ sai kace wata shara ko kayan wanki, yadda kasan bata taba ganina ba.
Janan da bata kula da rainin wayon da tambayar tazo dashi ba, ko kuwa ta fahimta fuskewa kawai tayi? Cikin murmushi tace “Anty kawata ce fa, Na’ilah. Yaya ya fada miki zata zauna damu kafin ta samu wajen zama a cikin hostel”.

Antyn ta sake waiwayowa ta kalleni, fuska a murtuke, bakinta a tsuke, wanda ba karamin kokari nayi wajen danne dariyar data kamo ni ba sanadiyar ganin expression dinnan ba. Tace “zama damu ko ke?”.
Janan din ta danyi turus! Kafin ta sake yin murmushi ta cigaba da jan akwatin zuwa dakinta tana furta “muje”. Ban kara waiwayarsu ba na bi bayanta.
Sai dai ko daga inda nake, ina iya jiyo sautin muryarta da maganganun da take yi da dan karfi, obviously yadda zamu jiyota sosai, “shima ‘Baby’ da dan banzan kwashe-kwashe. Kawai babu dangin iya balle na Baba ka wani kwaso mana yarinyar da baka sani ba, ka ajiye mana a gida. Ko da wanne yake so mutane su ji? Da wannan yar rainin wayon kanwar tashi ko kuwa da wata bare kuma?”, tayi shiru tare da yin kwafa, “wai wani kafin ta samu daki! Ko kuma kwadayi ba!!. A dai zo a zauna din, aga idan wata tsiya za’a b’anb’ara daga jikinmu….”.
Sauran maganar ta mutu lokacin da muka shige dakin Janan muka maida kofar muka rufe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button