A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na turo baki, “yanzu kuma kina bin bayan Yayanki ne, zaki yace min baya?”.
Ta matso kusa dani da sauri, “koda wasa wallahi, haba, akan me zan miki haka? Ni fa shawarar da nake gani zata fissheki ce naki baki ba wani abu ba”.

Na tashi tsaye, “whatever dai, ni dai an gama min wasa da hankalina, bana kuma tunanin zan iya tsayawa in sake sauraron shi”.

Janan bata ce komi ba, ta zuba min idanu. Ni kuma na fara cire kayan jikina.

Idan da ace wani zai gaya min cewa a haka yinin na yau assabar zai kare min, da tuni zan karyata shi. Idan ma raina ya baci sosai, in kara da fada mishi bakar magana. Yau dana tashi da safe, ba haka na hango ni ba, ban taba tunanin akwai wani abu da zai zo yayi ruining yinin nawa na yau ba, sai gashi tun ba’a je ko’ina ba, yinin yayi bacin da ban taba tunani ba.
Na kalli kayan jikina dana cire, naji wani makokon takaici ya kawo ni wuya, ko linke su banyi ba na cukuikuyesu na jefa cikin kayana. Na dauki towel babba na daura a jikina. Ban cewa Janan komi ba, na dauki bokiti na sauka kasa na tari ruwa naje na watsa ruwa a jikina haka nan.

Ina cikin yin wankan naji an kira sallar magriba, don haka na daura alwala na koma sama.
Ina shiga dakin naci karo da Esther a zaune, da kayan dana baro a inda na ajiye. Ni na ma manta dasu. Daga ita har Janan suka bini da kallo.
Esther ce ta fara magana, ban san me Janan tace mata ba, amma naji bata tado min zancen dazu ba. Na dai ji ta tana mitar, “Ni wallahi nayi zaton ko accident ne suka yi ko wani abu a dazun, har na tsorata. Daga yace wani abu na gaggawa ya taso, sai ki wani rikice har haka? Lallai kina da babban aiki kuwa yarinya!”. Ni dai na shareta ban ce komi ba.

Kayan dana ke sanyawa na shan iska na sa, na tada sallah nayi. Ina gamawa itama Janan ta shigo dakin, don haka na koma gefe na bata waje itama tayi. Tana gamawa Esther ta kallemu, tace “ni fa yunwa nake ji, kuma na rantse ba zanyi wani girki ba alhalin ga abinci nan ina gani a gabana. Idan ba zaki ci wannan abun ba, ki bani inci don ba zan so ayi asarar su ba gaskiya”.

Nace “gashi nan kiyi ta ci”.
Tayi tsalle ta rarumo kayan, Ina ji Janan tana itama a ajiye mata bari tayi sallah ta zo taci, nayi banza dasu su duka.

Ana kiran sallah na tashi nayi. Janan ma tana gama nata, ta zauna ta tada meat pie din da Esther ta rage mata da sauran drinks din. Dama guda biyar ne nayi babu yawa. Janan tana gamawa ta kalli agogo, tace “bari in tashi in tafi kafin Yaya ya dawo, yayi fada”.

Ai jin an ambaci sunan Yaya, sai naji raina ya kara dagulewa. Na koma kan katifa na zauna, na harde hannuwa a kirji ina turo baki ina kallon Janan tana gyara zaman hijabin jikinta a wuyanta, ta gama ta juyo tana kallona, “mai kike jira ne, ba zaki raka ni ba?”.

Na kara turo baki, “a’ah, ki gaida mutan gida!”.
Ta daga hannuwa sama in mocking surrender, cam cikin idanunta alamun dariyar da take ta kokarin boyewa ne. Na harareta, ta kara yin murmushi, tace “yi hakuri ki maida wukar, ba ni na kar zomon ba kin gane? Bari in karasa gida ni kam. Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, kada ki bari wannan abin ya taba zuciyarki kinji?”.
Na kalleta kawai, sanya abu a cikin rai na nawa kuma?
A haka dai ta mana sallama ta tafi.

Ina zaune ina kallon Esther data tashi tana hada kayan, tana cewa ita dai ba zata yi wanke-wanke ba fa, “Sai dai idan kin tashi gobe ki wanke kayanki amma ba zan iya ba”.
Ta dai gaji da mitar ta tayi shiru ganin ban tanka mata ba. Tana gama abinda zata yi, tace min ta tafi class. Exam dinmu ranar monday ne, amma nasan ko giyar wake na sha ba zan iya yin karatu ba yanzu. Don haka na kwanta kawai ina ta faman saka da warwara a cikin raina.

Har wajen karfe goma sha daya na dare idanuna biyu kyar, babu alamun barci a cikinsu. Juyi kawai nake yi, ba tare da takamaiman wani abu da nake tunani a kai ba. Wayata ta fara kara, daga farko cak nayi a zaune, hatta da numfashina sai daya tsaya sakamakon jin kalar karan. A hankali na juya na kalli wayar, babu shakka sunan Muhammad ne, ko kuwa Yaya Bilal zan ce? Yake yawo akan wayata.

Ban iya motsawa ba har ta katse, tana katsewar aka sake kira. Na hau gyada kai ina kara girgizawa cikin tsananin mamaki, yanzu har Yaya yana da sauran kunyar da zai iya kirana a waya dama? Oh duniya ina zaki damu?!.

Na dauko wayar da niyar kasheta, hannuna ya silale ya taba answer and speaker button ba tare dana kula ba, sai dana ji muryar shi radam kamar a cikin dakin yake yana magana, “hello? Oh thank God! Baby kina ji na? Baby…?!”.

Da sauri na danne wayar har ta mutu, na dafe saitin zuciyata data hau bugawa da sauri kuma da karfi. Jin muryar shi a yanzu, sai naji kamar an tado min wani tsumi. Ko ba’a fada ba, nasan yau munyi baram-baram ni da barci.

             Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe don Allah. Jiya sai dana yi typing, nayi zaton na turo na goge, sai daga baya naga ashe ban turo ba.

☆⋆23⋆☆

Washegari na tashi da wani azababben ciwon kai wanda ban taba zaton wani mahaluki zai taba yin kamar sa ba sai a ranar. Ni dama nasan za’a rina, yadda jiya na kwana ina sake-sake, barci ma sai gab da sallar asubahi sannan ya daukeni. Dalili kenan da yasa na so in makara sallah yau. Ina yin sallar kuma dana koma barci ma, kasa komawa nayi, sai can rana har ta ma fara fitowa sannan nayi barcin.
Yanzu kam zaune nake akan katifata da misalin karfe goma da rabi, kaina da yake bugawa kamar ana kwankwasa guduma tallabe cikin hannuwana guda biyu. Dakin babu kowa, Esther ta tafi church, Maimuna kuwa dama rabona da ita tun ranar juma’ah da safe da zan bar daki, ban kara ganinta ba.

Na samu na lallaba da dafa bango na tashi na fita. Ruwan wanka na jona a jikin heater, kasancewar ruwan da aka yi yau da asuba, yasa har yanzu garin sanyi garai. Yana dan yin zafi na je nayi wanka, nayi brush hadi da dauro alwala. Sai dana fara yin sallar walaha sannan na sake dafa wani ruwan a cikin kofi karami, na hada hot chocolate shi kadai na sha. Bayan na sha na balli paracetamol guda biyu na afa a baki na kora da ruwa.

Bayan na gama kin komawa in kwanta nayi, na kuma ki zama in saka tunanin Yaya Bilal da al’amuranshi a cikin raina. Sai kawai na dauki wayata na jona ta a jikin caji ba tare dana kunnata ba, na hada kan kayan wanke-wanke na kulle dakin na sauka kasa nayi.

Bayan na gama na koma dakin, ciwon kan ya dan sauka kadan, amma jifa-jifa na kan ji ya sara min har yanzu. Na bude dakin na shiga tare da maida kofar dakin na rufe. Kasancewar yau students suna ta hutawa kuma safiya ce, wasu kuma sun tafi gida, yasa hostel din yayi shiru babu hayaniya, yadda kasan ma babu kowa.
Na fara da kunna wayata. nasan dai ba zan dawwama a haka ba, komi daren dadewa nasan dole in fuskanci wannan chakwakiya. Ban shirya ba, amma nasan dole ne. Don haka naga gara in fara tun yanzu, the earlier, the better.

Ko minti goma cikakke banyi da kunna wayar ba, ta hau kara. Na saurara da goge-gogen da nake yi tare da tsayar da kira’ar Sheik Minshawi da dan yaro a cikin suratul-Mulk dake tashi daga cikin laptop dina, na dauki wayar. Ganin sunan Yaya Mudatthir na daga da sauri, cike da tunanin ko Anty Sailu ce ta sauka. Sai dai ina dagawa, tun ma kafin inyi magana ya riga ni, yace “wai ni Illo don Allah menene amfanin wayarki ne? Ke kullum aka kira wayarki a kashe? Me yasa ba zaki ajiye wayar kawai ki cire komi nata ba kowa yasan baki amfani da waya?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button