A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Shi kanshi Yaya din, yau da gobe ce tasa ya gane tana zaman gallazawa a gidanshi. Sai ma watarana da yazo ya tadda Sa’adiya wadda suke cewa Adi, kawar Raheemah din da take zaune a gidan, tana ta zagin Janan akan wai bata yi mopping din falo ba, ran Yaya ya baci matuka, ya tara su su duka ya ja musu kunne, kuma yace daga ranar duk wadda ta sake taba mishi kanwa a gidannan, sai ta bar mishi gida. Aikin gidan ma kuma daga ranar ya hana ta yi, ita ce dai taga dama taci gaba da yi, tunda kunnen kashi gareta. Duk yadda nayi da ita akan ta bari tunda yace ta bari din, kiyawa tayi. Don haka na zuba mata ido, ni dai nasan da ni ce, da zuwa yanzu su duka sun bar gidan.

To rayuwar dai haka ake yinta, yau dadi, gobe madaci, gashi yanzu wasu abubuwan sun zama sai dai a tarihi. Nan da lokaci kadan ma, zata bar musu gidan.

                               *








           *☆⋆04⋆☆*
  • ☆ *

Har washegari Lahdi ina jiran Baba ya turo min kudin mota, amma shiru kake ji, kamar an shuka dusa.
Na duba agogon dake daure a tsintsiyar hannuna, naga cewa karfe goma sha daya na safe ta wuce. Nayi kwafa. Wani text din na sake tura mishi. Sai can wajen karfe sha biyu da rabi naji karan shigowar text, na duba naga shine ya turo min kudin motar, nayi kokarin resisting takaicin daya tuko ni, zuciyata na tunatar dani gida za ni ba wani waje ba.
Sai da nayi sallah sannan muka yi sallama da Aylah cike da kewa. Ina shirin fita kiran Umar ya shigo wayata, ya sanar dani yana waje yana jira na, don haka na ciccibi akwatuna na fita.

Ya saka akwatin a bayan booth, ni kuma na bude gidan gaba na shiga. Ya shigo motar ya tashe ta. Sai daya tsaya a banki na ciri kudi, sannan muka tafi. Har tashar mota ya kaini. Sai daya biya min kudin mota, sannan ya min sallama. Na mishi godiya sosai. Allah ya taimakeni motar ta kusa cika, ba’a jima ba muka dauki hanyar Katsina.

*

Karfe biyar na yamma a cikin garin Katsina ta mana. Motar tayi karan karshe a cikin tasha, a gajiye na fito daga motar ina mika. Na rataya jakata a kafada tare da daukar dan madaidaicin trolley din dana sako kayan da zan bukata na fita daga tasha din. Shatar adaidata nayi har unguwar Magama inda gidanmu yake.

Madaidaicin gidane daidai masu rufin asiri. Na fita daga cikin adaidaita din bayan na biya shi kudin shi. Wasu daga cikin yaran gidan dake kofar gida suna wasa suka bazamo da gudu suna ihun min oyoyo, nayi dariya ina dukawa kasa yadda zasu ji dadin rungumeni sosai. Abbakar ya dauki trolley na, yayin da Auwal ya rike jakar hannuna, na kama hannun Mufeedah muka shiga gidan.

Matan gidan suna zaune a tsakar gida, Anty Alawiyya na dura kunun aya da take yi na sayarwa a cikin gororin ruwa, Anty Ramata kuma tana kofar kicin a zaune, ina zaton ita take da girki yau.
Duk suka saurara da abinda suke yi jin hayaniyar yara har muka shiga cikin gidan. Anty Alawiyya ce ta mike tana dan murmushi, “mutanen Zaria ne yau a garin? Ai bamu ji labarin zaki zo ba koda wasa!”.
Nayi murmushin yake, dama a ina zasu ji? Na san koda wasa Baba ba zai fada musu ba. Ni kuwa dama ba waya muke yi dasu sosai ba, tunda na fara makaranta, babu wadda ta taba daga waya ta kira ni da sunan mu gaisa, sai nice idan naga an kwashi kwanaki nake kiransu haka nan dai, musamman ma don mu gaisa da yara. Kullum idan na dawo daga makaranta zancen daya, ne babu wani canji.

Na sauke Mufeedah kasa tare da gaidasu daya bayan daya, suka amsa fuska babu yabo babu fallasa, na tabe baki tare da ciccibar akwatuna na tunkari dakin daya kasance nawa tunda muka dawo Katsina.
Na ja nayi turus, sakamakon ganin kofar dakin a bude, abin ya bani mamaki. Na tabbata da zan tafi makaranta sai da na saka kwado na rufe kofar dakin, kuma ban bar dan makullin a gida ba. Babu wanda yayi tunanin yi min karin bayanin abinda yake faruwa, don haka na tura kofar dakin.

Abu na farko daya fara min sallama shine tarin kayana da aka hade waje guda acan karshen lungu, akwatuna daya kan daya, kwalaye bisa kwalaye, yayin da ilahirin tsakiyar dakin yake shake da tarkacen kayan Maryam. Na juya na kalli Saudah yar autar Anty Ramata dake zaune a kofar dakin mamanta dake kusa da dakin da nake, nace mata “waye yake kwana a dakina?”.
Tace “Anty Maryam ce, Mama tace ta koma dakinki tunda kullum a kulle yake kuma tayi girma da zama a dakinta”.

Nayi kwafa ina kallon Uwarta ta, nace “shine saboda tsabar bani da muhimmanci babu wanda yayi tunanin sanar dani?”. Duk suka yi tsuru su biyun. Na sake yin kwafa tare da shiga cikin dakin. Ko karewa dakin kallo ban yi ba naje na dauro alwala na dawo dakin nayi sallah. Sai dana gama sannan na kira Umar na sanar dashi sauka ta, yayi min sannu da zuwa. Bayan nan na kira Janan itama muka gaisa, tana dariya tace “bana miki wayo, ni tun safe ina gaban Ummana!”.
Nayi yar dariya, “ya miki kyau ai, Allah ne ma yasa motar tayi gudu sosai, kila da sai magriba zan iso ni kam”.
Mun dan yi hira kadan da ita, har ta bani Umma muka gaisa, sannan muka yi sallama da ita.

Tashi nayi na fara gyara kayana da aka wulakanta a dakin, ina maida su ainihin wajen da suke da. Kafin a kira sallar magriba na kammala gyarasu tas. Nayi sallah, na zauna akan abin sallar nayi karatu kamar yadda na saba har aka kira isha’i nayi, sannan naci gaba da gyara dakin. Na share shi nayi mopping, na dauko room freshener dana saba yin guzurinta na fesa a dakin. Nan da nan dakin ya fito tas dashi, ba kamar yadda na same shi dazu ba kamar bana mahaukata.

Tun ina karatu naji alamun karan motar Baba alamun ya dawo gida. Kasancewar yau babu aiki nasan cewa daga shago yake. Zuwa yanzu nasan cewa ya ci abinci kuma ya huta, na dauki hijabina na fita zuwa dakinshi. Babu kowa a dakin na shi sai shi kadai. Na durkusa acan gefenshi na gaida shi, ya amsa. Da alamun yana cikin yanayi mai dadi, tunda har na zauna muka danyi hira dashi. Abinda sai lokaci zuwa lokaci yake faruwa.
Ban san me yasa ba, ni da Baba sam bamu cika shiri ba. Amma nafi kyautata zaton rawar kaina ce ta janyo hakan, tunda ya sha fada ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
Sai da Ramata ta shigo dakin sannan na mishi sai da safe, na koma dakina, ko ince dakinmu.

Ina komawa shirin barci na fara yi. Bayan nayi Sallar shafa’i da wutiri, na samu gefen katifa na zauna tare da dauko wayata dana ajiye a kasan filona. Ina cikin chatting Maryam ta shigo cikin dakin.

Duk yan dakin Ramata, ita, Aliyu da Hareerah, da ita kadai muka fi dasawa. Sauran suna kan hudubar uwarsu na cewa ‘yan uba, ba ‘yan uwa bane! saboda haka bamu cika shiri dasu ba. Amma ita babu ruwanta ko kadan.

Tayi murmushi tana kallona, “yanzu Hareerah take fada min cewa kin zo, ina ta mamaki”.
Nayi yar dariya ina kallonta tana zame after dress din dake jikinta, riga top mai karamin hannu da wnadon bakin jeans suka bayyana a jikinta, dariyata ta koma daga gida mai nuna alamun tambaya, nace “daga ina kike, kuma wannan shigar fa?”.

Ta kalli jikinta kafin ta kalleni, “kawata take bikin birthday, shine na leka wallahi”.
Na girgiza kai, “birthday party kuma sai da irin wannan shiga Maryam? Me yasa?”.
Tayi dariya, “Yaya Na’ilah ke da kike makarantar jami’a kin fa fini sanin irin wadannan abubuwan. Yanzu ‘yanmata ai sai da swagger! Idan mutum ba so yake a dinga mishi kallon taro-uku-sisi ba!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button