A ZATO NA COMPLETE

Baba yace “shawarar me zan sake? Zubda kimata da mutuncina yaron nan ya riga yayi, yanzu duk cikin unguwar nan kowa zancen yake yi. To zai zauna yayi min a gida kuma? Ba zan iya ba, ya tarkata nashi-i-nashi ya bar min gida kawai”.
Sai lokacin na samu kwarin gwiwar yin magana, nace “Baba kamar yadda Anty tace, wannan fa ba shawara bace. Zancen zubewar girma da sauransu, duk bata taso ba, tunda abinda dai ya faru ya riga ya gama faruwa, kuma ba’a dawo da hannun agogo baya. Abinda ya faru ya riga ya faru, sai dai a tari na gaba kawai. Amma korar Aliyu daga gidannan ba mafita bace, Allah ya gani. Baka tunanin idan ka kore shi din, maimakon ya saduda, sai hakan ya kara sanya shi yabi wata hanyar daban kuma? Duk kuma dai abinda zai yi nan gaba kana da alhaki akai, kuma duk inda zai je ya dawo dai, nan da shekaru goma ko dari, dole ya dawo gareka saboda danka ne, tsatsonka ne. Shi hannunka ai baya rubewa ka yanke ka zubar”.
Baba yace “sai dai in hannun baya damuna. Amma tuni zan yar da dan banza in huta. Tun yaushe Aliyu yake bata min rai? Makaranta baya zuwa daga ta boko har ta islamiyar, bai san komi ba sai daukar magana a cikin unguwa. Yau ya zagi wancan, gobe ya bugi dan wancan, shi kadai ranshi yabi ya addabi mutane ina dalili?”.
Nace “hakuri dai za ayi, shima ba zai kara ba”.
Baba ko in ce iyaye da dama, suna da wani hali na sangarta yaransu, to the extent that sangartawar zata wuce misali. Yara zasu lalace, su daina ganin kan kowa da gashi, wani abin dariya ko tausayi shine yadda hatta da iyayen nasu ma zaki ga basa jin maganar su. Sai labari ya sha banban, yaro yaje ya dauko magana, sai kuma anan iyaye suzo su ce basu san wannan ba. Su zo su kori yaran. To me kenan aka yi? Ihu bayan hari kenan. Maimakon tunda da sanya hannunka hakan ta faru, ka tsayawa yaronka ya koma gagara-badau, lokacin da yayi tashen tsageranci da rashin da’a ka tsaye mishi, maimakon idan sun dauko maganar da tafi karfinsu su sake tsaye musu, a’ah, sai suce sun janye hannunsu daga garesu.
Sun manta lokutan da suka tsaye musu suka dinga yin abinda suka yi din, har suke ganin babu wani ko wata wadda ta isa sai su.
Don bana manta lokuta da dama da mutanen unguwa zasu kai karar Aliyu wajen Baba, akan wani abu da zai musu, muma mun sha kaiwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma bai taba daga baki yace mishi don me? Ko kul ba.
To yanzu idan iyaye basu dauki responsibility din laifukan ‘ya’yansu ba, wanda idan aka yi duba tun tali-tali suna da kamasho a ciki, wa zai dauka?
Bayan doguwar muhawara da jeka-ka-dawo, da kyar muka samu ni da Anty Alawiyya Baba ya sassauto. Duk wannan abu da ake yi, Ramata da Aliyu na gefe in banda sharar hawaye babu abinda suke yi.
Daga karshe dai yace ya hakura, akan sharadin idan makamancin haka ta sake faruwa lallai zai kore shi. Ni dana kasance zabiya, ni nace naji na amince. Nan ya sake hada mu yayi mana nasiha mai shiga jiki, yace ya sallamemu.
Ina tashi, Ramata ta kamo hannuna. Kuka take sosai kamar wadda aka yiwa mutane, godiya take jera mana kamar harshenta zai fado kasa, “nagode, nagode, Na’ilah! Yau da ba don ke ba ban san yadda zanyi ba, Allah yayi miki albarka, nagode!!”.
Ni kam na ma rasa abinda zan ce mata, jiki a sanyaye na dinga binta da kallo har sai da tayi radin kanta ta sake ni, sannan na juya na fita daga dakin.
Kai tsaye dakin Aliyu na wuce, na same shi a gefen katifarshi a zaune. Zama nayi dirshan a tsakiyar dakin, magana muka yi mai tsayi ni dashi game da abinda ya faru. Ba karamin mamaki na ci ba lokacin daya fada min wai kudi yake bukata shi yasa ya fara saida tabar saboda yaga abinda yaran unguwar sa’anninshi suke yi kenan, kuma suke samun kudi.
Nace “kai kuwa me ka nema ka rasa haka?”.
Yace “to Baba baya bamu kudi, yanzu ko Mama baya bata. Kudin makarantarmu kusan term biyu bai biya ba, sai da aka koro mu. Kuma Mama bata da lafiya, in taje asibiti aka bata magunguna, Baba baya sai mata. Ya zamu yi?”.
Wannan a halin Baba kam ba abin mamaki bane, haka yake. Duk wadda baya dasawa da ita a cikin matanshi, to ba ita kadai ba, har ‘ya’yanta ma sai sunji a jikinsu. Na gani a kaina, hakan kuma ta faru akan ido na. Ina ga ina bukatar mu sake zama na musamman da Baba. Yana bukatar wani ya fahimtar dashi irin wannan rashin adalcin nashi, ba abu bane mai kyau. Sai dai dana sake tunanawa, sai naga ba hurumina bane hakan. Watakila Yaya dai zai iya shiga cikin maganar tunda duk cikinmu, baya jin maganar kowa kamar tashi.
Nan na zaunar da Aliyu, na fahimtar dashi cewa hakan fa ba mafita bace, sai jefa kanshi daya kusa yi a cikin halin k’ak’a-ni-kayi. Na tunatar dashi muhimmancin hakuri, da cewa ita rayuwar duniya ba lallai bane sai ka mallaki abinda kake so ba. Tunda ba duka kake samun komi ba, kuma idan kace kai sai ka mallaki komi to kai zaka kwana ciki kuwa. Na jima sosai a dakin nashi kafin na tashi na koma dakin Maryam.
Ina zuwa na tadda Kulsum, nan muka hau hirar yaushe gamo. Tana nan har an sanya musu ranar aure da wani lakcaran su. Sai da za’a rufe gida sannan ta mana sallama ta tafi.
Bayan munyi shirin kwanciya, na dauki waya na kira Yaya Mudatthir na zayyane mishi duk abinda ya faru. Yace Baban ya mishi waya a jiyan, amma bai sanar dashi hukuncin daya yanke ba. Mun jima muna tattaunawa dashi, daga karshe muka yi sallama dashi akan cewa cikin satin zai zo. Bayan mun kashe wayar, Yaya na kira muka raba dare muna hira. Muna gamawa ko barcin minti talatin banyi ba, na tashi sallar tahajjud.
Da asuba muka tashi ni da Maryam muka dafa abincin sahur. Bayan munyi sahur, Mazan sun tafi masallaci, mu kuma muka yi tamu sallar a daki. Na dauki Al-Kur’ani mai girma na fara karantawa.
Gari ya fara yin haske lokacin da Ramata ta fado dakin kamar an jefota, ni da Maryam duk muka bita da kallo cike da mamaki. Ta tsaya a bakin kofa muna kallon-kallo da ita. Maryam ce ta tambayeta, “Mama lafiya?”.
“Na’ilah kiyi hakuri!”. Itace kalmar data fara fita daga bakinta. Tsabar mamakin jin kalmar yasa na saki baki hangangan ina kallonta kamar wata sabuwar halitta.
Bata damu da kallon da nake jifanta dashi ba, ta fara cewa “nasan cewa bani da hurumin baki hakuri akan duk wasu abubuwa dana miki, nasan na aikata abubuwa da dama na rashin kirki a gareku, amma wallahi na aikata hakan ne cikin tsananin jahilci wanda kishi ya haddasa min. Amma yanzu na gane, na kuma dawo cikin hayyacina, don Allah ku yafe min abubuwan dana aikata muku”.
Har lokacin bakina a bude, bansan abinda yakamata in ce mata. Strangely, sai naji wata fahimta ta shige ni. Wani fannin na raina ya fahimci abinda tayi din. Ban sani ko hakan yana da nasaba da halin da nake ciki a yanzu bane. Zama tsananin mata irin Ameerah da Raheemah, zai sanyaka ka fahimci abubuwa da dama kamar halin da muke ciki yanzu da Ramata dai.
Akwai lokuta da dama, da tsabar kishi, son zuciya da zugar shaidan suka sha taso ni a gaba da wasu irin shawarwari da muggan sake-sake. Wadanda tsabar tsananin tsoron Allah da abinda zan tarar idan nayi abinda Ramatan tayi ne kawai yake dakatar dani, don haka ne na dage da rokon Allah akan ya yaye min irin wadannan abubuwa. Allah kuwa maji rokon bawanshi ne, a hankali naji duk wadannan sake-saken na daina yin su.