A ZATO NA COMPLETE

Nasan Ramata tabi zugar shaidan ne da son zuciya. Son zama da tauraruwar da haskenta bashi da wani tasiri balle hasken azo a gani.. Sai dai son zuciya irin nata ya janyo mana yin rayuwar kunci da wulakanci a lokacin daya kamata ace munyi mabanbanciyar rayuwa.
Sai dai idan na sake duba hakan da wani ido na daban, son zuciya irin nata ne ya tseratar dani daga aikata mugun halin data aikata mana ga sauran abokanan zama na. Allah ya sani, ina da damar yin hakan, ina da fadar yin hakan, sai dai tunanin cutar da wani ta hanyar data cutar damu yakI ya zauna min, na kasa yin hakan. Idan na tuna zafin da naji, idan na tuna tsananin kunar da naji, idan na tuno darare da dama da nayi su cikin kuka da bakinciki da takaicin abinda matar nan tayi a gareni, sai inji ba zan taba iya aikata hakan ga kowa ba. Ba zan taba iya so wani yaji rabi-rabin abinda naji ba.
Sai dai ban hakuri daga bakin Ramata, abu ne da ban taba zaton zanji daga gareta ba, ban kuma shiryawa hakan ba.
Don haka naci gaba da kallonta kawai, har ta gama fadin abinda zata fada, ta juya ta fita daga dakin. Shiru ya biyo baya daga nan, ni da Maryam muka hau yin kallon-kallo, kafin na maida kallona ga kur’anin da nake karantawa.
Zuwa lokacin dana gama, gari ya gama wayewa, yara sun tashi suna ta shigowa gaisuwar safe. Sai lokacin na bude gwangwanin alewar eclairs dana kawo musu, bayan sun gama karba sun fita, sannan fa na koma barci. Ban tashi ba sai wajen karfe sha biyu na rana, shima wayar Yaya ce ta tada ni. Bayan mun gaisa dashi, na tashi na fita tsakar gida.
Babu kowa duk suna daki. Nan na fada bandaki nayi wanka. Sai anjima da yamma zamu tashi, hakan ya bani damar gudanar da duk wasu shirye-shiryena a nutse.
*
Kafin mu tafi na kira Aliyu dakina, na bashi kudi nace washegari ya raka Mamansu asibiti a dubata sosai. In yaso koma menene daga baya, zan kirasu inji.
Har bakin motarmu suka raka mu, Ramata har da kukanta tana ta godiya. Aliyu ya bude min bayan motar na shiga, ya maida ya rufe. Har lokacin kalma daya bata sake hada mu da Ramata ba, saboda ban san abinda yakamata in ce mata ba.
Yanzu da nake kallonta, ita da dan nata da a da, babu abin wulakantawa a wajensu kamar ni, abu daya ne yake min yawo a ka, ‘lallai abinda ya baka tsoro, wata rana sai ya baka tausayi!’.
Muna first class ni da Yaya. Bayan jirgi ya gama lodi, aka fara sanarwar tashin jirgi. Kaina yana kan kafadar Yaya, hannuna na dama cikin nashi yana shafawa a hankali. Hankalinshi yana kan jaridar Vanguard yana karantawa.
Na lumshe idanuna a hankali kafin na bude su, ina kallon gajimare da muke ta ratsawa ta cikin tagar dake kusa dani. Na sauke wata doguwar ajiyar zuciya. Dana duba baya, shekara daya data wuce, ban taba zaton cewa yanzu war haka zan kasance akan kafadar mijina, Yaya Bilal, muna tsallaka Nigeria zuwa yin ibada a kasar Makkah ba. Idan na tuna gwagwarmayar da muka sha, da yadda abubuwa suka juye, har zuwa yadda aurenmu ya kasance, sai naji ina girgiza kaina kawai, hikimar Allah da ikonsa suna da ban al’ajabi.
Can kasar zuciyata, na kasa yakice wata murya da take mintsini na, ‘shin ban ga aya ba?!’.
Yaya ya shafo kumatuna da bayan hannunshi, hakan yasa na bude idanun da ban san na rufe ba, na sauke su a kanshi. I can’t help myself, duk lokacin da zan kalle shi, sai naji tali-talin yawon abubuwa a cikin cikina, tunanin how I’ve come to be this lucky yaki barina.
Yace “tunanin me kike yi ne haka, kin barni ina fama da takarda?”.
Babu tunanin komi nace “kai!”. Sau tari bana tauna maganganu irin haka kafin in furta su, Yaya Bilal has that effect on me.
Shi kanshi bai yi zaton amsar da zan bashi ba kenan, ya daga girarshi cikin mamaki, yana wani irin murmushi, “haba? Akan me?”.
Na kara gyara kwanciyata a jikinshi, nace “ta yadda aka yi ka fara so na mana. Tell me, love at first sight ce, ko kuma sai a hankali?”.
Yaya yayi shiru yana kallona kamar mai tunani, amma kuma har yanzu murmushi yake yi. Yace “kin tuna ranar farko da muka hadu dake?”.
Nace “sosai ma. Ranar da kazo ka daukemu ni da Janan ka kaimu Kaduna, lokacin bikinka da Ameerah idan ban manta ba”.
Ya girgiza kai, na kalleshi in confusion, “no? Ba lokacin bane?”.
Ya jinginar da kanshi akan seat din, hakan ya kara bani damar sake makale mishi.
Yace “zaki iya mantawa, amma ni ba zan taba mantawa ba. How could I?”. Yadda yayi maganar ne, yasa na daga kai na kalleshi. Idanunshi na kaina, cike suke da longing da ban taba katarin gani a cikin idanunshi ba.
“Akwai wata rana, da ban san dalili ba, kawai tsintar kaina nayi a cikin mota na tafi Funtua. Ban sani ba, tunanin Yaya Sa’a ne a cikin raina ko kuwa Janan? Na kasa mantawa. Sai dai duk wadannan tunanikan sun bi iska lokacin da nayi tozali da kyakkyawar halittar dana kusa bugewa da motata lokacin dana dora idanuna a kanta a karo na farko. Ban san cewa a take a lokacin tayi awon gaba da zuciyata ba sai da nayi nisa, nisan da ba zan taba iya dawowa daga inda na tafi ba har abada”.
Kallonshi kawai nake yi cike da alamun tambaya don ban fahimci inda maganganunshi suka sa gaba ba.
Ya kalleni yana murmushi sosai, da alamu ba karamin dadada mishi rai abinda ya tuno yake yi ba, yace “kin tuna watarana da kuka shiga staff quarters ke da Janan siyan wani abu, meye ma sunan?”.
Na zare idanu na kalleshi, mamaki kamar zai kashe ni, ta yaya ma aka yi na manta ranar?.
Watarana muka taba shiga cikin staff quarters, makotan gidan su Anty Sa’a a lokacin suna saida iloka, muka je saye. Ga takaicinmu muka samu babu, akan hanyarmu ta fitowa, muka ci karo da wani kare. Nan muka yi cak muna kallon-kallo dashi, yana shirin juyawa ya kara gaba, kawai Janan da dama tunda muka ganshi, ta fara rawar jiki, sai kawai ta dafe keya ta ranta ana kare. Shikuwa kare yace da wa Allah ya hada mu idan ba daku ba! Nan muka kafa tsere.
Tabbas, wannan rana itace ranar farko da muka fara haduwa da Yaya. Saboda kafin in san abinda yake faruwa, naji mota taja wawan burki, hakan ya tsorata karen ya juya a sukwane. Ni da Janan kuma muka tsaya muna maida numfashi kamar zamu amayar da kayan cikinmu.
Bayan mun gayawa Yaya dalilin daya kaimu nan, neman iloka, ya mana fada sosai. Washegari sai gashi ya dawo da iloka cike da bokiti. Daga wannan ranar duk lokacin da zai zo sai ya taho mana da ita.
Na maida kaina na kwantar a inda yake da ina murmushi, wani irin giddiness ya rufe ni, nace “wow! Lallai ka jima cikin tarkon so na. Amma me yasa baka taba fada min ba?”.
Yace “kece dai baki taba fahimtar duk hints din dana dinga nuna miki ba”.
Na kara daga kai na kalleshi, “wasu hints?”.
Kafada kawai ya daga. Don haka nima na komawa previous position dina, wasu sake-saken naci gaba da yi.
*
Zuwanmu Makkah, da sabuwar soyayyar da muka kulla ta sanadiyar confession din da Yaya yayi a cikin jirgi. Hakan bai hana mu yin wasa ko sakaci da ibada ba. Sosai muka dage wajen ibada da addu’a babu wasa balle kakkautawa.
Kwananmu goma sha biyar a Makkah, mun je Madina ziyara kwananmu hudu muka sake dawowa, tuni mun fara shirye-shiryen juyawa gida nan da kwanaki biyar wanda zai yi daidai da washegarin ranar sallah.
Mun fito daga wata babbar mall ni da Yaya, tsaraba ce na fara hadawa. Hannuwanmu cike suke da ledoji masu dauke da tambarin mall din da suna. Muna fitowa hasken rana ya dalle min ido, wani irin jiri ya kwashe. Da ba don Yaya daya taro ni da sauri ba, da tuni na kai kasa.
Ya dubeni cike da kulawa, “lafiyarki lau kuwa? Na kula tun jiya kike jin jirin nan. Ko zamu je asibiti ne?”.