A ZATO NA COMPLETE

Kawai sai ta zube kasa ta fashe da kuka, kukan ihu bayan hari, kukan nadama da bata da amfani. Tana ba Yaya hakuri, wai don Allah yayi hakuri ya maidata, sharrin shaidan ne. Yaya ko kallonta bai kara yi ba, ya ja hannuna zuwa cikin motarshi ya tada. Maigadi ya bude mishi gate ya fita a sukwane, muka wuce Raheemah tsugune anan, crying her heart out.
☆
Wajen aikin su Yaya muka wuce. Kai tsaye ofishinshi da yake hawa na goma sha biyu muka wuce. Muna shiga ya dauki land-line ya kira secretary dinshi yace tayi oda din abinci. Ya zauna akan kujera yana maida numfashi.
Tashi nayi tsam na koma kusa dashi na zauna, na kamo hannunshi na rike a hannuna ina shafawa soothingly. Gabadaya ya ma kasa magana, mun jima a haka, kafin ya iya daga baki. Maganganu suka fara fita daga bakinshi kamar ana turo su, duk akan yadda Raheemah ta cuce shi ne.
Ban ce mishi komi ba sai hakuri kawai da nake bashi har ya dan nutsu, nace mishi “ka daina blaming dinta, abinda Allah ya kaddaro dole sai ya faru babu makawa, babu kuma tsumi balle wata dabara ta mutum. Raheemah ta saka min magani ko bata saka ba, dole cikin jikina ya fita tunda Allah bai kaddaro zai taka kasa ba. Don haka ka daina damun kanka don Allah, don’t beat yourself for it”.
Ya kalleni, “for real baby? How are you this calm? Da kunnenki fa kika ji abinda tace, ita ta zubar mana da ciki. Kin kuma ji abinda likita tace, that ba lallai ki iya kara samun wani cikin ba cikin lokutan nan”.
Murmushi na sakar mishi mai sanyaya zuciya, na kamo hannunshi na dora a saman cikina, nace “saboda shi Allah ba azzalumin bawa bane, baya kuma dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba. Yasan abinda yake cikin zuciyoyinmu, ya kuma fimu sanin cewa muna bukatar ganin sanyin idaniyarmu a gabanmu…”.
Nayi shiru ina kallonshi, ina jiran yayi calculating din abin da kanshi. Ba’a jima ba kuwa ya gama tarawa da ninkawa, ya kalleni, “kina nufin..?”.
Na gyada mishi kai a hankali ina murmushi, gefe daya kuma ina danne kwallar data ciko min ido.
Bakinshi rawa yake, da kyar ya iya kakaro kalmar “how… wata..?”.
Nace mishi “sati biyar”.
Daga nan bai ce komi ba, sai janyo ni cikin jikinshi da yayi ya rungume. Ba sai yayi magana zan san yana cikin tsananin farinciki ba, saboda na sani, wani farincikin yafi karfin ka daga baki ka bayyana shi, saboda duk kokarinka da iya bayyana abu, farincikin nan ba zai taba iya bayyanuwa ba. Halin da Yaya yake ciki kenan a halin yanzu.
Sai da aka kawo abincin da yace a kawo, sannan ya zameni daga jikinshi, yadda ya maida ni cikin kujerar ma ya ajiye kamar wani kwai kadai yasa na bi bayanshi da kallo cike da murmushi, kaunar mijina tana kara dabaibaye ni.
Ya amso abincin ya dawo, da kanshi ya dinga bani abincin nan har na koshi. Daga nan kuma muhawara muka hau tafkawa akan gida zan wuce in huta ba wajen aiki ba, da kyar na samu na iya fahimtar dashi lafiyata lau, kuma zan iya zuwa wajen aikina. Sannan fa ya saka ni a gaban mota ya kaini har ward dinmu, bayan dogon bayanin in kular mishi da kaina fa da baby, ya juya ya tafi. Ya barni da su sister Hajara da suke ta sheka mana dariya.
*
Janan tafi minti biyar tana ihu da shewa, har sai dana kai ga kauda wayar daga kunnena kafin ta kai ga kassara min ji na ina zaman lafiya. Sai data gama ihun murnar, sannan kuma ta hau zuba hamdala, “kai Alhamdulillahi, Allah na gode maka! Yau ina zan kai farinciki a cikin rayuwata?! Finally, Allah ya raba mu da bakar kaska, zamu huta dai. Gari ya waye dukan duhu na yayewa!!”. Ta karasa maganar da take yi cikin sautin wakar gari ya waye.
Hakan yasa na saki dariyar da ban shirya ba. Na dawo gida daga wajen aiki. Duk da cewa ba yau na saba dawowa na tarar da gidan babu kowa ba, sai dai wannan karon da banbanci. Wannan karon nasan cewa komin dare babu wadda zai dawo, zan ci gaba da kasancewa ni daya, ban sani hakan ko abin murna da farinciki bane a gareni ko kuwa na jajantawa?
Janan itama tayi dariyar, “Malama kada ki fuske mana, nasan ran nan naki yau fari tas kamar likkafani”.
Nace “ke fa baki da kirki wani lokacin wallahi, likkafani seriously?”.
Ta kwashe da dariya. Ina tunanin yau dai ba za’a samu yin hira mai ma’ana da ita ba, don haka nace mata taje taci gaba da abinda take yi kawai.
Tace “shine don wulakanci ranar nan kika ce wai baki da ciki?”.
Nace “waya fada miki ina da ciki ne?”.
“Dalla can, an gaya miki zancen duniya yana buya ne? Zancen cikinki ai ya gama zagaye gari da dangi yanzu, har yaron goye yasan da maganar”.
Na girgiza kai kawaI, na manta ba’a maganar sirri da Yaya, musamman wadda ta danganci wannan.
Nace “to naji, je ki cigaba da soyawa maigidanki cin-cin, nima abinci zan zo in dafa mishi”.
Ina jin tana guna-gunin wai kada in mata gorin miji fa, na kashe wayar kawai ina dariya.
☆⋆50⋆☆
Finale
Watanni goma sha uku kenan bayan haka, na samu kaina tsaye a kofar gidan a can cikin unguwar Tudun Wada cikin Zaria. Gida ne kadaran-kadahan, amma zaka fi saka shi cikin jerin gidajen ya-ku bayi. Gabadaya gine-ginen unguwarma haka take, kwata, bumps, ramuka da bola sunyi yawa a wajen.
Muhaaseen, diyata mai kimanin wata biyar dana haifa watanni biyar da suka wuce, tana sakale a kan kafadata gefen damana. Sunan Mamata marigayiya taci. Hannunta rike gam da gululun kwalliyar dake jikin jakata tana ja tare da yin wakokinta na yan yara wadanda basa taba kin kawo murmushi kan fuskata. Yanzunma murmushin nake yi a tausashe, kauna ce ta uwa da d’iya Allah ya sanya mana, ko a halin da take ciki na yarinta, ta sanni sosai. Na kara sakin wani murmushi a karo na barkatai, tare da manna mata sumba a gefen kumatunta. Tana jin motsi na tayi saurin juyo da fuskarta, tare da kamo lebbana tana tsotsa, na saki dariya a hankali, gefe guda kuma ina kai hannu ina kara buga kofar gidan.
Bayan wasu dakikai, har na fara tunanin kila ko babu kowa a gidan. Ina shirin juyawa kenan, naji ana taba kofar da daga gani wani katon abu aka sanya daga ciki aka tokare saboda yanayin yadda kofar ta nuna, taga jiya da yau sosai, babu alamun zata iya daukar kwado ko makulli daga ciki.
Wata siririyar bakar mata ta bude kofar, muka tsaya muna kallon-kallo da ita. Yadda ta zare idanu tana kallona cikin wani yanayi mai kama da mamaki da kuma tsoro da shock yasa na kara kallonta sosai, a zuciyata ina tunanin ko na santa?.
Murya na masifar rawa ta ambaci sunana, “Na’ilah?!”.
Sai a lokacin ne fahimta ta saukar min, nace “Raheemah ce?”.
Tayi kasa da kanta a kunyace, kafin ta dago tace min “shigo mana!”. Ba musu na daga kafa na bita cikin gidan.
Kwanaki masu yawa da suka wuce, lokacin da naje Kaduna haihuwa, nake jin labarin hatsarin daya aukawa Raheemah din da ‘yan’uwanta a hanyar Nijer. A cewar wadda take bada labarin, mahaifiyarsu a take ta rasu, su kuma sun samu sun fito da kyar, rabin jikin Salame ya kone da wuta, Raheemah kuma Allah ya takaita ta fita ba tare da wasu munanan raunuka ba sai tsagewar kashi da kurjewa nan da nan kawai.
Mummunan hadari ne motar golf din tayi da wata babbar motar mai, Allah ne kadai ya nuna ikonsa da har wasu suka iya fita da rai.
Tun a wancan lokacin naso zuwa yi musu gaisuwa kwarai, Allah bai nufa ba. Sai yanzu da muka shigo Zaria jiya ni da Yaya. Wani babban aminin Babansu ne tun yarinta yayi rashin lafiya har aka kwantar dashi a asibiti. Bayan an sallameshi ne Yaya yace zai zo ya duba jikin nashi ya kuma ga ‘yan’uwa, nima na nuna sha’awar ina so in biyo shi. Ko babu komi nima na jima rabona da Zaria.