A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Can ainihin gidansu na Hanwa na taba zuwa, aka ce min ai tun bayan rasuwar mahaifiyarsu suka koma wajen mahaifinsu da zama. Don haka na juya akalar tafiyar tawa na taho nan, da kyar da kwatance na karaso. Wai don ma mahaifinsu ba boyayyen mutum bane a unguwar.

Tana tafe ina binta a baya, yanayin gidan kawai da suturar jikinta nake karewa kallo, tabbas, babu wanda zai kalli Raheemar dake gabana yanzu yayi tunanin hadata da Raheemar baya. Wato kawai a duk halin da mutum ya tsinci kanshi a rayuwa, ya godewa Allah ne.

Dakin data kaini yafi kama da akurki maimakon falo, babu komi a ciki sai tarkacen kaya iri-iri, daga kwanukan abinci, bokitai, kayan wanki, gasu nan dai birjik kudaje na bi abin babu kyan gani. Ta dauko wata yamutsattsiyar tabarma ta shimfida min a tsakiyar falon, na zauna ina kara kallon wajen.

Tsayawa tayi kikam a kaina tana kallona tana faman susar kai kamar mai fama da kwalkwata, “me ya kawo ki nan wajajen?”.

Sai lokacin na maida kallona kanta, “naji rasuwar Momcy ne shine nazo muku gaisuwa. Ya hakuri? Allah ya jikanta”.

Maimakon ta amsa min kawai sai naji ta saki dariya, “hahhh.. Su Momcy fa lokaci yayi, hmm!”. Ta wani ajiye numfashi. “Ai in gaya miki, labarin wani zazzafan malami muka ji acan cikin Nijer, shine fa muka kama hanya muka tafi. Muka je ya bamu magunguna, wanda zai sa Bilal ya sake ki ya manta dake da cikin jikinki ni kuma ya maida ni, ita kuwa Halimo ta karkato hankalin wannan shegen tsinannen mijin nata kanta, kawai ba sai muka ci karo da motar mai a hanya ba? Sakaran direba kawai, yana ta wa Momcy surutu akan ta bashi lambar wayarta ya hada mu da motar. Dan iska!”. Ta ja tsaki kafin ta kwashe da dariya.

Ni kuwa da nake ta binta da kallo cike da mamaki, na sake ware idanu ina kallonta. Dama naji Janan tace wai ance tun bayan rabuwarsu da Yaya, kamar kwalwarta ta tabu haka take, ban tabbatar ba sai yanzu. Ta kalli Muhaaseen da tunda muka shiga gidan ta makalkaleni, haka take duk lokacin data ganta a gaban mutanen da bata sani ba.

Ta zare ido, “laa, wannan ce diyar da kika haifa? Amma fa kyakkyawa ce!”. Ta kai hannu kamar zata dauketa, yarinyar tayi saurin kara makalewa a jikina, ni kuwa na sanya hannu na kara riketa tsam a jikina, a can kasan raina ina cewa Tubarkallah. Duniyar yanzu baka san bakin mutane ba.

Ganin na riga na gama yin abinda ya kawo ni, ga wani irin wari da yake tashi a cikin falon da yake kokarin tasar min da zuciya, yasa na mike tsaye ina cewa “bari mu tafi, sai anjima”.

Tace “da wuri haka?”.
Na kalleta cikin rashin abin cewa, idan na tsaya mai hakan zai kareta dashi?

Tace “to shigo ki duba jikin Salame mana”.
Bata jira nace komi ba ta tunkari wata kofa, cikin sanyin da jikina yayi na bi bayanta.

Ina shiga dakin nayi baya da sauri, wannan warin da nake ji a falo sama-sama ya bugo ni full force. Sai lokacin na fahimci daga inda warin yake fitowa. Daga inda nake na hango Salamen kwance acan kuryar dakin kamar kayan wanki akan shimfida, rabin jikinta lullube da mayafi inda aka sakaya private parts dinta.
Naji wani irin tsoron Allah ya kamani a lokacin, lallai shi dai mutum ba a bakin komi yake ba a wajen Allah.
Kamar yau ne fa, suka tareni suna min dibar albarka a cikin gidan aurena, akan mijin da nake aure. Yanzu dana duba baya, lallai ba karamin lokaci bane ya wuce, amma kuma a cikin kaina sai nake ganin kamar yau hakan ta faru.

Da kyar na iya karasawa kusa da ita, da alama ma barci take yi. Itama gefenta kwanuka ne birjik a ajiye, wasu ma daga ganinsu ba karamin lokaci suka dauka anan ba.
Nace “har an sallameku daga asibiti ne?”.

Tace “ina fa! Koro mu suka yi saboda babu kudin gado dana magunguna. Ni kuwa nace aikin banza kenan, muka maidota gida. Ai yanzu maganin gargajiya ma ake mata. Shima kwana biyu dai an daina bata ma”.

Na gyada kai a hankali, ina so in kara watso mata wata tambayar, amma bakina ya kasa budewa, don haka na dinke bakin nawa kawai na mike tsaye. Ina ji Raheemah ta biyo bayana tana wasu surukai dana kasa fahimtar abinda take cewa, na dai tsinci sunan Salamen da kuma zagin da take dankarawa.

Na kara rike Muhaaseen sosai ina kokarin sanya takalmina, wani zagi data saki ne yasa na daga kai na kalleta cikin mamaki. Tace “kan ubar nan!! Wannan shegen hadadden takalmin fa? Zai yi dubu nawa? Kai, wallahi dama ki bani shi in dinga kwalliya dashi abina”.

Ni yanzu tsoro ma take bani kuma, yadda tayi tsaye a kaina tana watso min hakoranta da tsabar rashin wanki yasa suka yi wani yalo-yalo, gani nake kamar a kowane lokaci zata iya kawo min mazga. A karo na farko na fara tambayar kaina tsautsayin daya kawo ni nan. Musamman idan na tuna ta yadda ma aka yi Yaya ya barni na zo gaisuwar nan.

Ban ce mata komi ba, na tunkari kofar fita da sauri, ta biyo bayana. Muna gab da kofar gidan hayaniyar yara ta kusantomu, ihu kawai kake ji da kururuwa.
Haleemo da itama babu banbanci tsakaninta da Raheemah, duk da ita suturar jikinta da yar dama-dama akan ta Raheemah, ta fado gidan hannu rike da fararen manyan plastic bokitai da sauran shinkafa da tarin kabeji a ciki. Tsinin dake cikinta zaka fara gani kana dora idanu a kanta.

Waka da shewar da yaran suke yi ta kara yawa,
‘Yar iska taki zaman aure, daga talla sai yawon iskanci!
‘yar iska tayi cikin shege…!

Ita kuma tana korarsu da kayan hannunta tana dankara musu zagi da tsinuwa, har dai Allah ya bata sa’a ta shigo gidan ta maida kyauren ta rufe da sauri tare da daukar wani gingimemen dutse ta jingina da jikin kofar.

Tana juyowa ta kallemu tayi turus! Ta kalli Raheemah tace “wannan fa wacece?”.

Raheemah din ta watsa mata harara da sauri, “to uwar yan tsegumi, ina ruwanki da bakuwata?”.

Ta tabe baki, “jibeta sakara kawai, banza mai tabin kwakwalwa, to sai me don kinyi bakuwa? Daga gani ma kuskuren gida tayi ba wajenki tazo ba don daga gani bata yi kama da irinki ba”.
Raheemah ta tunzura da abinda tace “na dai gode Allah, duk da tabin kwalwar tawa dai ban je nayi cikin shege ba!”.

Ta daga baki kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa, tayi cikin gidan tana “oho miki dai, mahaukaciya”.

Ba shiri na kama dutsen nan na janye da sauri na fita daga gidan, Raheemah ta sha gabana tana wasu yan soshe-soshe.
“To Hajiya Na’ilah, na gode ko? Yaushe zaki sake dawowa? Gashi kin zo ko ruwan sanyi ba’a baki ba. Nasan ba zaki iya shan ruwan randa ba, ni kuwa bani da ko sule balle ko na fiya wata ne a sayo miki”.

Ganin take-taken bata da alamar rabuwa dani don wasa da kuma abinda take hinting, yasa na zage jakata na ciro kudin da ko kirga su banyi ba, na mika mata. Ta warta kamar wadda take tsoron zan kwace ta jefa su cikin rigarta. Sai data tabbatar ta boye kudin sannan ta juyo ta hau zuba min godiya, tana lissafo abubuwan da zata sayo taci dasu ta hana ‘yan uwan. Ban kara cewa komi ba na juya da sauri, ina ji kamar ma in sheka da gudu. Jindadina daya, da bata sake biyo ni ba.

Na bude wajen direba a motata Benz, ruwan ash mai haske sosai daya zama kamar white-gold, wadda na saya da kudina da albashina duk da dai sai da Yaya ya min ciko, lol.
Na maida kofar na rufe, na kwantar da Muhaaseen a seat dinta dake bayan motar. Sannan na sauke wani dogon numfashi da ban san na rike ba.
Sai dana nutsu, sannan na tashi motar tare da ja na fita daga cikin unguwar a hankali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button