A ZATO NA COMPLETE

*
Na kwankwasa kofar dakin Yaya sannan na tura kofar na shiga.
Yana zaune a tsakiyar dakin akan carpet, Muhaaseen na kwance akan cinyarshi tana yan wasanninta na yara. Laptop dinshi da tarin takardu da jaridu shimfide a gefenshi suna jiran ya karkata hankalinshi garesu. Hankalinshi baya kan su though, kai gabadaya ma baya cikin dakin. Idanunshi na kan Muhaaseen, kamar wanda yake kula da duk wani motsi da tayi, sai dai daga gani kawai idanunshi ne suke kallonta, amma gabadaya hankalinshi baya ma cikin dakin. Tuni yayi nisa a cikin duniyar tunani.
A nutse na ajiye farantin dana shiga dashi a kusa dashi. Karamar kettle ce dana zuba shayi a ciki, sai fresh grapes da berries a cikin wani bowl.
A hankali na kai hannu na dauke Muhaaseen daga jikinshi. Yayi firgigit! Ya zabura yana kallona a dan rikice.
Na kalleshi cike da alamun tambaya, kusan kwananmu takwas da dawowa daga Zaria, amma na kasa gane kanshi. Duk lokacin da zaka ganshi, a zaune yake ko yayi tagumi, ko kuma yayi zurfi cikin tunani. Haka a yawancin lokuta zan tashi cikin dare in ganshi zaune a tsakiyar gado cikin zuzzurfan tunani, sai dai duk lokacin da zan tambayeshi abinda yake faruwa sai dai ya girgiza kai kawai. Ko yace ya gaji ne, ko aiki ne ya mishi yawa, ko kuma wani abu dai. Wanda daga ni har shi mun san cewa ba haka bane.
Amma gabadaya yan kwanakin nan naga abubuwan nashi sun fara yin yawa, na kula har wasu dark spots sun fara fito mishi a kasan idanunshi alamun akwai abin da yake matukar damunshi.
Ban ce mishi komi ba, na tura mishi plate din dana shigo dashi. Cikin sanyin jiki ya janyo laptop dinshi ya fara aiki, na kula da yadda hannunshi yake dan yin rawa slightly. Nan ma na kauda kaina. Na dauki inabin tare da kaishi saitin bakinshi. Ya dago kai ya kalleni yayi dan murmushi tare da daga bakinshi ya karbi inabin, sai daya hada da yatsata ya dan ciza.
Da sauri na janye yatsar tare da sakin dan kara a hankali, hakan yasa Muhaaseen dake kan cinyata ta zabura. Nayi saurin fara lallashinta ina hararar shi ta kasan ido, yayi kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai dan siririn murmushin daya saki na tsokana.
Ina gama lallaba Muhaaseen tayi barci, na kwantar da ita a cikin crib dinta dake gefen gadon da muke kwanciya. Na sake komawa gefen Yaya na zauna, yana aikinshi ni kuma ina cin abubuwan da na ajiye ina kuma bashi, har muka gama su. Sannan na dauke kayan na kai kicin. Sai dana tsaya na kashe duk wasu abubuwan wuta sannan na wuce dakina, nayi shirin da zanyi na kwanciya sannan na koma dakin Yaya.
Har yanzu yana zaune inda yake, sai dai ba aiki yake yi ba, al’adarshi ta tunani yake. Raina gabadaya naji ya dagule.
Na zauna a gefenshi tare da nade kafafuna sosai ina fuskantarshi, cikin sanyin murya nace “Abban Maama, wani abu yana faruwa ne?”.
Yayi saurin girgiza kai yana kokarin mazewa kamar yadda ya saba, “me kika gani?”.
Nace “meye ma ban gani ba? Wani abu ya faru ne a Zaria? Tun muna can fa na kula da canzawar da kayi, ina kuma ta tambayarka amma sai dai kace min babu komi. A tunanina ni din abokiyar shawararka ce, kamar yadda kake abokin shawarata?”.
Da sauri ya hau gyada kai kamar wani karamin yaro, “haka ne baby, na sani. Just… Ban ma san ta inda zan dauko zancen bane”.
Jin haka yasa na kara matsawa kusa dashi sosai, “to menene? Ka fada min, kaji? Idan ma wani abu ne da yafi karfinka zamu iya hada karfi da karfe, idan ma yafi karfinmu dai duk babu abinda zai gagara, kaji? Menene?”.
Yayi shiru yana kallona cikin tunani. Kai ya girgiza kawai, “I’m sorry baby, maybe next time, amma ba yanzu ba”.
Nayi kasa-kasa da ido, “Yaya…!”
Sai dai ban kai ga karasa fadar abinda nayi niyar fada ba, naga ya tashi da sauri kamar wanda aka mintsina yayi hanyar bayi. Na bishi da kallo cike da tsananin mamaki, a hankali wani abu mai kama da takaici ya tsaya min a makoshi. A ganina ina laifin wanda ya damu da damuwarka? Akalla kullum zan tambayi Yaya abinda yake damunshi, yafi sau a kirga. A tunanina, ko bai fada don muyi maganin abin ba, ai zai fada ko don raba damuwarka da wani kamar ka cirewa ranka rabin damuwar ne.
Nayi kwafa a hankali tare da mikewa tsaye ina karkade kayan jikina. Ko kofar bayin daya shiga ban kara kallo ba, na wuce wajen da Muhaaseen take kwance na tofe ta da addu’o’i. Na haye kan gado tare da shafe nawa jikin nima da addu’ar kwanciya barci.
Ban ma san lokacin da Yayan ya fito daga bandakin ba saboda lokacin barci ya fara daukata. Daga can dai naji lokacin daya hayo kan gadon ya kwanta tare da laluboni jikinshi, nayi banza na share shi. Kodayake, shariyar ta dan lokaci ce, babu shiri na manta da dan guntun fushin da nake yi na kara kwantar da kaina akan faffadan kirjin mijina.
Cikin tsakiyar dare na farka, tunda na laluba gefena naji babu kowa nasan cewa Yaya sana’ar yake yi. Na mike zaune da kyar tare da daukar bargo na rufe saman ruwan cikina dashi, saboda sanyin da yake dan bugowa a lokacin.
Kamar yadda nayi zato, zaune yake a gefen gadon, ya zira kafafunshi ta kasa, kanshi a kasa, ban sani ba duk cikin tunanin ne, ko kuwa barci yake yi a haka?.
A hankali na kai hannu na dafa samar kafadarshi, daga yadda jikinshi yayi tensing, nasan cewa idanunshi biyu.
Nace “Abban Maama…”.
Kaico! Masana iya magana dama sukan ce wai rashin sani yafi dare duhu, kuma dana sani k’eya ce.
Da ace nasan kalmomin da zasu fito daga bakinshi, da ban farka ba, da ban yi tunanin yi mishi magana ba a tun farkon fari, dana sani da naci gaba da kwanciyata koda kuwa na kasa komawa barci. Ban shiryawa jin abinda ya fito daga bakinshi ba.
“Na’ilah, aure zan yi!”.
Kalma mafi muni data taba shiga cikin dodon kunnena a cikin tarihin rayuwata kenan. Naji duk wasu ayyukan dake wakana a cikin kwalwata sun dakata da aiki, kai ni a karan kaina sai naji ni kamar wata sassaken sak’ago, ko wata statue. Na kasa numfashi, na kasa motsa komi a jikina, na kasa tuna komi a cikin raina. Wadannan kalmomi hudu daya furta, su kadai nake fahimta, su kadai kuma suke min yawo a cikin kaina.
Ban san lokacin daya juyo ya fuskanceni ba, sai da naji hannunshi da a da, idan ya taba ni dasu na kanji duk wata gajiya da wahala dake tattare dani ta gudu daga jikina a take, amma yau ya banbanta. Sai naji kamar ya dauko duk wata gajiyar duniya ya dora min ne, babu shiri na fara kokarin zame nawa hannun daya kama, amma bai bari hakan ta faru ba.
“Na’ilah, baby, ki saurareni don Allah, wallahi ba wai don bana sonki bane zanyi wannan auren, I love you more than anything in this world, bani da zabi ne, don Allah ki saurareni, kinji?”.
Na daga idanuna da na kasa tsayar dasu waje daya. Daga jin zafin da suke min, nasan cewa cike suke da hawaye, sun kuma canza kala. Cikin muryar da ni kaina sai dana yi mamakin jin ta fita daga bakina, nace “me kace?”.
Ya kara damke tafin hannuna cikin nashi, “please baby, ki bari in fara miki bayani kafin…”.
“aure kace?”, na katseshi ta hanyar jefe mishi wannan tambayar, ba tare da tunanin maganganun da yake fada ba.
A hankali, kamar wanda yake tsoron wani abu, ya daga kai sama.
Ban san lokacin dana kwace hannuna ba, na dira daga kan gadon cikin wani irin sauri da rawar jiki da ban taba zaton akwai irinsu a duniya ba.
Yaya yayi kokarin sake kamo ni, amma ina! Gabadaya duk wani sauran tunani daya rage a jikina yayi kaura. Ture shi na sake yi. Daya matsa da kiran sunana da kokarin kamo ni, sai kawai na kasa da gudu. Na fada dakina na maida kofar da sauri na kulle da makulli na hada da sakata.