A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Cikin mamaki nake kallonta, “ban san daga ina kika dauko wannan kalar abu ba Maryam, amma hakan bai kama ce ki ba gaskiya. Ta ya kike zaton Mamanki zata dauki wannan maganar idan taji irin shigar da kike boyewa a cikin hijabi? Don daga ji nasan cewa wannan ba shine karonki na farko ba”.

Tayi dariya tana watso min wani kallo irin ‘are you kidding me’ dinnan Tace “me Mama zata ce kuwa? In fada miki gaskiya ita ta bani shawarar in dinga sanya after dress idan zan fita, in naje can inda zan je sai in cire saboda kada wani idon sani ya ganni a haka… Amma meye na wani boyo? Zamaninmu ne fa!”.
Tunda ta fara maganar bakina a hangame yake a bude, Subhanallah! Yaushe yaran gidanmu suka fara bin wannan hanyar ne? Nasan cewa tsakanin iyalan dama babu hadin kai da kaunar juna, saboda tun farko basu ga hakan daga wajen iyayensu ba, amma wannan wani babban al’amari ne, wanda nake ganin idan har aka bari ya girmama, akwai matsala. To amma, abinda uwa take supporting da dukkan karfinta, waye yake da karfin hana ta?

Ta tunkari kofa zata fita tana furta, “bari in zo inyi sallah!”.
Ina nan zaune ina ta saka da warwara ta dawo, ta shimfida abin sallah ta kalli gabas. Yadda take yin Sallar ma kadai abin zai baka mamaki. Kamar wadda bata taba taka ajin islamiya ba Raka’o’in data jero masu yawa yasa na fahimci cewa ba sallar isha’i kadai tayi ba.

Sai dana bari ta gama duk abinda zata yi, har ta kwanta sannan na dubi inda take, nace “ni kuwa a wani matakin karatu kike yanzu a islamiya?”, na dai san cewa yanzu tana ss2.
Tayi dariya, “na kusa wata ma ni rabona da makarantar nan yanzu, yan ajinmu aka wa karin aji zuwa na yan sauka, ni kuma aka barni a ajin baya shi yasa na daina zuwa ma kwata-kwata”.

Na tashi zaune sosai ina kallonta, sanin halin Maryam na saurin fahimta da ganewa yasa nafi jin dadin zama yi mata magana ko gyara akan wani abu, ba kamar Aliyu ba. Sau tari dan karamin gyara sai ya kaimu ga ya kalli tsakiyar idanuna ya zage tas kamar wanda yake jira dama.

Nace “kin san fa yanzu kece babba a gidannan Maryam. Kuma duk abinda kika yi, kannenki da suke tasowa shi zasu dinga yi. Yanzu idan basu ga yayarsu na zuwa makaranta ba, ta ya kike tunanin zasu samu kwarin gwiwar zuwa makaranta? Kinga ke dai baki da bakin cewa su zo su tafi, tunda kema ba zuwa kike yi ba. Sannan dubi dai irin shigar da kika yi yanzu, ya Baba zai ji, kuma me kike zaton zai ce duk ranar da yaci karo da irin wannan abu da kike yi? Maryam, kinga ke diya macece, sannan yarinya, kada ki bari rudin duniya da abokai ya rude ki, ki saka kanki cikin rayuwar da tafi karfinki. Shiga irin wannan da kike yi ta nuna jiki, ki shiga cikin kawaye ana ta cakuda da maza, akan wane dalili? Ina kika baro tarbiyar gidanmu da kuma al’adarmu ta hausa/fulani?”.

Tayi kasa da kanta a kunyace, “wallahi Yaya, Mama ce take cewa in dai ba za’a hada mu da yan ajinmu ba, sai dai in daina zuwa makarantar. Kuma ita take sawa inyi shigar. Ranar ma ana bikin Na’imah dana sanya hijabi sai ta hau fada, tana cewa wai ni ban waye ba!”.

Na girgiza kai cike da jimami, iyayen yanzu yawanci su suke bada gudummawa wajen lalacewar tarbiyar yaranmu. Uwa ce wai zata dorawa diya akidar yafa gyale da saka suturun banza, ita zata sanya mata akidar bin kawaye da samarin banza, daga karshe kuma idan lamari yazo ya bace bakinta ne zai fi na kowa wajen ihun cewa an lalata mata tarbiyar yara, bayan kuma itace tayi contributing wajen lalacewar tata.

Tsam na tashi na koma kusa da ita na zauna tare da dafa kafadarta, nace “idan tayi hakan ba laifi bane, tana so ne ki zama abar kallo, kamar tauraruwa. Sai dai, zaki iya zama fiye da hakan ma, ba kuma sai kin sabawa Ubangiji ba, kin gane?”. Ta daga kai.
Nace “good. Saboda haka gobe zamu je islamiyar taku, zan samu malaman naku muyi magana dasu. Sannan don Allah, shiga ta banza mai nuna jiki, ki daina yin ta. Ko ba don ke ba, ki duba kimar da Baba yake da ita a idanun mutane, balle ke kanki idan baki kame kanki a matsayinki na ya mace ba, Maryam zaki ga kin rasa girmamawar mutane, kin fahimce ni?”. Nan ma ta gyada kai.

Nayi murmushi cike da jindadi. Yanayin yadda jikinta yayi sanyi ya nuna min cewa taji, kuma ta dauki abinda nace. Na rungumota gefen kafadata ina kara yi mata bayanai da nasiha akan rayuwa. Daga karshe dai na janyo laptop dita na kunna mana kallo a ciki, babu TV a dakinmu sai na Baba dana matanshi, yawanci can muke zuwa muyi kallo. Ranar akan katifarta na kwana.

Tunda Baba ya tashemu sallar asuba ban koma barci ba. Ina gama azkar din dana saba yi lokacin gari ya fara yin haske, na fita na share tsakar gida tas. Na hada kayan wanke-wanke nayi, na shiga kicin na kunna wuta tare da dora ruwa wanda yara zasu yi wanka dashi na kuma dora musu abincin da zasu tafi makaranta dashi.
Har wajen karfe bakwai na safe ban ga motsin kowa a tsakiyar gidan ba. Matan sun riga da sun san dama ni nike ayyukan gidan, shi yasa daga ranar da nazo, har in bar gidan babu wadda take ayyukan gida. Duk da har yanzu Ramata bata sakar min ragamar ayyukanta ba, ranar girkinta ita take yin girkinta gabadaya, wanke-wanke da shara ne dai take bari na dasu. Hakan bai dameni ba.

Yanzun ma ina kan zuzzubawa yara taliyar dana dafa musu a cikin kulolim makaranta, sai gata ta fito daga dakin Baba. Kicin din ta shigo, na gaidata ta amsa. Tukunyar ruwan zafi ta bude, ta zuba daidai wanda zata hadawa Baba shayi ta fita daga kicin din.
Daya bayan daya yaran suka fara fitowa, na dauki kofi ina zuba zuzzuba musu. kowannensu yazo, sai ya duka ya gaida ni, ni kuma sai in mika mishi kofin shayi da biredi ya amsa ya tafi.
Maryam da take tsaye a gefena tun dazu, tayi murmushi lokacin dana mikawa Auwal nashi kofin shayin bayan na shafa kanshi.
Tace “shi yasa nake son ki zo gida wallahi, yaran nan sun fi behaving. Yanzu da ni ce da har yanzu ina nan ina ta faman su zo su amshi abincin, amma su ki”.
Nayi dariya, “kin san yara sai da lallashi da lalama. Yadda nasan halinki na zafin kai dama, ta ina yara zasu dinga binki sau da kafa?”.
Duk muka yi dariya ni da ita. Itama na zuba mata nata ta tafi ta karya.
Ban fita daga kicin din ba sai da duk suka tafi, sannan nima na zuba nawa nan tafi daki na karya.

Bayan na gama gyara kicin, wanda nasan idan ban gyara ba haka zan dawo in same shi. Musamman ma tunda yau da safe Ramata ta fita daga girki. Haka kuma Anty Alawiyya zata shiga tayi nata girkin ta barshi kaca-kaca. Na girgiza kai cike da takaicin halayen wannan matan.
Dana gama da kicin daki na koma shima na gyara shi. Kai tsaye wanka na fada, na sanya riga da zani na atamfa, dinkin single da fitted riga. Sallama na wa mutanen gidan na shiga cikin unguwa. Daya baya daya na bi gidajen makota muna gaisawa, daga karshe na dire a gidan su Kulsum, a raina ina ayyana sai da yamma sannan zan je nata gidan, in yaso bayan magriba sai in dawo.

Ina yin sallama a tsakar gida, na ja nayi turus ganin yar halas din a tsakiyar gida tana wa yarinyarta yar shekara uku, Muneerah wanka.
Tana ganina tayi murmushi, “saukar yaushe?”.
Nayi dariya ina zama a gefenta, “jiya da yamma wallahi. Me kike yiwa mutane a gida haka tunda safiyar Allah Ta’ala? Inna ina kwana?”. Na gaida Inna data fito daga cikin madafi. Inna ta amsa tana min sannu da zuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button