A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Janan ta kame baki, tace “Innalillahi! Na’ilah, kece kuwa ko dai wata ce mai kama dake?”.
Nayi murmushi nace, “shafa ki ji!”.

Ta jinijina kai, “Allah kenan! Kuma rayuwa kenan, babu abinda ta bari. Idan wani yace min akwai rana da zata zo ki tausar da wani akan zama da kishiya, wallahi ba zan taba yarda ba”.

Na gyada kai a hankali, ko ni kaina ina mamakin kaina.

A shekaru biyar ko shida da suka wuce, idan wani ya fada min cewa zan zauna in fadi wani alkhairi game da zama da kishiya, hakika da idan muka fara fada dashi babu wanda zai iya raba mu dashi sai Allah.
Ban taba zaton akwai lokacin da zai zo, in so kishiya ba, in kuma kaunace ta, ban taba ba.

Duk a zato na, kishiyar bala’i, masifa ce, wadda zata kawo maka rashin zaman lafiya da kowa naka, wadda zata kawo maka bakin jini ta sanya maka cuta a cikin jiki da zuciyarka. Ashe duk rashin fahimta ce ta kawo hakan.
A zato na, bata nufar kowa da alkhairi sai sharri. Nayi zaton tana shigowa tunanin fitar dani daga cikin gidan aurena zata fara yi, sai naga banbanci.
Tabbas Anty Sailu tayi gaskiya, da tace ba duka aka taru aka zama daya ba. Duniyar Allah mai fadi ce, ba’a rasa mutanen kirki a cikinta. Kamar yadda ba’a rasa abokan zama na gari a cikinta.

Ina ga ni nayi dace ne sosai, Allah ya hada ni da wadda ban taba zaton zan hadu da ita ba.
Koma dai menene, ta dalilinta sai gashi ina kallon abokiyar zama da wani ido daban, in a different way, in a different light.
Ta saka ni fahimtar cewa, tsanar kishiya dana taso ina yi, saboda banyi dacen haduwa da mai halin kirki bane, wadda take kaunar zaman lafiya da zaman aminci da amana.
Ramata dama can halinta mara kyau ne, irin mutanen nan ne da dama can tun asali basa son wani daban ya rabe su ko wani nasu, sun fi son komi ya kasance nasu ne su kadai, basa son cigaban kowa sai nasu. Saboda haka ne suke yin duk abinda suka ga zasu iya, don su ga cewa sun kawar da duk wani abu da zai yi threatening dinsu da cigaban su. Saboda haka ne su son kishiya ko diyanta, baya cikin lissafinsu, me yasa zaka so abinda kasan cewa ya fika matsayi a inda kake so kaga cewa kafi kowa matsayi?.
Haka Raheemah, haka ma Ameerah.

Na fahimci cewa su irin wadannan mutanen, son zuciya da son kai ya musu yawa. Shi yasa basa tunanin komi, kuma basa tunanin kowa sai kansu.
Ita kuma duniyar yanzu, cike take da mutane masu son kai da son zuciya, yan kalilan ne masu son farincikin wasu da cigaban wasu.

Duk ban fahimci hakan ba sai a dalilin zaman da nayi da abokiyar zama na, Hajara. Yanzu zan iya fada da alfaharina, cewa ita ba kishiya ta bace, ‘yar uwa ce. Ta dalilinta idanu na suka washe sosai, har nake iya dauko uzurirrika akan dalilin da yasa wadanda na zauna dasu a baya suka dinga yin abubuwan da suka yi din, sai naji na dan fahimce su. Duk da cewa naga rashin wayonsu, tausayinsu yafi rinjayata.
Dama sun bi ta wata hanyar da ba wannan ba.
Dama basu biyewa rudin duniya, shawarar abokan banza, da bakar zuciyarsu ba.
Dama sun bi ta hanyar data dace, dama sun sowa wasu daban irin rayuwar da suke sowa kansu.
Watakila da yanzu muna tare dasu cikin aminci kamar yadda muke zaune da Hajara.

Kwanaki naji cewa Ameerah ta samu tayi aure da kyar, bayan manema kusan shida na fitowa suna guduwa saboda zancen dalilin da yasa ta bar gidanta na farko da suke ji. Sai daya zama kamar ma kyautar da ita ma iyayen suka yi. Gidan mata uku aka kaita, itace cikon ta hudu. Ga tarin ‘ya’ya. Hakan yasa ni zama wani tunani, duk wata kauna da iyayenki zasu nuna miki a matsayinki na ‘ya mace, ta dan lokaci ce. Dole dai gidan aure nan ne gidanki na har abada. To ko meye amfanin shiga cikin rayuwar auren ‘ya’ya da iyaye suke yi? Bayan sun san cewa, daga ranar da ka karbi sadakinta, duk wani hidima nata da komi nata ya tashi daga karkashinsu ya koma kasan wanda ka aurawa? Yakamata iyaye su bude idanunsu, su kuma kula da cewa shiga cikin rayuwar auren ‘ya’yansu mata da suke yi suyi babakere, har su dinga karfafa mata gwiwa akan sabawa miji, hakan baya haifar da komi, sai zubewar darajarsu a idon yaransu da mazajensu, wanda hakan zai iya kawo rabuwar aurensu daga karshe. Kunga anyi biyu babu kenan. Tunda ba kowa bane zai iya zama ya iya jurewa a dinga yi mishi wasa da rayuwar aure.

Na sauke ajiyar zuciya a hankali ina kallonta, nace “baki kula da juyin da aka samu bane? Lokacin da za’a min kishiya nima fa haka kika zaunar dani kina min nasiha da bada shawarwari”.

Ta gyada kai tana murmushi, “kwarai anyi haka. Sai dai ni ban taba zaton idan nawa lokacin yazo ba, zaki maidawa kura aniyarta ba”.

Na hau karewa falonta kallo, hotunanta dana mijinta da ‘ya’yansu, Abdul-Azeez kusan sa’an Muhaaseen, da dan kaninshi Sultan, sun mamaye falon. Shekaru uku da suka wuce aka wa mijinta Al-Mustapha canjin wajen aiki, suka dawo Abuja. Tun daga nan muka kara hadewa, kanmu a hade yake sosai. Musamman da wajen aikinmu ya zama daya, tare da ita muka yi masters dinmu anan wata private university. Hajara ma ta shigo cikinmu. Idan ka ganmu kamar wasu ‘yan uku, babu mai cewa ita din kishiyata ce.
Kulsum ma ta auri wani dan kasuwar kayan masarufi, tana Kaduna abinta da danta Suleiman.

Nace “rayuwar kenan, haka take zuwar ma mutum a bai-bai, cike da ban mamaki da tu’ajjibi”. Ta gyada kai.

Nace “to yanzu ya ake ciki ne?”.
Tace “ni fa dama can ban hana shi yin auren shi ba, ce mishi nayi Allah ya sanya albarka. Kawai ina ta tunanin ta inda na gaza ne da har zai yi tunanin kinkimo min kishiya ya kawo min. Naga dai babu abinda na rage shi dashi. Gyaran jikin nan duk karshen wata yin sa nake, watarana ma kafin karshen watan yayi nayi. Ke karewa ma, VIP ce ni a Tee-Tee’s Care. Ki duba fa yadda fatar jikina take taushi da laushi da komi!”. Ta karasa fada tana nuna min hannunta.

Na matsa gefe guda ina harararta cikin dariya, “dalla can matsa Malama. Wai ke an fada miki wadannan abubuwan suna hana maza karo aure ne idan suka yi niyya? Kawai dai nasan suna kara miki wata daraja a idanunsu musamman idan ita wadda aka kawo miki din bata san sirrin gyaran nan ba”.
Ta gyada kai.
Hakan ta tuno min, lokacin da Hajara ta haifi Suhaima, sai data kusa yin yaji saboda yadda Yaya ya dinga mata. A cewarta, ce mata yayi gabadaya ta canza, yace ta same ni in gaya mata yadda ake gyaran jiki idan aka haihu. Wanda hakan shi ya bata mata rai. Ni kaina naji na tausaya mata, sai dana sameshi kuma na fada mishi hakan babu dadi, kuma bai dace ba.
Saboda tsananin gyaran dana samu lokacin dana haifi Muhaaseen, sai da Yaya yayi min kyauta mai girma. Su Anty Haleemah kuwa da su Fatsu sun sha godiya tafi cikin daro.
Sai dana zaunar da ita na fahimtar da ita muhimmancin irin abubuwan nan, duk da hakan ma dai tana dan yi ne kawai. Su ainihin yan boko ne, irin wadannan abubuwan babu su a cikin dictionary dinsu. Lokacin data fada min haka, ba karamar dariya na sheka mata ba. Kitso da kunshi ma, musamman ma dai kunshin, sai idan zamu je ni da Janan muke jan ta muje.
Mawuyaci ne kaji fadan mu ni da ita, idan ma kaji, ba akan son zuciya bane fadan, abu ne ziryan tsarkakke, ko kuma kawai sabawa da zaman tare yake kawowa. Wannan kuwa is natural, fada ce kuma ta ma’aiki, duk zaman da za ayi shi babu ire-iren samun sabanin nan, akwai alamar tambaya a cikinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button