A ZATO NA COMPLETE

Yana zube kayan akan gado ya juyo ya janyo ni jikinshi, ya nutsa kanshi a cikin gashin kaina, nayi yar dariya tare da zagaye hannuwana a bayanshi.
Yace “ya kike, ya babynmu, hope baya matsa miki ko?”.
Nayi dan murmushi, “dukkanmu lafiyarmu lau. How was your trip?”.
Yace “Alhamdulillah, mun samo fiye da abinda muka je nema”.
Nace “to madallah, haka ake so”.
Mun dan jima a haka, kafin na dago kaina na kalleshi, “kada fa ka tsaida Hajara da jira, nasan itama tayi kewarka, sai da safe ko?”.
Yace “wato har kin gaji da ganina kenan?”.
Nayi dariya ina kama baki, “ni har na isa in ce na gajii da kai? Ban ki mu dawwama a haka ba. Amma bana so mu shiga hakkinta ne ko kadan”.
Yace “to shikenan, sai da safe”.
Nace “sai da safe, ku tashi lafiya”.
Ya wuce gaba na bishi a baya, a bakin kofa ya juyo ya manna min sumba a goshi, sannan ya juya ya tafi. Nayi murmushi kawai tare da girgiza kai, na maida kofar na rufe tare da murza makulli.
Shirin kwanciya barci nayi, na kashe wuta na bi lafiyar gado.
*_...Alhamdulillahi Rabbil-Aalameen. Masha Allah La Quwwata Illah Billah!_*
*Da haka muka kawo karashen littafin 'A Zato Na'. Ina fata Allah yasa mu fi karfin zukatanmu, Allah yasa kuma mu amfana da sakon da wannan littafi yake dauke dashi. Kurakuran dake ciki, Allah ya yafe mana, ameen.*
Ina mika sakon dumbin gaisuwata da fatan alkhairi ga daukacin jama’ar ZAB, bamu da bakin yi muku godiya da baku hakuri amma duk da haka zan kwatanta. Mungode, Mungode, Mungode, Allah ya kara dankon zumunci. Bamu so abubuwa suka kai har haka ba, mun gode kwarai da hakuri da tarin uzurirrika da kuka mana, bamu da abin cewa sai Allah ya kara dankon kauna kawai. Fatan alkhairi gareku bakidaya! Jeedderh Loves you all! ???? ♥ ♥ ♥