A ZATO NA COMPLETE

Na kalli Kulsum, “ko dai awon ciki kika zo ne?”.
Ta dan harareni, “wani irin awon ciki kuma ana zaman lafiya? Mu a gidannan ma muka kwana in fada miki!”.
Jikina yayi sanyi da jin abinda tace, nace “kamar ya? Ban gane ba, wani abu ya faru ne?”.
Inna tace “menene ma bai faru ba yar nan? Ai tafi wata daya a gida yanzu”.
Naji zancen kamar wani saukar guduma a kaina, nace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un!”.
Inna ta girgiza kai kawai, “ai ke dai abin ba’a cewa komi Na’ilah. Sai dai abinda Allah ya kaddara dama babu makawa sai ya faru, sai hakuri kawai”.
Na fara cira idanu tsakanin Inna da Kulsum, Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har ta gama yiwa Muneerah wankan, ta tsaneta cikin zani. Muna zaune ta shiryata cikin kayanta, ta tura ta zuwa wajen Inna. Kallo kawai nake binta dashi.
Tun can nasan cewa dama suna ta faman samun sabani da mijinta Mukhtar. Ko waccan zuwan da nayi dama, sai da suka sha dabi har sai da Iyaye suka shiga cikin maganar. Sai dai wannan karon, jikina yana bani cewa wannan yafi karfin fadan da suka saba yi.
Tana gama hada kan kayan, na ja ta zuwa dakin da yake nata da. Tarin akwatunan dana gani da kuma kayan kwalliyar daki yasa naji jikina ya kara yin sanyi. Na zaunar da ita a gefen gado nima na zauna, tun kafin in daga baki ma in tambayeta ta riga ni, tace “rabuwa muka yi da Abban Muneerah!”.
Na zare ido kamar zasu fado kasa, na kara yin wani salatin dai na sanar da Ubangiji. Ta girgiza kai, “Abban Muneerah ya rikice. Zama yaki ci yaki cinyewa. Ki duba lokacin da aka yi aurenmu, yazo ya hana ni karatu kiri-kiri, haka muka hakura ni dasu Baba. Yazo ya dinga gallaza min a zamanmu, wasu abubuwan ma kawai shiru nake yi. Tun ina kawo kara gida ana mishi fada, har aka daina. Abinci wannan haka ya dinga gagarata a gidanshi, ke kin san yawancin abubuwan dake faruwa. Sana’a na fara yi da kudina, amma haka zai zo ya cinye kudin kuma ya hana ni. Kwanan nan aka ba Inna kudin adashi, ta hada kan kudinnan ta sai min keken dinki, wallahi ko sati uku keken bai rufa ba ya dauke shi yaje ya sayar. Wai kudin toshi ya kai da kudin…”. Kuka ya kwace mata anan.
Na dafata ina lallashinta har tayi shiru.
“Ashe wata ce ya hango a wajen aikinsu. Bai ma gaya min yana nemanta ba, sai a gari naji labari. Wata makociyata ta jiyo labarin take gaya min. Dana tuhume shi, kai tsaye ya amsa babu musu. Na tambayeshi dalili, sai cewa yayi saboda tana da ilimi, kuma ta fi ni hankali da natsuwa. Nace laifin waye to da bani da ilimin? Sai ya hau cewa ni ce sakara ai. Daga wannan rana gabadaya sai ya kara rikicewa, wallahi bamu kara samun zaman lafiya ba. A gabana zai kira ta a waya, su raba dare suna hira, tun ina kuka har na hakura na daina. Iyayenmu duk sun shiga cikin maganar, Kawu Bala da yaje akan maganar baki ji zagin kare dangin daya mishi ba, yace ina ruwanshi tunda ni matar shi ce? Bashi da ikon da zai hana shi yin abinda yaga dama. Ke magana taki ci taki cinyewa fa. Ranar nan kawai ina zaune da dare, sai gashi ya shigo gidan. Yace min an sanya aurenshi watanni biyu masu zuwa, nace mishi to Allah ya sanya alkhairi, yace ameen. Washegari wai sai ya sameni yace shi tafa bashi da wajen da zai saka amarya idan tazo, nace ‘to Abban Mufeedah, ya kake so ayi kenan?’, bai ce komi ba dai ya tafi. Haka muke ta zama dai, hatta yan uwanshi sai da suka fara shigowa suna zagina. Wai ni matsiyaciya ce, ban iya komi ba sai ci. Ita kuma wadda yake neman auren tana ta musu hidima. Abubuwa fa duk suka rikice. Yanzu kawai ranar nan ina zaune, sai gashi yazo da takarda ya miko min, wai ya sake ni saki biyu. Nace ‘me na maka?’, sai ya hau zage-zage da daga jijiyar wuya, wai shi dama can ya gaji da zama dani, yana ta hakuri da nine dama, kuma hakurinshi ya kai makura, in fita in bar mishi gidanshi kawai. Nace to shikenan, shine na tattara kayana na dawo gida abina!”.
Cike da jimami nace “to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Kuma babu wanda ya same shi game da maganar akan haka?”.
Tace “ace mishi me Na’ilah? Last week aka daura mishi aure, har cikin gidannan yayi sallama ya kawowa Malam katin gayyata”.
Na zare idanu, “ikon Allah! Wannan ai cin fuska ne!”.
Tayi dan murmushi cike da takaici, “cin fuska kuma wani iri ne ban gani ba a wajen Mukhtar? Ai sai dai in karas kawai. Kuma yaje na barshi da Allah!”.
Nayi saurin girgiza kai, “a’ah, kada ki ce haka mana. Ko babu komi mahaifin diyar ki ne, kuma akwai sauran igiyar aure a tsakaninku, idan Allah ya nufa sai ki ga kun komawa aurenku!”.
Tace “da wa? Allah ya tsareni wallahi. Kinsan cewa sauran Kayankayan dakina da ba’a dauka ba, ya sayar dasu?”.
Nace “me yake damun wannan mutumin ne haka?”.
Tayi kwafa, “tijara mana! Su Malam zasu yi magana, nace su barshi. Wallahi na yafe mishi duniya da lahira, Tunda dai na samu aka rabu lafiya, to ni na godewa Allah”.
Na janyo ta jikina na rungume cike da nuna lallashi, nace “to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku ku duka”.
Tace “Ameen. Ni yanzu haka so nake in gama iddata, makaranta zan koma in cigaba da karatu na”.
Nace “haka ne, Allah ya sanya albarka to. Allah kuma yasa hakan shine daidai”.
Tace “Ameen. Ina Janan?”.
Daga nan muka canza akalar hirar zuwa ta Janan. Sai ma dana kirata muka sha hira da ita. Ita kanta taji haushin abinda Mukhtar din yayi, ta ma so ta fi ni jin zafin abin. Sai data gama kumfar baki sannan kuma muka hau hira.
A gidan na yini, muna daki muna ta maida bayanai, irin zaman da suka yi da tsohon mijinta, da yadda danginshi suka juya mata baya lokaci daya. Wasu abubuwan ma dai gwanin ban takaici. Tunda kwata-kwata wasu abubuwan kawai sai dai fa yayi su ya kawo wani excuse da bai hau ba ya dora. Kawai abin dai dama kamar yana neman hanyar fita ne, shi yasa.
Da lokacin yin abinci yayi na shiga gida na dafa, na koma muka dora daga inda muka tsaya.
Da yamma na raka Maryam islamiyarsu, na samu malamanta muka yi magana dasu. Korafinsu daya, rashin maida hankali da take yi. A sati bai fi taje makaranta sau biyu ba, idan tayi da yawa sau uku. Na musu alkawarin idan Allah ya yarda za’a mata magana, nan suka ce idan ma ta maida hankali zata iya bin yan ajin nasu, dama as a warning ne yasa aka yi mata hakan, ko zata hankalta. Nan dai na musu godiya tare da biyan kudin watanta da bata biya ba, tace Baba ya bata amma cinyewa nayi. Anan na barta ni kuma na koma gida.
Kwana na shida a gida, komi yana tafiya yadda yakamata. Yawanci a gidan su Kulsum nake yini. Da safe idan na gama yin komi nawa zan shiga can. In taya ta aikin awara da dankali da take yi na saidawa da rana. In muka gama kuma mu hau aikin zobo shima da take yi ana kaiwa shaguna suna sai da mata. Haka dai nake juya rayuwar tawa.
Na shigo gidan kenan da yamma, daidai kofar dakin Aliyu dake kusa da kofar gida naji motsi da hayaniya. Sautin kida yana ta tashi daga dakin nashi. Na girgiza kai, ban san me yake damun yaron ba, haka zai tara yaran unguwa sa’anninshi su yi ta hayaniya a daki. Basa komi sai jin kida da wake-wake. Bana tunanin yaje makaranta ma yau.
Har na wuce ta kofar dakin, sai kuma na koma sakamakom hayaki da naga yana fita daga jikin labule da aka sakaye dakin dashi. Daga farko nayi tunanin ko girki ne yake yi a dakin, tunda wasu lokutan yana shiga cikin gidan ya kwashi garwashi yace zai dafa ruwan shayi.
Sai dai abinda na gani ne yasa na yaye labulen dakin sosai.
Shisha ce a tsakiyar dakin, sun sakata a tsakiya shi da abokanshi su uku suna zuka.