A ZATO NA COMPLETE

Yaya Mudatthir da kanshi yaje ya dauko ni. Ya kalli yadda nayi wuki-wuki saboda gajiya yayi dariya, “Subhanallah!! Illo! (nick name din da yake kira na dashi), you look like a total mess!”.
Nima nayi dariya, “Yaya tafiyar awanni fiye da bakwai a mota ai ba ta wasa bace ba!”.
Ya gyada kai, “kwarai kuwa. Sannu da zuwa. Ya hanya?”.
Nace “Alhamdulillah”. Ya taya ni daukar akwatina ya dora akan mashin dinshi, nima na hau muka tafi.
A gidan Bako ya ajiye ni, ko shiga bai yi ba yace min zai dawo bayan magriba, na mishi godiya. Ya juya ni kuma na shiga gidan wani almajiri ya biyo ni da akwatina.
Inna Fatsu na gaban wuta tana tuka tuwo nayi sallama na shiga cikin gidan. Ta tashi tsaye tare da dago kanta sakamakon jin muryata a kanta. Kafin ta tantance ko ni ce ko ba ni bace ba, na saki jakar hannuna kasa na falla da gudu na fada jikinta. Allah ya taimaka ta dafe bango da sai na kaimu kasa gabadayanmu.
Ta fara kokarin yakice ni tana mitar, “ban san ko sai yaushe bane zaki daina wannan shirmen naki ba Na’ilah. Ina ga dai sai ranar da Allah ya baki sa’a kika buga mu da kasa mu duka kika karya min kugu sannan zaki daina!”.
Nayi dariya tare da daga kaina na kalleta, “Fatsu na, kin sake yin kyau wallahi. Me Malam yake baki kina ci ne?”.
Ta girgiza kai, amma murmushine akan fuskarta, “tuwon dawa ne da miyar. Idan so kike yanzu in bada nikanta”.
Nayi dariya, “Inna kin san wannan ba cima ta bace. Abu zaki bane mai sanyi da mai romo don na kwaso gajiya da yunwa”.
Tace “ki fara shiga kiyi wanka, sai ki zo kici abinci”.
Nace “haka za ayi”. Na fada daki.
Ita ta biyo ni da jakar hannuna dana yasar da akwatina tana mita. Dariya kawai na dinga mata.
Idan ina gabansu ji na nake yi kamar wata karamar yarinya yar shekara goma.
Da nayi wankan sai na dauro alwala kawai. Na shiga dakin Fatsu da aka mamaye da carpet mai laushi. Dakin irin tsarin nan ne na mutanen da, gadon karfe babba da kuma karami na katako, sai wardrobe babba, da kuma tarkace da ba’a raba tsofi dasu. Na zauna na shafa mai tare da lalubo kaya masu karancin nauyi na saka. Ina sakawa sai gata ta shigo dakin da plate da kula.
Na mike kafa akan carpet din tare da amsar plate din, maltina ce mai sanyi har raba yake da ruwan sanyi, kular kuma soyayyar indomie ce a ciki.
Tace “Yayanki yace kada ayi abinci dake, za’a dafo daga gidanshi a kawo miki”.
Nayi murmushi cike da jindadi, “sai ni yar gatar Yaya da Anty Sailu”.
Tayi dariya, “kwarai kuwa, dazu zuwanta biyu nan wai taga ko kin zo”.
Nima nayi dariyar. Sailuba itace wadda Yaya Mudatthir ya aura. Wannan shekarar su ta biyo ne kenan. Auren dangi ne suka yi, diyar Iya Lami kanwar Mama ce. Da yake duk tare muka taso da ita da sauran diyan dangi sa’anninmu, kusan duk abokan juna ne mu.
Na sa fork na fara cin indomie, taji maggi da dan taruhu, dama in dai Inna Fatsu ce bana jinta wajen girki. Ta iya hada abinci kala-kala, tun daga na da har na zamani.
Sai dana kusa yin rabi sannan na daga kai na kalleta, “wai ni ina Malam yayi ne? Nayi zaton ma yana dakin soro ne”.
Tace “ai Malam wajen jana’izah yaje, nasan kuma daga can zai wuce masallaci. Shi da gida sai bayan isha’i”.
Nace “Allah sarki, waye ya rasu?”.
Tace “wani abokinshi Malam Mati idan baki manta shi ba”.
Nace “ina zan manta Malam Mati? Shi da nake kaiwa rubutuna idan nayi a allo ya wanke min kafin in iya?”.
Inna tayi dariya, “Aikuwa shi ne. Rashin lafiya ce yayi wallahi, ya kusa share watanni biyu a aaibiti”.
Nace “Allah ya jikanshi, Allah kuma yasa mutuwar hutu ce a gare shi. In shaa Allah idan na fita gobe kuwa zan je inyi gaisuwa”.
Tace “yakamata dai”.
Ina gama cin abincin aka fara kiran sallah. Na daukesu na fidda waje na koma daki nayi sallah.
Ina gamawa naji wayata tana kara, na tashi a nutse na dauketa daga inda na ajiyeta, lokacin kiran har ya katse. Na duba naga Maryam ce. Murmushi nayi kafin na sake kiranta. Yana fara ringing ta dauka, “Yaya Na’ilah tun dazu nake kiranki baki dauka ba, hankalina har ya fara tashi wallahi!”.
Nayi dariya, “ban jima da isowar bane, ina zuwa kuma wanka nayi. Ina ga lokacin kika kira. Na sauka lafiya, ina dakin Fatsu na ma idan abinda kika kira ki tambaya kenan”.
Tace “shine dama. Ya hanya? Kin same su lafiya dai?”.
Nace “lafiya lau kowa. Ya gidan?”.
Mun danyi hira da ita ta fada min yadda su Muneerah da Auwal suka dinga cigiyata a gidan, ina ta dariya. Daga karshe dai muka yi sallama da ita akan cewa zan kira washegari ta hada ni da yaran. Bayan mun kashe wayar Baba na turawa text na sanar dashi na sauka lafiya duk da cewa nasan Yaya zai fada mishi.
Kan abin sallah na koma na zauna gefen Fatsu da take lazumi nima na fara nawa har aka kira sallah.
Sai bayan sallar isha’i sannan Malam ya shigo gidan. Na dauki kwanukan da aka zuba mishi abinci na tafi dakinshi. A bakin kofar dakin nayi sallama, daga can ciki na jiyo ya amsa cikin muryarshi mai cike da kamala da haiba.
Na yaye labulen dakin na shiga, yana ganina ya hau sakin murmushi “Masha Allah, amaryar tawa ta karaso kenan?”.
Nayi yar dariya tare da zama a gefen shi, “ni ai nayi fushi, tunda kaki zuwa tarya na!”.
Yayi yar dariya, “to, ki ce wannan karon da yan rigimun kika zo kenan?”.
Inna data shigo dakin hannunta dauke da kofin ruwa tace “kamar kuwa ka sani!”.
Na zauna a gefenshi tare da ajiye kwanukan a gabanshi. A nutse na gaida shi ya amsa tare da tambayata mutanen gida, na amsa tare da mishi ta’aziya.
Inna ta gama zuba mishi tuwon. Ya wanke hannunshi tare da yin bismillah ya fara cin tuwon. Ya kalleni, “yau ba za’a taya ni cin abincin bane?”.
Inna tace “yau dai kai kadai zaka ci abincinka. Girkin matar Yayanta take jira”.
Tana rufe baki sai ga sallamar Yayan a tsakar gida. Na tashi da sauri na fita tsakar gidan. Wani dan ihu nayi na dafe Sailuba dake gefen Yayan. Ya girgiza kai kawai ya shige dakin Malam ko tunanin yi mana magana bai yi ba, don yasan in muka hadu sai a hankali.
Sai da muka gama murnar ganin juna sannan muka shiga ta gaida su Malam.
Na dauki kwandon da suka shigo dashi na ja ta muka koma dakin Inna. Da yake da wuta kar a garin, na kara mana gudun fanka.
Farfesun busasshen kifi ne ta kawo min da chips din doya. Na zuba iya wanda zai ishe mu na ciccibi sauran na kaiwa su Inna.
Dakin na koma muka dasa dandalin hira ni da ita, bamu san dare yayi ba sai da Yaya ya leko yace mata ta tashi su tafi. Na raka su har kofar gidan muka yi sallama dasu.
Dakin Fatsu na koma nayi shirin kwanciya barci na. Ina zaune Fatsu itama tayi nata shirin ta tafi dakin Malam. Wutar dakin na kashe tare da sakaya dakin, na kara ware iskan fanka na fada kan karamin gado na kwanta.
Sai dana kira Janan muka gaisa na fada mata ina Gashua sannan na dannawa Umar kira.
Yana dauka ya tare ni da, “haba Sweety na, ina kika shiga ne tun safe nake nemanki?”.
Nayi murmushi, “hello to you too, and yes, lafiya lau na wuni!”.
Ina jin sautim dariyar daya saki, “Lols.. Da gaske nake fa. Har na fara shirya kayan tahowa Kt gobe idan baki amsa kira na dama”.
Nayi murmushi, “lallai ma, yanzu kawai sai ka taho Katsina?”.
Yace “ai ba kawai bane, ina lafiya bugun zuciyata bata daga kira na?”.
Nace “ba kin daga wayarka nayi ba, ina tunanin matsalar netwok ne. Kasan ina Gashua fa!”.
Yace “hope komi lafiya?”.