A ZATO NA COMPLETE

Bayan fitarshi Fatsu ta kalleni cikin yin kasa da idanu, murya cike da gargadi tace “kinsan dai Yayanki ba zai ji dadin wannan magana ba ko?”.
Na kada idanu, “gaisawa ce fa kawai ba wani abu ba. Beside, babu wata magana a tsakanina da Magaji sai zumunci kawai da girmama juna”.
Tace “ai shikenan!”. Hijabina na saka na fita.
Magaji kusan zan iya cewa abokin Yaya ne, duk da dai ba aboki bane na kut-da-kut, they were more like classmates. Shekaru kusan uku da suka wuce ya nuna yana da sha’awar aurena, tun ma kafin mu hadu da Umar. Na sanar dashi ban shirya yin wani relationship ba a lokacin, yace ya yarda zai jira ni. Ni dai na fito fili na sanar dashi cewa bani da ra’ayin yin wata alaka data wuce ta mutunci dashi, yace babu laifi, ya amince. Amma lokaci zuwa lokaci ya kan yi min tuni, ko kuma nuna alamun har yanzu fa yana so na, ni kam sai dai in banzatar da maganar kawai.
Yanzu ma gaisawa kawai muka yi, ya sanar dani dama wucewa yazo yi, da yake jiya ya ga wucewar mu ta kofar shagon dinkinshi, shine yace bari yazo ya min barka da zuwa.
Muna tsaye anan Yaya yazo wucewa, na dan duka ina gaida shi, hararar daya daka min kadai tasa naji diyan cikina suna kadawa. Ya ba Magaji hannu suka gaisa yana ta wani basarwa, ya shige cikin gida.
Yana bada baya Magaji ya dube ni yana dan yin murmushi, “to ranki ya dade, bari in koma shago, sai wani lokaci kuma”.
Na gyada kai, “to Magaji, na gode”. Na shige ciki, shi kuma ya wuce.
Ina yin sallama a gidan, Yaya ya taro ni da fada, “wato Na’ilah kunnen kashi ne dake ko? Sau nawa ina fada miki na hana ki tsayawa da Magajin wannan?”.
Nace “ni fa Yaya babu abinda yake tsakaninmu dashi sai mutunci kawai, zuwa ne yayi mu gaisa fa ba wani abu ba!”.
Murya cikin fada yace “koma menene, na fada miki na hana. Kuma wannan shine gargadi na karshe da zan miki akan wannan maganar, idan na kara ganinki dashi a tsaye, kinsan hakan ba zai miki dadi ba. Kina ji na?!”. Ya shura kafa ya bar gidan tun kafin in ce mishi wani abu.
Na turo baki ina satar kallon Fatsu da take sakar ta kamar bata san abinda yake faruwa ba. Na kara turo baki na wuce daki ina dira kafa.
Washegari a Damaturu na wuni gidan Inna Talatu. Da yamma Hafiz, babban danta namiji ya biyo ni muka dawo gida. Sana’o’in shi yake yi a garin Gashua da sauran kananun garuruwa da kauyuka dake makwaftaka da Gashua.
*
Kwanaki bakwai nayi a Gashua ina shan hutu na. Da za’a tambayeni menene ainihin ma’anar hutu? To ni zan ce hutu a gaban Fatsu da Yaya ne hutu.
Nan kadai ne zan yi rayuwata yadda naga dama ba tare da an juya ni ba. Babu abinda yake burgeni da zama a Gashua sai gani na tare, kuma lullube da dangi, duk inda na juya sune. Babu ranar banza da wani nawa ba zai yi sallama ya shigo gidan Bako ba, ko kuma ni ban je naga wani nawa ba. Wannan kadai, ni abin dadi ne a gareni. Ina son dangina, musamman fannin Mama.
Dangin Babana da yake suna da rufin asirinsu daidai misali, kuma da yake babu wasu na kusa, daga diyan kawunnai sai kannen kakanni. Idan kaje gidajensu sai su yi ta wani daga hanci suna shan mur, ko suna zaton rokonsu kaje yi ne? Shi yasa wasu lokutan idan naje Gashua bai fi in leka su sau daya ba, sai dai ko idan biki ake yi ko wata hidimar.
Yau kauyen Alkali muka je ni da Sailuba. akwai wata kanwar Babana, from another father da take aure acan, sunanta Fatima amma Juma ake ce mata. Duk cikin dangin Baba ita kadai ce mai kirki da kuma zumunci. Yawanci idan harka a gidanmu ta tashi, musamman idan su Anty suka haihu, ita kam tana zuwa. Haka idan nazo Gashua, watarana har takanas take yi tazo nan mu gaisa. Shi yasa nima bana zuwa ba tare dana leka ta ba.
Kayan dana kai wa diyanta, yawancinsu wadanda suka min kadan ne na kai musu, sai mazan dana shiga kasuwa na samo musu, tayi ta godiya yadda kasan harshenta zai fadi kasa.
Yini guda muka musu, musamman da yake yau kasuwar garin take ci, muka shiga mu da Hanne babbar diyarta da take kai tallar nono. Rana ta dan fara alamun faduwa lokacin da muka yi sallama dasu zamu tafi, suka ciko mu da tsarabar kayan kauye cike taf da buhu.
Kasancewar Fatsu ta min fadan jimawa a unguwa yasa ko gidan Sailu ban shiga ba na wuce gida.
Bako yana kofar gida yana alwalar sallar magriba, na durkusa na gaida shi, kai kawai ya gyada min, na mike na shige gida. A gidan ma itama Fatsu alwalar na tarar tana yi, na shiga daki na ajiye kayan hannuna na fito nima na daura alwalar.
Tun wajen karfe tara na kwanta saboda gajiya da nayi saboda mun sha yawo a garin Alkali yau. Har barci ya fara dauka ta na jiyo muryar Yaya a kofar dakin Fatsu suna magana shi da ita, Fatsu take cewa “aikuwa ta dade da kwanciya, idan ba sa’a ba ta riga tayi barci zuwa yanzu”.
Yace “to gashi ki ajiye mata, nima a hanya na sayo shi, kin santa da son kifi soyayye”.
Ai jin an ambaci kifi sai nayi wukit, na hantsalo daga kan gado. Kawai sai gani na suka yi a gabansu. Fatsu ta dafe baki, “kai wannan ‘ya, Allah ya kyauta miki ke kam. Nayi zaton kinyi barci?”.
Na ja ledar dana gani a gabanta ina murmushi, nace “na dai fara, amma bai yi nauyi ba. Yaya ya hanya?”.
Yayi dariya, “lafiya lau Na’ilah.. Bari in karasa gida ni”. Muka mishi sai da safe ni da Fatsu, ya tafi ni kuma na tashi na shiga daki na dauko yaji na koma na zauna. Kifin na bare, ina cire mana kayar ina dangwala shi da yaji ina ci, Fatsu kam haka nan taci shi. Ganin Malam bai shigo ba yasa na kai mishi nashi daki.
Ruwa na kora mai sanyi na koma daki na kwanta.
Wayata ta fara haske wanda yake nuna min ajiyayyen sako da ban daga ba, nayi unlocking wayar ina dubawa. Umar ne da Janan. Shi yana tambayar yadda na wuni, ita kuma tana tambayar ko naji komawa makaranta nan da kwanaki hudu? Na maida mata amsar na sani, shi ma Umar din na maida mishi reply din.
Na koma kan gadon na kwanta, zuciyata cike da tunanin Umar din. Kwana biyu bamu yi waya dashi ba, ko musayar sako, to da yake ma sau tari haka muke kasancewa yasa ban cika damuwa ba.
A hankali tunanin nawa ya gangaro kaina, jibi nake so in koma gida saboda in fara shirye-shiryen komawa makaranta. Kasancewar shekarar karshe zamu shiga, nasan projects da sauransu ba zasu bari in kara samun hutu mai tsayi kamar wannan ba.
Tuni kewar su Fatsu ta fara lullubeni. Nayi fatan ace na hado duk wasu kaya da zan bukata daga gida, da bari zanyi kawai in wuce daga nan tunda dama na saba yin hakan. Amma yanzu babu damar yin hakan, su ma nasan kila tsakanina dasu sai dai ko in Yaya yaje Kano ko Kaduna, ya biya ta wajena. Amma na kudirta idan muka samu hutun sallah wannan karon anan zan yi shi. Da wadannan tunanikan barci ya daukeni.
Washegari na shiga yin sallama da mutanen garin Gashua, wasu dangin ma sai a ranar na leka su kasancewar Mama na Allah ya albarkace su da dangi Masha Allah.
Ranar da zan tafi kam ban ma fara shirin tafiya ba sai dana karya. Sai wajen karfe tara sannan na mike, tuni kayana sun nabba’a a bayan mashin din Yaya. Bayan akwatina, akwai jakar Ghana madaidaiciya shake da tarkacen tsaraba da aka hada min wadanda zan koma makaranta dasu, dangin busasshen kifi, cukwi. Akwai wani abu da Iya Lami take yi wai shi ‘mitimis’, da nikakkiyar danyar gyada ake yi da sugar, sai a yanka in cubes kamar dai tuwon madara. Shima sai data cika min katuwar leda dashi. Haka dai abin yake kasancewa a duk lokacin da naje Gashua.
Kaunar da mutanen nan suke nuna min is so overwhelming da take saka ni zubar da hawaye a lokuta da dama. Ko yanzu da Yaya ya raka ni tasha, ya biya min kudin mota tare da damka min wasu a hannu in case zan bukace su, ga kuma hannuna rike da plastic rubber da Sailu ta soya chips din dankali da sauce din kwai ta bashi ya kawo min, hawayen nake sharewa, ya dafa kaina yana murmushi fondly, cike kuma da tsokana, yace “daina hawayen mana. Bansan wanda ya shagwaba ki da yawa ba Illo, har sai yaushe ne zaki girma ke kam?”.