A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Nayi murmushi ina share hawayen, yana tsaye na shige mota, da yake karama ce ba bus ba, tuni ta cika. Yaya yana tsaye yana daga min hannu muka fita daga cikin tasha din. A mota na rubuta text na turawa Janan da Umar don su san da tahowata, na maida kaina jikin kujera na kwantar.

*

Wasu masallatai har sun gama sallame sallar isha’i lokacin dana yi sallama tsakar gidanmu. Motar Baba tana fake a nan bayan dakin su Aliyu inda ya saba ajiye ta, hakan ya sanar dani yana gida. Babu kowa a tsakar gidan, don haka na ja akwatina na shiga daki.

Maryam dake kan abin sallah, tayi tsalle daga jin muryata ta dafe jikina tana ihun oyoyo, ina tunanin jin ihunta ne ya janyo hankalin su Auwal, sai gasu sun fado dakin da gudu su ma suna nasu ihun murnar. Nayi dariya tare da zama daram a kasa sakamakon jin suna neman kayar dani a kasa. Sai da suka gama ihun murnar, na bude jakata na ciro cakuletin eclairs na damkawa kowannensu a hannu, sannan duk suka watse.

Na tashi na shiga bandaki na dauro alwala. Kasancewar an fara yin ruwa, iska mai sanyi yake kadawa sakamakon ruwa da aka yi da rana.
Sai da nayi sallah sannan na dauki wayata na sanar da su Yaya da Fatsu karasowa ta gida lafiya.
Na fita na leka dakin su Anty duk na musu sannu da gida. Nasan cewa in ba lekawa nayi ba, babu wadda zata damu da ko furta min kalmar sannu da hanya ne. Zamu iya haduwa dasu a tsakar gida ma gobe su nuna kamar dama can ina gidan.

Ina gamawa dasu ban bata lokaci ba na nemi makwancin barci, ina yada kai akan katifa kuwa, barci yayi awon gaba dani.

         *☆⋆06⋆☆*

“Ni dai yanzu haka maganar da ake yi babu kudi a hannuna Na’ilah, duka-duka shekaranjiya na biyawa yara kudin school fees su ma, ga kuma sauran hidimar gida dake kaina, ta ina kike zaton zan lalubo naira kusan dubu arba’in cikin kwana biyu?”.

Na kifta idanuna kamar wanda abu ya fada cikin idanun, tunda ya fara maganar kallonshi kawai nake yi babu ko kiftawa saboda jin maganganun da suka fita daga bakinshi, sai dana hadiyi yawu na jika makoshina da naji ya bushe, nace “amma Baba tun da nazo dama na fada maka, kuma yanzu idan ban biya kudin akan lokaci ba, ba zan taba samun accomodation ba!”.

Ya kalleni a kaikaice, “to yanzu ya kike so inyi ne? Tunda nace miki bani da kudi a hannuna, ta ina kike tunanin zan je in lalubo su?”.
Ramata dake gefenshi ta kalleshi tana wata kwarkwasa, “kasan akwai kudin anko na dake kanka ko? Kuma bikin satin sama ne”.
Ban san lokacin dana jefa mata harara ba, aka yi sa’a ta kalloni muka hada ido, da sauri ta janye kanta daga kallona, nayi kwafa, can kasan zuciyata ina raya ‘kin kyautawa kanki!’.

Baba yace “to bari mu jira zuwa ranar laraba mu ga yadda hali zai yi”. Daga wannan magana sai ya dauke kanshi gabadaya daga inda nake, clearly dismissing me, na mike gwiwa a salube na fita daga dakin.

Gefen katifa na laluba na zauna, Allah ya so ni Maryam bata gidan, wai ta tafi suna gidan kawarta, shigar banzar dai dana mata magana akai, ita tayi. Binta da kallo kawai nayi lokacin da naga ta fito sanye da riga da siket na atamfa, an musu wani irin dinki na cin mutunci. Siket din ya matseta tsam, kamar in tayi nishi mai karfi zai yage, rigar ma haka, ga wani dan iskan ‘show me your back’ shima da aka yi, tayi daurin dankwali mai nadin doughnut a goshi, ga gyalen nan kamar matacin koko saboda shara-shara da yayi ta dora a wuya. Ban ma yi tunanin yi mata magana ba, har yanzu fushin abinda Aliyu yayi min kamar sabo yake a cikin raina, ban shirya shiga wani bacin rai makamancin haka ba so soon kuma. Koma dai menene tayi, Allah ya gani, nayi iyaka bakin kokari na. Magana akan shigar banza irin haka ba tun yau nake yiwa Maryam ita ba, tun kafin ta fara kirgan dangi muke haka. Sai kuma ta nuna ta fahimta, taji maganata, daga baya sai uwar ta kara zuga ta dai, sai ta koma cikin ruwa tsamo-tsamo.
Allah yasa for now dai, ita kadai ce budurwa mai tasawa a gidan, sauran duk suna kan hanya, ina kuma fata kafin su gama yin hankalin kansu, su dauki irin dabi’arta, zata daina.

Rashin Maryam a dakin shi ya bani damar jingina da bango, na tsunduma cikin tunani mai zurfi. Yakamata ace na saba da abinda Baba yake yi min, sai dai, kamar yadda ba’a taba sabo da wahala, haka ma ba’a sabo da bacin rai. Musamman idan wanda yake haddasa maka hakan ya kasance majibanci, kuma majingini a gareka, wanda kake ganin zaka iya rab’a a duk lokacin da komi ya yaye maka baya, kuma ya tallafa maka. Sai dai no, ko kadan ba hakan take ba.
Lokacin da zamu tafi registration dinmu na farko, haka Baba yayi min wannan delaying din. Sanadiyar haka na rasa accomodation a cikin hostel, wata kawarmu da muka yi sbrs da ita, ita tayi squatting dina. Believe me when I say, it wasn’t fun at all. Ban taba raina kaina ba sai a wannan lokacin, ban taba jin dadin rayuwar gidanmu ba, in fact, ni zan iya dukan kirji in ce rayuwar makaranta ta fiye min rayuwar gidanmu, amma a wancan lokacin sai dana fara rethinking wannan tunani. Sai dana gwammace rayuwar gidanmu sau dari akan wannan rayuwar. At least a can, ina da wajen da zan kira dakina, sannan duk lokacin da dare yayi, a gida nasan cewa ina da wajen da zan kwantar da hakarkarina, amma ban da nan.
Haka taci gaba da faruwa, for once, ban taba biyan makaranta akan kari ba, kullum, kuma kodayaushe, sai na kara kwanaki ko satika, duk da cewa kowani lokaci nakan fadawa Baba da wuri yadda zai tanadi kudin, but no, kodayaushe akwai uzirin da zai ratso ya shiga ta cikin kudinnan. Ban sani ba, daga gareshi ne ko daga matanshi, ko kuwa in ce matar shi? Allah ne masani.

Yaya Mudatthir, Allah ya albarkaci rayuwar shi. Da ba don shi ba kam, ban san yadda karatuna zai kasance ba. Idan Allah ya taimaka yana da kudi, shi yake daukar jigilar registration dina, daga baya in Baba ya turo, in tura mishi, duk da a yawancin lokuta ya kan dawo min dasu ko kuma yace in barsu, sai dai in maida mishi rabi ko ya dawo min da rabi.
Ko last year, Allah ne yasa Yaya Jameel, yayan Janan, da yake lecturer ne a cikin makarantar, ya bata daki, Yaya ya hanata zama, ni kuma ta bar min shi.

Da tunanika iri-iri na kwanta. Sau tari sai inji gabadaya karatun ya fita a cikin raina, inji kawai gwanda in hakura dashi, in huta da bakinciki da takaicin da nake kwasa daga wajen Baba. Sai dai wasu lokutan, sai in ga daurewar tafi. Musamman idan naga cewa shine kadai gatana a yanzu. Karatun shi zai tallafa min, in tsaya akan kafafuna ba tare dana jingina da wani ba. Idan nayi hakuri, na dan lokaci ne. Komi wucewa zai yi, ya zama tarihi, kamar bai taba faruwa ba. At least, abinda nake fata kenan.

                                   *

Washegari da dare, mun zagaya nan bayan gidanmu ni da Kulsum dubo wata Hassana wadda muka yi aji daya da ita a makarantar Islamiya. A hanyarmu ta dawowa, muna tattaunawa game da matsalolin da ita Kulsum din take fuskanta daga tsohon mijinta.
Ya fara mata zarya akan cewa yana so ya amshi Muneerah daga wajenta, ita kuma tace gaskiya bata son bashi ita.

Ni kaina shawarar dana bata kenan. Nace idan da yadda zasu yi akan haka, gaskiya suyi, ya bar mata diyarta ta tarbiyantar da ita a gabanta. Tunda ma ba maganar aurenta bace ta taso, ko iddah bata gama ba, balle yace ta wannan dalili yake son karbar ta.
Wahalhalun dana sha a hannun kishiyar uwa, shi nake guje mata. Duk da cewa ni rashin mahaifiya ne ya jawo min, ita tata mahaifiyar tana raye. Kuma tana ji tana gani, haka za’a fi karfinta akan diyarta. Bana fata ko makiyina ya dandani kwatankwacin abinda na dandana. Abinda na dinga tunani a cikin raina kenan, ban furta mata hakan ba amma.
Koda kasancewarta kawata, ko ma ince aminiya, tarihin gidanmu, da irin zaman da nayi da mutanen gidan, dama wanda nake yi, ba duka ta sani ba. Ta dai san wanda kunnenta ya jiye mata, kuma idanunta suka gane mata, shikenan. A tunanina, tado abinda ya wuce, yake kuma sosa ran mutum, duk ba solution bane. Hakan babu abinda zai haifar sai ma wani karin bacin rai, hakan zai sa ka kullaci mutane a cikin ranka, kila dan mutuncinta da kake gani nasu ya zube. Babu abinda zai sa, kuma babu abinda zai hana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button