A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Da alama maimakon maganar ta sanyayar mata da rai, sai ma ta kara tunzurata, tace “to akansu zaki zauna ne da zasu yi korafi? Idan kinzo din duka kwana nawa ne zaki yi ki wuce hostel abinki? Ba lallai kullum sai kun hadu dasu ba!”.
Nace “duk da haka Janan, gaskiya kiyi hakuri kawai. Zan kara turzawa dai in gani, tunda jarabawa ce kawai, zanyi karatuna a gida, sauran lectures idan na dawo I’ll catch up with you”.
Dan siririn tsaki taja, “ai sai kije kiyi tayi, sarkin kafiyar kai. Ba’a tana nuna miki gabas ki bi, sai dai kiyi yamma!”. Ta katse wayar tana gunguni. Murmushi na saki a hankali ina girhiza kai, Janan kenan!.

Sai dai ba’a yi mintuna talatin ba, sai gashi ta sake kirana. Na daga da sauri, sai dai tun kafin inyi magana ta riga ni, “to Yaya dai yace ki hado kan kayanki ki taho gobe!”. Kafin ince komi ta sake kashe wayar, na bi wayar da kallo baki a dage.

Dawowar Maryam yasa na mika mata wayar, na cigaba da tukin tuwona cike da sake-sake. Wani bangaren na zuciyata yana fada min inje, wani kuma yana ce min a’ah. Na farko ni dai ban taba zuwa gidansu na kwana ba, na biyu ga yar tsamar da muke yi da kanwar matarshi nasan da kyar ne idan watarana, duk kawar da kaina, na biye mata mun raba hali ba, sannan ni fa bana son zuwa gidan mutane haka kawai in zaune musu. Ni duk wani abu da zai sa in zama uncomfortable bana son shi ko kadan.

Na gama tuwon na gyara kicin din tsaf, wanke-wanke na barshi sai gobe don dare ya riga yayi. Kulolin dana zubawa Baba nashi, na cicciba na tafi zan kai dakin Alawiyya da take yin girki. A gefen gado na sameta a zaune dafe da gefen cikinta, na ajiye kayan a kasa, na kalleta cikin kulawa nace “Anty baki jin dadi ne?”.

Ta dago ta kalleni, fuskarta na yamutsewa cikin nuna jin ciwo, tace “babu komi, cikina ne yake dan juyawa, amma zan sha magani”.
Sai dai jikina ya bani ba wannan bane, zata iya yiwuwa ciwon cikin ne, amma ba na shan magani bane. Jikina yana bani wani abu ne daban. Kai kawai na gyada mata, na mata fatan Allah ya bata lafiya na fita daga dakin.

Ina yarinya kimanin shekaru takwas, na fara ganin haka. It was weird. Wani lokacin kalar idanun mutum ce zata canza, wani lokacin hayakine zan ga yana fita daga waje ko jikin mutum, wani lokaci kuma jikina ne kawai zan ji ya bani. Wanda aka yiwa sammu, ko wanda yayi sammun, da wajen da aka binne ko aka kona abinda aka yin, cikin ikon Allah duk ina iya gani.
Mama Allah jikan rai, farkon abin tace iska ne, Malam Bako yace ba lallai sai shafar aljanu bane yake kawo hakan, Iko ne kawai da wata hikima ta Ubangiji ba wani abu ba.
Koma dai menene, ina godewa Allah. Zaman Mama da Ramata na sha ganin ire-iren abubuwan nan. Wasu lokutan a bandaki, daidai wajen tsuguno, sai dai in ciro layoyi, wasu lokutan kofar dakin Mama, watarana na Baba, sai dai in daukesu kawai in kaiwa Malam. Ko Mama watarana bana fadawa balle ta sani. A yanzu haka, bayan su Malam da Yaya, babu wanda yasan da hakan.

Ina shirin kwanciya, Janan ta sake kirana, a sanyaye na daga. Tace “har kin gama shirin ko?”.
Ni sai ma ta bani dariya, nace “wani irin shiri kuma kike magana a kai?”.
Tace “dawowa mana”.
Sai dana dan yi shiru kafin na fara magana, “look Janan….”
Tayi saurin katseni, “a ganina ko yankar namanki za’a dinga yi, hakan ba zai hana ki k’i zuwa ki zauna dani ba. Haba Na’ilah, ba fa cewa aka yi zaman har abada ba zaki yi, duka satika nawa ne, zasu kai biyu? Ki zo mu zauna muyi shirin exams dinmu, mu fara fuskantar projects da suke tunkaro mu. Kin san idan kika zauna a gida babu abinda zaki iya yi, na riga na yiwa Yaya magana, ya kuma ce babu matsala zaki iya zama, to me kike jira kuma? Matar Yaya da kannenta duk ba matsala bace, ba fa a gidan zaki dinga wuni ba!”.

Na kada kai gefe guda, ta wani bangaren haka ne, it’s for my own good. Don haka na daga baki nace “to zan sanar da Baba, amma sai ranar Lahdi zan taho”.
Ihun murnar data saki shi ya sake bani dariya, na girgiza kaina kawai. Tace “ko ke fa? Sai ki fara shirin tahowa”.
Nace “in Allah ya yarda”, muka yi sallama da ita, na kashe wayar.

Koda na fadawa Baba, haka yace “Allah ya kaimu kawai”. Babu tambayar yadda mutanen gidan suke, ko yadda ita yarinyar take, kawai to yace. Na koma daki na fara hada kan kayana. Wanki na fara yi.

Rana ta fara yi lokacin da naji wani irin gurnani mai kama da kuka yana fitowa daga dakin Anty Alawiyya. Da sauri na saki kayan da nake wankewa na fada dakin, kwance rub da ciki a tsakiyar dakin, itace dafe da cikinta tana ihun kuka. Na tallabota jikina ina tambayar lafiya? Amma ta kasa magana. Yadda take yi har numfashinta yana alamun daukewa, yasa naji wani irin tausayinta ya lullubeni. Na tashi na dauki kofi na debo ruwa, nazo na dinga mata tofi a ciki. Ayoyin tsari da kariya na karanto na tofe mata a ciki, na tallabo kanta na dura mata ruwan, wani yana zubewa a kasa haka nan na dura mata, sauran ruwan da tayi kuma na shafe mata cikinta dashi.
Mintunanmu kusan arba’in a haka, sannan ciwon ya fara lafawa. Ta fara zufa kamar wadda ake kwarawa ruwa. Na tashi na kara mata iskan fanka. Data dan dawo cikin hankalinta na taimaka mata ta koma kan gado ta kwanta, ni kuma na fita. Duk wannan abin da ake yi, Ramata tana tsakar gida a zaune tana jin rediyo abinta. Nayi kwafa kawai lokacin da muka hada ido da ita.

Duhu yana fara yi, na salube jiki na fita daga gidan. Inda naga Lubah jiya naje na duka ina haskawa da fitila har na hangi inda nake nema, hannu kawai nasa ina tona wajen kasancewar kasa ce a wajen. Hannuna ya fara cin karo da wasu irin duwatsu da ban taba gani ba, wasu irin kala su ba bakake ba, kuma ba jajaye ba. Sai dana ciro kusan guda biyar, sai kuma naga wata tsohuwar wuka, gashin dabba kamar na Tunkiya dankare da wukar gaba da baya. Nayi bismillah na daukesu na nade su gabadaya na maida kasar wajen na rufe kamar babu abinda ya faru, na shige gidansu Inna.

A gaban Inna na zubesu ina mata bayani, ta hau tafa hannuwa tana salati. Tace “ai wannan sai dai a kona, kai Allah ya kiyashe mu da rashin tsoron Allah irin na mutane. Allah kadai yasan mugun abin da yake kunshe da wannan abu!”.
Nace “duwatsun fa? Ya za muyi dasu? Tunda ba lallai su kone ba?”.
Tace “to sai dai a nunawa Malam ya gani, sai muji abinda zai ce!”. Anan take muka kona wutar, wata irin kalar wuta data dinga fita daga jiki, ga wani irin wari kamar na bunsuru da take fitarwa, haka dai muna tsaye suka gama konewa kurmus. Wukar Inna ta dauka ta hada da duwatsun nan. Sai dana yi sallah sannan na koma cikin gida.

A haka dai na lallaba zuwa ranar Lahdi. Karfe goma na safe ina cikin tasha, bayan nayi sallama da mutanen gida.

  *☆⋆07⋆☆*

Muna shigowa Zaria, kiran Umar ya shigo cikin wayata kamar ya sani. Kamar ma babu network a inda muke, saboda bana jin shi ta bangaren da yake, na gaya mishi bana jin shi amma idan na karasa gida zan kira shi, na kashe wayar.

Muna shiga tasha mota ta samu waje tayi parking. Na biyo jerin wadanda suke fitowa, na dauki akwatina da jakata. Fita nayi daga tashar ina wurga idanuna ta tsallaken titin domin hango abin hawan da zan kira. Kamar wanda yake jira, ina fita, Umar yana tsayawa a gabana. Yayi murmushi lokacin da yake fitowa daga motarshi, nima na maida mishi martanin murmushin. Ya tsaya a gabana yana kallona, “welcome sweetie!”.
Na saki dariya a hankali ina kallonshi cikin girgiza kai, “is this suppose to be a surprise welcome?”.
Yayi murmushi, yace “ko kadan, na kira ki in fada miki na fito daukar ki sai baki ji na… Maza ki shigo mu wuce kada ki zube min anan saboda gajiya!”. Ya karasa fadar haka yana bude min kofar gidan gaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button