A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Janan ta dubeni fuskarta cike da damuwa, “don Allah kiyi hakuri da abinda tace!”.
Na daga kafada cikin nuna alamun rashin damuwa, duk da cewa kawai don kada ta damu ne na fadi hakan, amma fa maganar kwadayin nan ta taba raina sosai, nace “menene abin jin haushi a maganganunta? Babu komi wallahi. Bari inyi sallah”.
Tace “to”, a lokaci daya kuma tana fita daga dakin. Ni kuma na fada bandakinta.

Ina gama sallah, ta hau turo min plates da bowls na abubuwa. Na kallesu ina kwashewa da dariya, nace “baiwar Allah ina kike so in kai wadannan abubuwan? Ba dai cikina ba ko?”.
Itama tayi dariyar, “na san ki da rashin son cin abinci idan zaki yi tafiya, na tabbata rabonki da abinci tun karin safe”.
Nayi shiru ban amsa ba saboda haka ne, shima karin safen da nayi shayi ne kawai, babu abinda na hada dashi. Daga shi sai maltina din wajen Umar. Hakan ya tuna min da ledar daya hado ni da ita.

Na tashi na nade abin sallar, na koma gefenta na zauna bayan na dauko ledar. Lemuka ne kala-kala was ciki, wasu juices wasu kuma fruit juices sai su tarkacen doughnuts da cupcakes. Tare muka ci abincin da ita muka gama, bayan mun gama ta fita da kwanukan abincin, yayin da na ciro wayata daga cikin jaka na hau kiran yan gida ina sanar dasu na sauka lafiya.

Wajen karfe takwas saura bayan mun gama yin sallah, Umar ya kira ni ya sanar dani yana kofar gida. Na dauki gyalena dana rataye a jikin hanger ina kokarin yafawa, ko hoda ban kara ba balle janbaki. Ni kwata-kwata bana ganin amfanin yin wannan kwalliyar ta dare idan za’a fita hira, koda yake dama ta yaya za ayi in gani tunda dama can kwalliyar ba damuna tayi ba?.
Janan dake kwance ruf-da-ciki akan katifarta tana chatting ta kalleni lokacin da nake shirin fita, tace “kada dai ki wuce karfe tara da rabi, idan kuma ya shigo daga ciki, ku koma daga waje duk da nasan cewa ba lallai Ahmad ya bude mishi gate ba, sai dai idan baya nan”.

Nayi yar dariya ina kallonta, “kada dai kice min kuna da curfew a gidannan?!”.
Tace “Yaya ne yasa wallahi. Samarin su Salama suke shiga da fita babu kakkautawa a gidannan, ko ina kuma shigo dasu suke yi har cikin falon nan, shine ya kafa wannan doka”.
Na gyada kai, “yayi kokari gaskiya, da haka ake yi a wasu wajajen ai da an samu zaman lafiya kuwa”. Tayi yar dariya, “kin ci sa’a ma Yayan baya nan, da sai kin amsa tambayoyi daga wajenshi kamar kina rubuta jarabawar jamb kafin ki fita yanzu”.
Na kama baki cike da mamaki, gefe daya kuma ina jinjina kokarin Yayan, a ganina hakan da yayi hanya ce mafi sauki ta sanin halin da kannenshi da samarinsu suke ciki. Na dai mata sallama na fita.

A kofar gate muka yi clashing da Haleemo ita kuma zata shigo, ta ja da baya tana daga waje alamun ta bani waje in fara fita, na danyi murmushi appreciatingly na raba ta gefenta na fita. Ta kalli gefen gidan inda Umar yayi parking din motarshi, tace “saurayinki ne ya dawo?”.
Mamakin tambayar ta kama ni, amma sai na fuske nayi yar dariya kawai ina gyada mata kai, tace “kinyi sa’a abinki ke kam!”. Ta shige gida, na bita da kallo baki a bude slightly, ko meye hadinta da zancen soyayyata, sa’a ko rashinta? Na daga kafada tare da tsallakawa daya gefen.

Da kanshi ya bude min murfin motar, na shiga ciki bakina dauke da sallama. Barin murfin motar nayi a bude, ban maida shi na rufe ba. Ya amsa min sallamar, scowling, na kula baya son hakan ko kadan, ya sha fadin hakan ma ba sau daya ba sau biyu ba. Kunnen uwar shegu kawai nake yi dashi.
Mun fara hira dashi game da makarantarmu da wajen aikinshi. Ya fada min anyi posting dinshi zuwa Kaduna, satin sama zai shirya ya tafi. Na mishi addu’ar Allah ya taimaka. Daga nan hirar ta koma ta masoya, ya fara amayo kalmomin soyayya. Jinsu kawai nake yi suna shiga suna fita cikin kunnena. Ban sani ba, ko akwai ranar da zanji wani yace yana so na, in yarda da hakan? Inji zuciyata ta mamaye da haske da farinciki sanadiyar jin haka? Nayi nisa cikin tunanina, totally zoned out. Wani abu daya zame min jiki da zarar naji mutum ya fara amayo kalmomin nan, ban san lokacin da hakan take faruwa ba, kawai sai dai in tsince ni nayi nisa a duniyar tunani, I couldn’t help it.
Umar ya murza yatsunshi biyu a fuskata, sautin da suka yi ne yasa na dawo daga tunanin dana shiga. Na kalleshi sosai, kallona yake yi, nace “me kace?”.

Fuskarshi ta nuna alamun damuwa da kulawa, yace “Sweetie, ban san sau nawa kike so in fada miki cewa bana jin dadin abinnan da kike yi ba. Sau tari sai in ganki kinyi nisa cikin tunani, hakan yana kona min rai. Don Allah ki fada min, idan wata damuwa ce take damunki, ki fada min inyi miki maganinta!”.
Na girgiza kai, ina mishi murmushi a sanyaye, “babu abinda yake damuna Umar, kaima kasan cewa da da akwai zan fada maka ne”.
Ya juya kai, “abinda kike cewa kenan kullum, babu canji. Har zuwa yaushe ne don Allah? Sai inga kamar baki jin dadin kasancewa da nine”.

Na kalleshi cike da mamaki, “meya sa ka yin wannan tunanin? Ni fa na fada maka babu abinda yake damuna, idan akwai zan fada maka wallahi, kaima ka sani”.
Ya rausayar da kai, “to ai shikenan sweetie, yadda kika ce”. Shiru ya ratsa wajen, kafin naga ya bude dashboard ya ciro wani kwali. Yanayin tsayin kwalin yasa nayi zargin waya ce a ciki.
Ya miko min, bakinshi dauke da murmushi kamar zai tsaga bakin. Yace “dazu na ganta a shago, sabuwar shigowa ce, ban yi tunanin kowa ba sai ke lokacin dana ganta”.

Na sanya hannu na karba tare da budewa, sabuwar wayar Samsung ce sai sheki take yi. Duk da bai fada min kudin wayar ba, nasan ba karamin kudi zata yi ba.
Cikin alamun tambaya nace “amma me yasa? Ina da waya, ka tuna?”.
Murmushin fuskarshi ya bace, “na sani mana, shi yasa ma na sai miki. Na kula da taki ta ma fara fading fa, kai gabadaya ma ta tsufa”.
Na kai yatsa daya na shafo saman hancina, wani abu da nake yi unconsciously idan magana bata karbu a wajena ba, ko kuma idan maganganun mutum were so bored. Niyyata in tambayeshi sai me don wayata ta fara tsufa? Naga dai ina amfani da ita lafiya lau, kamar dai yadda sauran masu latest wayoyi suke yi. Sannan wayata lafiyayyiya ce, bata bani wata matsala balle yace saboda matsalar ta ne.
Sai dai nayi shiru kawai, nasan cewa idan na daga baki nayi magana hakan zai kaimu ga yin sa’in’sa, hakan kuma ba dadi zai mana ba. Don haka nace mishi “to nagode kwarai, Allah ya amfana. Amma zaka amshi tsohuwar tawa wayar ne ko?”.

Yayi wani irin murmushi, idanunshi na karade fuskata da kallo, “ko kadan sweetie na, amma zaki iya bani dan kiss, a matsayin tukuici na”.
Na daga kai na kalli tsakiyar idanunshi, babu alamun wasa ko kadan, alamunshi sun nuna da gaske yake. Duk da haka, sai na maida abin wasa, nayi yar dariya kawai, “dadina da kai ka cika ban dariya wallahi Umar… Bari in koma daga cikin gida don lokacin da aka dibar min ya kusa cika!”..

Ban jira ya bani amsa ba, na yunkura da niyar fita daga motar. Kawai ji nayi murfin motar ya koma ya rufe, tare da wani karamin kara alamun an sa motar a lock. Na kai hannu da niyar bude motar, sai dai naji gam, kamar yadda nayi zato ya rufe ni.

Na juya ina kallonshi, fuskata a dinke tsam babu alamun wasa balle yayi tunanin kawo min maganar shirme, nace “meye haka? Bude min kofa in fita don Allah”.
Ya gyara zamanshi sosai, “a’ah, magana zamu yi dake sosai. Na kula duk lokacin dana fara furta miki abinda yake cikin raina, sai ki banzatar da maganar ki maidata wasa, an fada miki ni dan wasan kwaikwayon ban dariya ne? Ni fa in fada miki gaskiya na gaji haka nan Na’ilah! Na gaji! You are officially my girlfriend!! Yakamata ace zuwa yanzu mun wuce kan wannan maganar, ba tun yau ba yakamata ace wannan maganar a tsakaninmu ta wuce, ace mun wuce wannan matakin. Nima fa mutum ne. Nima ina so ace ina taba ki, ace zuwa yanzu jikinki ya riga ya saba da nawa, amma kullum sai ma kara janye jikinki da kike yi daga nawa, to na gaji, yau sai dai ayi ta ta kare tsakanina dake!!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button