A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Duk bayanan da take yi sai lokacin ta dago ta kalleni, ganin yadda nake kallonta kamar wata tababbiya yasa ta sake sakin wata dariyar, “da gaske ba wani abu bane, ni wallahi ban damu ba. Besides, su suke yin abincinsu da rana, wanda sai na ga dama nake ci”.
Nace “ai shikenan, me zan taya ki dashi ne?”.
Ta jefo min peeler, na cafe, tace “fara da dankalin can mu gani”.
Na fara fereye dankalin yayin da taci gaba da soya kayan miya da tayi grating.

Cikin dan lokaci kankani na gama firar, muna yi muna hira jifa-jifa, duk da dai shiru yafi yawa. Na kunna stove tare da dora frying pan da mai a ciki, yana yin zafi na fara zuba dankalin da na yanka a tsaitsaye, bayan na zuba maggi da dan gishiri, wata dabarar soya chips da Fatsu ta koya min.

Muna gamawa ta dauko kula da flask, ta zubawa Yaya nashi da kunun gyada, fari tas dashi yana ta kamshi, ta kai falo ta ajiye.
Muna cikin maida kayayyakin da muka yi amfani dashi bayan mun wanke, muka jiyo karan bude gate. Janan ta leka ta tagar kicin din da take fuskantar gate, ta jiyo ta kalleni “Yaya ne!”.
Na ajiye frying pan a inda yake na juya ina kallonta, “bari in shiga wanka kawai, bakwai ta kusa yi”, kai kawai ta gyada min saboda hankalinta yana kan sauran kunun gyadar da take juyewa a cikin wani babban silver flask. Na fita daga kicin din.

Ina shiga daki na hada kayan da zan bukata na fada toilet. Bandakinta babba ne, yana da fadin shi daidai misali da kuma kayan amfani na zamani. Nayi amfani da sabulunta na ‘Vix’ mai kamshin sandalwood nayi wanka. Ban tsaya bata lokaci ba don nasan bamu da cikakken lokaci.
Ina gama wankan nayi amfani da karamin towel na kafe jikina. A cikin bandakin na zura doguwar rigar material ruwan kasa mai laushi, kafin na fita.

Janan tana gefen katifarta daure da towel, waya a hannu, da alamun jirana take yi. Ta daga kai ta kalleni lokacin da taji na maida kofar bandakin na rufe.
“wai fada kuka yi ne ke da Umar?”.
Naji wata irin faduwar gaba lokacin da naji ta ambaci sunanshi. Tunda na tashi da safe nake ta gujewa tunaninshi a cikin raina. Na hana kaina sakat, da naji sunanshi ko fuskarshi na shirin fado min a cikin raina sai inyi saurin sako wani abun daban.
Na daka fuska ina zama akan kujerar dake gaban dressing mirror dinta, “me kika gani?”.

Cike da tuhuma tace, “ban sanar dake bane kawai, amma tun jiya da dare yake kiran wayata da turo texts, sai daina dagawa nayi. Yanzu ma tun dazu yake kira, yace in baki hakuri”.
Nayi kwafa kawai ban amsa mata ba, ta tashi tsaye tazo ta dafa kafadata, “ki daure ki daga kiranshi don Allah, baki san abinda yake son ya fada miki ba. Nayi zaton kun wuce matakin irin wannan fadan ke dashi?”.
Na harareta ta cikin madubin, “bamu wuce ba, kuma ma in Allah ya yarda wannan shine karo na karshe da zamu yi fada dashi, we are done Jan!”.

Fuskarta bata nuna komi ba, babu mamaki, farinciki ko akasinsa, sai kai kawai data gyada, tace “bari inyi wankan nima, amma ki dai daure ki bude wayarki, ko ba don shi ba saboda mutane masu nemanki. Yaya Mudan ma ya kirani lokacin da kina wanka, shima dai ya nemi wayarki a kashe”.
Sai lokacin naji nayi murmushi, nace “wato har yanzu dai Mudan dinnan yana nan ko? Kinsan Yaya ya tsani sunan nan”.
Tayi dariya, “ramawa kura aniyarta kenan!”. Daga haka ta shige bandaki. Nayi dariya kawai naci gaba da shirina.

Zuwa lokacin dana gama hada komi da zan bukata, Janan ta fito daga wanka itama ta fara shiri. Da wayarta nayi amfani na kira Yaya, yana jin ni ce ya fara zuba min korafin ina na shiga? Excuse din dana bashi shine ‘wayar ce babu caji tun jiya’.
Yace “su Malam ne nima suka dameni da kira tun safiyar yau, wai suna ta kiran wayarki su ji in kin sauka lafiya kuma a kashe, shine hankalinsu ya tashi!”.

Ni gabadaya na ma manta ban kira su ba a jiyan. Na manta yadda suke ne, musamman idan zanyi tafiya, hankalinsu baya kwanciya sai sunji muryata na tabbatar musu da saukata lafiya sannan.
Nace “afuwan, ka basu hakuri don Allah. Wallahi mantawa nayi ban kira su ba, idan nayi caji zuwa anjima zan kira su”.
Yace “to shikenan, Antynki tana gaishe ki”, daga nan inda yake ina jiyo sautin muryarta tana kiran sunana, nayi murmushi nace “a gaishe ta itama, sai anjima”. Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefena.

Ina zaune har Janan ta gama shirinta, ta dauki jaka tana zuba jotters da handouts dake tsakiyar dakin a yashe inda muka barsu jiya da muka gama karatu. Na mike nima ina kara gyara kayan jikina. Muna gamawa muka fita daga dakin, ina kallo tasa key ta rufe dakin ta maida key din cikin jakarta.
Har yanzu falon babu kowa, gabadaya gidan ma shiru kake ji kamar babu masu rai.
Sai da muka fita daga gidan muka dauki hanyar da zata sada mu da babban titi inda zamu hau bus, tace “Yaya sauri yake yi, shi yasa bai tsaya kun gaisa ba, ya bar sakon gaisuwa dai”.
Nayi murmushi, “babu damuwa, idan ya dawo zamu gaisa ai in da rabo”.

Ta zage zip din bayan jakarta ta ciro dubu biyar, sababbi kar ta miko min, na amsa ina kallonta fuskata cike da alamun tambaya, nace “me zanyi dasu?”.
Ta daga kafada, “Yaya yace a baki!”.
Na zaro ido, “what?…,” a lokaci daya kuma ina mika mata kudin, “A’ah, gaskiya ba zan amsa ba, this is way too much!”.
Ta harareni, “sai ki bari in yazo ki maida mishi da hannunki. Kafin kuma ki fara wani tunani, wannan ba wani abu bane. Kamar kudin albashi ne daya saba bamu gabadayanmu har su Haleemo, saboda hidimar makaranta da sauransu, kin gane?”.

Na karkata hankalina gabadaya na maida kanta, “duk sati yake baku 5k, kawai saboda hidimar makaranta?”.
Ta gyada kai tana kallona, irin ba wani big deal bane a wajenta.
Nayi yar dariya, “Woah, dole a makale a gida aki tafiya, kuma dole ace kwadayi nazo yi ba wani abu ba. Maganar gaskiya though, ba zan iya amsar kudin nan ba gaskiya, kiyi hakuri ki amsa”.

Ta fara huro hanci alamun na fara bata haushi, “sai kiyi kuma tunda kin saba, ni na gaya miki sako aka bani na baki, in kinga dama kada kiyi amfani dasu, ki jira har sai Yaya ya dawo sai ki maida mishi ki gani idan amsa zai yi!”.
Na dan dakata da tafiyar da nake yi, “meye abin fushi kuma anan Jan?”.
Tace “ke din ce ai idan ba gani kika yi ana miki wuta ba, baki cika fahimtar abu ba”.
Nace “to naji, na karba, kuma na gode, Allah ya saka da alkahiri”.
Ta harareni cikin wasa, “abinda yakamata ki ce tun dazu kenan, ba ki tsaya neman magana ba!”.
Nayi dariya kawai jin abinda tace. Muka cigaba da takawa har muka fita bakin titi. Shatar keke-napep kawai muka yi saboda lokaci daya fara kurewa.

Allah ya taimaka muka isa akan lokaci. Kasancewar duk practicals ne muka yi, kuma abubuwa basu fara yin nisa ba, yasa bamu jima ba muka taho gida. Karfe biyu ma bata karasa ba muka dawo.
Wannan karon ma napep muka hau. Muna sauka, wata hadaddiyar Range Rover tana shiga gidan. Muka bita a baya muma muka shiga gidan. Ganin ta gangara can bangaren Yaya Jameel, yasa na kalli Janan, “Anty Sarah ta sake mota kenan?”.
Tace “da alama, ko kuma ta gidansu ce. Tunda ko yau da safe motar bata nan”.

Wadda muke maganar a kanta ta bude gidan gaba ta fito. Matar Yaya Jameel ce. Saratu da muke kira, ko ince ake kira da Sarah, cikakkiyar yar gayu ce, wadda tasan fashion, kodayake kamar akan abinda naji ance tayi karatu kenan, ko kuma dai wani abu mai kama da hakan. Daga yanayin yadda take shigarta, takunta da gudanar da al’amuran rayuwarta, zaka tabbatar da cewa wayayyiyar mace ce, wadda ilimin boko ya ratsa ta. Gidansu gabadayansu yan boko ne. Kai ita kanta a kasar Germany naji ance taje ta hado degree dinta. Matsalarta daya, rashin shiga mutane. Zaku iya kwashe sati cikakke baku hadu da junanku ba, ni da yake dama ba zuwa gidan nake yi sosai ba, zan iya cewa na kwashe watanni fiye da biyar ban ganta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button