A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Mintunanmu talatin kacal muna hira ta hanyar musayar rubutattun kalmomi, sai gani kwance rigingine a tsakiyar daki, ina kallon fankar dakin dake juyawa, waya a hannu ina ta faman rubutu, yayin da lokaci zuwa lokaci sautin dariya zai fito daga baki na, walau na sani ko ban sani ba. Hakan ya kan sa Jan, da har lokacin tana kan waya, zata juyo ta kalleni cikin alamun tambaya, amma bata tambayeni ba.

Zuwa lokacin da yayi min sallama akan wani aiki da zai tafi yayi, ba ni kaina ba, hatta zuciyata da gangar jikina naji sun aminta da mutumin. Wanda hakan a karan kanshi ma abin tambaya ne, na farko ban san mutumin ba, babu abinda na sani dangane dashi sai sunanshi, yana aiki da wani kamfani da yake sarrafa takardu, shikenan. Dana tambayeshi yana da mata? Sai yace ba ga ki nan ba? Hakan yasa naji sautin bugun zuciyata kamar zai tsaga tsakiyar kirjina zuciyar ta fito.
Tsakanina da Allah ban so muka yi sallama dashi ba, na tabbata idan zamu kwana muna chatting dashi ba zan taba damuwa ba a cikin raina, kai a takaice ma zan so hakan ba kadan ba. Muka yi musayar sai da safe, ya tafi bayan ya turo min ‘sleep tight!’, ya Allah, ban taba jin dadin ganin kalmomin nan daga kowa ba a rayuwata sai a yau din nan.
Yana sauka naji gabadaya chatting din ya fita daga raina, don haka nima na sauka.
Na lalubo jakata na ciro littafai daga ciki na fara karatu da bibiyar practicals din da muka yi yau.

Sai wajen karfe goma Jan ta gama tata hirar da Almunta, (yadda take kiranshi). Ta juyo ta kalleni tana murmushin tsokana, “fadan masoya hutu, wato saboda kun shirya shine kike wannan glowing?”.
Nayi murmushi kafin na jefa mata harara, “ni kada ki min sharri wallahi”.
Tace “wani sharri? Ga abu nan a fuskarki, kin kuwa ga yadda kike ta zuba murmushi sanda kuke chatting dinnan? Har wani dariya kike yi, irin soyayya tayi dadi dinnan!”.

Na danyi frowning ina kallonta, a hankali nace “ba da Umar nayi chatting ba dazu”.
Ta hangame baki cikin mamaki, “wasa kike yi ko? I mean, idan ba Umar ba, waye to? Yanzu da kika fadi haka sai na tuna Umar baya dogon chatting, wanene muka samu??”. Ta karasa fada tana daga min gira cikin alamun tsokana.
Na jefeta da littafin hannuna, ta cafe tana dariya, “fada min mana!”.
Na mike ina tattara kayan dana baza a wajen na maida su cikin jaka. Bandaki na fada kai tsaye na barta tana ihun, “ko shekara zaki yi a ciki sai kin fito kin fada min wanene yarinya!”. Dariya kawai na saki mai sauti. Nasan kafin in fito ta manta da zancen.

Har mun kashe wutar daki bayan mun kwanta, Janan ta kira sunana, na amsa a dan gajiye da kuma barci daya fara cin idanuwana, tace “wai me ya hada ki da Umar ne da?”.
Nayi sighing a hankali, “abinda ya faru ya riga ya faru Jan, mun riga mun shirya dashi, that’s all that matters. Tone-tonen abinda ya riga ya faru, babu abinda zai mana, don haka ki manta da maganar”.
Tace “of course sugar, baki da matsala dani”.
Kaunarta naji tana kara ratsa zuciyata, fahimtarta da goyon bayanta a kullum suna kara sa inji ta can cikin zuciya da ruhina. A hankali nace “nagode Jan”.
Ina jin sautin murmushin data saki cikin duhun dakin, “sai da safe Na’ilah!”.
Nima na maida mata martanin murmushin duk da nasan ba lallai ta gani ba, nace “sai da safe Jan!”. Na juya barin damana, tare da rufe idanuna.

Daren ranar mafarkai nayi masu yawa, da yawa daga cikinsu sun kunshi wani mutum da yake ta nanata kalmar, “ke ce Matata!,” kamar waka.

-Afuwan, in shaa Allah gobe zan turo mai yawa, wannan dinma aradun Allah da kyar hannuna da idanuna suka bada hadin kai nayi typing dinsa. Thank you all.

F.W.A

.

.

☆⋆10⋆☆

A gabadayan tarihin rayuwata, ban taba, ko a cikin mafarki kuwa, tunanin akwai wata rana da zata zo da zan kwanta in kuma tashi da tunanin abu daya a cikin raina ba, musamman idan abinnan ya kasance d’a namiji. Amma yau sai gani na tashi cike da tunanin wannan bawan Allah da ko sunan shi ban sani ba. Har nayi wanka, na shirya, muka karya, muka dauki hanyar asibiti, tunaninshi ne a cikin raina. Daidai da sakan daya bai bar cikin raina ba.
Muna kan hanya, text message dinshi ya shigo cikin wayata. Na zaro wayar daga cikin jaka na daga, kawai cewa yayi,
‘salam, just wanted to say hi… Ban sani ba ko kinyi tunanina tunda kika tashi, ni dai nayi. Anyway, have a nice day!.’
Ji na nayi kamar wadda aka wa kyautar kujerar makkah. Garin bai ma gama wayewa ba, amma wannnan text din kadai made my day already.
Na shiga cikin contacts dina nayi saving number da, ‘Mysterious’. Wannnan a karan kanshi abin tambaya ne ga wadanda suka sanni farin sani, domin haka kawai bana saving lambar mutane a cikin wayata, musamman wanda na sani na rana daya kacal, abu ne mai matukar wahalar yarda a wajensu.

Yau ma da wuri muka dawo gida. Yau gidan babu kowa, muka dauki makullin gidan a wajen da suka saba ajiyewa muka bude muka shiga. Bayan sallar la’asar muka shiga kicin ni da Jan, muna cikin girki sai ga Haleemo ta fado kicin din, bamu ma ji lokacin data shigo gidan ba. Ta mana sannu muka amsa, tace “don Allah wayar wa take da sauran canji a cikinku ta taimaka min inyi kira?”.
Jan tace ta baro wayarta a daki, ni kuma da wayata take saman cupboard muna sauraren kida da ita, na dauka na bata. Tayi godiya ta amsa ta fita.

Janan ta kalleni bayan fitarta, “da alama kuna shiri da Haleemon nan”.
Nace “tafi sauran yan uwanta kirki da rashin rawar kai shi yasa”.
“uhmmm, don dai kawai ba a gabanki take yin abubuwa bane, amma kada ki bari shiru-shirunta ya kwashe ki wallahi, duk ta fisu rashin mutunci”.
Na kalli kofar da tabi ta fita cike da mamaki, “amma kuma yanayinta sam bai yi kama da irin nasu ba”.

Tace “dama idan mutum bashi da mutunci, rubuta shi yake yi a goshi ne? Ai ba tambari gare su ba, lokacin da suka buga miki shi ne zaki ji kamar kiyi kuka”. Na kyalkyale da dariya.
Ta girgiza kai, “wato dariya ma na baki? Zaki yi bayani ne yarinya!”.

Haleemo ta dawo kicin din, ta miko min wayar tana murmushi, “yauwa, nagode Na’ilah”. Na jinjina mata kai ina dan murmushi kawai, na karbi wayar na maida na ajiye.
Ta leka kanta cikin tukunyar da muke girki da ita, “sai kamshi mai dadi yake tashi, me kuke dafawa ne?”.
Nace “shinkafa ce da miya”. Tayi murmushi, “ki ce yau dadi zamu ci? Amma nasan sai zuwa dare don yanzu kaya zan dauka, wajen kamun bikin wata cousin dinmu zamu je”.
Ni da Jan dai “humm!” kawai muka ce mata, ta fita daga kicin din. Bayan ta dauko kayan ma, sai data biya ta mana sallama sannan ta wuce. Mu dai muka samu muka gama girkin. Muka zuba musu a cikin manyan kuloli, mu kuma muka dauki namu muka wuce daki.

Da dare Umar yazo, mun jima dashi a gefen gidan muna hira dashi, fir naki shiga motarshi. Ko yanzu ma hirar da muka yi dashi cikin dari-dari muka yi ta. Tun yana korafi har ya koma magiya, ya dawo ban hakuri. Nace mishi yayi hakuri, amma na kasa sakin jiki dashi, a haka dai muka yi sallama.

                              *

Ranar assabar yini muka yi a daki. Yaya ya dawo daga Abuja, amma da yake a gidan Anty Ameerah ya sauka, kawai dai ya biyo ne muka gaisa. Ina bandaki lokacin daya dawo a jiyan da yamma, har ya tafi bamu gaisa ba. Naji Jan tana cewa sai yau da yamma zai dawo nan.

Tunda muka tashi wajen karfe goma na safe, brush kawai muka yi muka fita falo. Da alama mutanen gidan suna daki don babu kowa, muka shiga kicin da niyar dora abinda zamu karya dashi. Ga kaya nan baje a kicin din, da alamu anyi amfani da kayan ne amma ba’a wanke ba. Abinda suke mana kenan tunda nazo gidan, kodayake nafi kyautata zaton sun riga sun saba yin hakan ne tun ma kafin in zo gidan. Idan suka yi amfani da abu, anan zasu watsar dashi sai dai mu mu gyara. Hatta da su plates din da suka ci abinci, yawanci anan tsakiyar falo suke barinsu sai idan mun je gyara sannan zamu dauke shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button