A ZATO NA COMPLETE

Yanzu ma tattara su kawai muka yi, bayan mun dama kunun tsamiya, Janan ta soya mana kosai muka shiga daki muka ci.
Muna cikin ci muka ji anyi knocking a kofar dakin, muka kalli juna ni da Jan, kafin ta tashi ta bude kofar. Ina ji ta fara cewa “Yaya ina wuni?”, nayi sauri na lalubi hijabi na dora a saman kaina, nima na tashi lallaba na raba ta gefenta na durkusa nima na gaishe shi. Ya amsa hankalinshi akanta.
Dadina da halin Yaya kenan, yana da kulawa, sai dai yana da kame kai matuka. Bai cika sakarwa Janan fuska ba, amma kuma ta acts dinshi kadai zaka san da cewa yana matukar son ta, kuma yana kulawa da ita matuka.
Ya kara zuro kanshi cikin dakin yana shinshinawa, “meye haka kuka ci yake neman tado min yunwata?”.
Janan tayi dariya, ni kuma na sunke kai a cikin hijabi ina dan murmushi. Tace “kosai ne muka yi, ko zubo maka zanyi?”.
Idanunshi suka dan bude sosai, kamar alamun hope ko dai wani abu mai kama da haka, “kun girka da ni ne dama?”.
Tace “mun dai yi da dan yawa ne saboda munyi tunanin zamu iya cinyewa saboda yunwa sai kuma muka yi saura.”
Yayi yar dariya, “watarana zarinki zai janyo miki yin kibar da baki so. Ni dai tunda Allah ya taimakeni ya tsaga da rabona, ki zubo ki kawo min ina falo. Dama ban karya ba wallahi…. Mutanen gidan basu tashi bane?,” ya tambaya yana juyawa yana kallon falon kamar mai duba wani abu.
Janan tace “bari in kawo maka kunun”, ba tare data amsa mishi tambayarshi ta karshe ba. Ya juya ya fita yayin da ta bi bayanshi ta dawo da plate da kofi a hannunta, ta zuba mishi ta cicciba ta fita. Ina jiyo sautin tashin muryarsu, suna hira, don haka na janyo wayata na jingina da bango na tsokano My mysterious Man, kamar yadda sunan nashi ya koma yanzu cikin wayata.
Cikin yan kwanakin nan, mun kulla wata irin abota mai karfi dashi. Bai taba kirana a waya ba, kullum daga text sai ta chats kawai muke hira dashi, duk da cewa Allah kadai yasan yadda nake iya cijewa rashin jin muryarshi da ban taba yi ba, ban taba kokarin gwada kiranshi ba. Amma ina kwadaituwa da hakan. Ina yawan tunano yadda muryarshi zata kasance, yadda shi a karan kanshi zai kasance in person. I really want to see him. Amma dai na daure, ina jira in ga iya gudun ruwanshi.
Har Janan ta dawo, ina kan waya ina chatting dina. Ina jinta tana korafin watarana sai ta dauke wayata, ko kuma ta goge whatsapp da duk chats dina, sai dai kasancewar hankalina yayi nisa ko jin abinda take cewa bana yi sosai. Sai da aka kira sallah muka hakura.
Bayan azuhur, zaune muke a tsakiyar dakin, nayi matashin kai da cinyar Jan din tana warware min kalbar da tayi min. Saboda tsananin santsin kaina da tsayi, ban cika yin kitso ba. Idan ma nayi, baya daukar kwana uku yake warwarewa da kanshi. Jan take zaunawa ta min kalba, watarana sai ta sanya rubber bands kanana a karshen kowane kitso sannan yake dan yin kwanaki biyar zuwa sati. Shi yasa ban cika yin kitson bama sam.
Littafin ‘Always a Fighter’ nake karanta mana a fili, lokaci zuwa lokaci zan saurara mu dan dara idan na karanta abin dariya, ko kuma mu dan tattauna akan wani abu daya ratso.
Muna cikin haka sai b’ammm!! Karan turo kofa kamar za’a balleta, gabadayanmu sai da muka zabura muka tashi zaune a firgice.
Mimah ta afko dakin a sukwane, kai tsaye bayan labule ta shige ta kame kamar wadda mutuwarta ta biyota. Cikin mamaki nace “Mimah lafiya? Ke da wa?”.
Kafin ta amsa, an sake turo kofar dakin dai an shigo, muka maida hankalinmu ga kofar gabadayanmu. Anty Sarah ta fado dakin, tana karewa dakin kallo, da alamu Mimah ta biyo.
Sai data karewa dakin kallo tsaf, sannan ta jiyo tana amsa mana gaisuwar da muke mata, ta kara da, “Mimah bata shigo nan bane?”.
Muka kalli juna ni da Janan, ni ce na fara cewa “a’ah, bamu ganta ba”. Daga haka ta juya ta bar dakin. Tana bada baya muka hade kawuna ni da Janan muka kwashe da dariya, tace “baki da kirki wallahi, mutum da diyarshi?”.
Nayi dariya nace “kika san ko laifi tayi zata bata kashi? Sannan yarinyar nan tana bukatar fresh air da hasken rana, na tabbata rabonta da waje tunda aka dawo da ita daga makaranta jiya”, na maida hankalina wajen inda Mimah ta boye, “Mimah fito, ta tafi”.
Ba musu ta fito daga bayan labulen, da gudunta tazo ta haye kan cinyata, na shafa kanta ina murmushi, “meye na gudowa daga gida, laifi kika wa Mommy hala?”.
Ta girgiza kai tana dariya, “naa, naki zuwa ta min wanka ne wai zamu raka daddy unguwa, ni kuma Uncle nake so, yace zai kaini wajen granny”.
Muka yi dariyar yadda take maganar ni da Jan, na kamo kumatunta ina ja cikin wasa, “uhhhh Mimah, soooo adorable. Amma yi hakuri ki tafi kafin Mommy tayi fushi, ki bari idan kun dawo daga unguwar, sai Uncle din yazo ya kai ki”.
Yadda ta dago da sauri, idanuwanta manya, farare tas cike da murna yasa naji zuciyata tayi rashin dadi akan turbar da zan dorata tunda nasan ba lallai hakan ta faru ba, tace “da gaske?”.
Na daga mata kai da sauri, “hmm, ni da Janan ma zamu biyo ku muje tare”. Tayi tsalle daga jikina ta dire cike da murna, “yay!!”.
Gabadaya ni da Janan muka saki dariya, nace “to maza ki tafi kafin ta sake dawowa nan, ki kawo mana tsaraba fa”. Ta fita daga dakin da gudu, ni da Janan muka bita da kallo muna murmushi har ta fita, sannan muka cigaba da tsifar da muke yi.
*
Washegari tun da safe, ina jin ko karfe tara bata yi ba, muna kwance muna barcinmu, muka jiyo ana ihun murna daga falo, hakan ya tashe mu babu shiri duk muka tashi zaune muna sosa idanu.
Su Haleemo ne suke ihun ‘oyoyo, Mommynmu!’, a raina na girgiza kai cike da mamaki. Zuwan suruka gidan surukai tun da safiyar Allah Ta’ala? Ban taba jin haka ba.
Janan ta fara shiga ta wanke baki da fuskarta ta fito, nima na bi bayanta. Bayan mun dan fito more presentable, muka fita falon. Babu kowa, amma muna jin tashin hayaniyarsu daga can dakin Raheemah da yake kusa dana Yaya.
Janan ta ja ni muka leka muka gaidata. Daga ganinta kasan kaga mahaifiyarsu, saboda kama da suke yi da ita gabadayansu, kamar tayi kaki ta tofar. Kallo daya zaka mata kasan cewa ka ga wayayyiyar mace, wadda duniya ta bude mata ido, wayewar kan har tayi yawa. Tun daga kan daurin dankwalin da tayi na yan duniya, da shigar da tayi, hakan yasa na daina mamakin irin shigar dasu Salama suke yi idan zasu fita, daga gani babu tambaya kasan gani suka yi ana yi. Duk da kasancewarta fara, har ma da ‘ya’yan nata, amma daga ganin farinta kasan cewa an kara dana kanti.
Ta amsa mana gaisuwarmu tana yatsina kamar taga kashi, tuni naji matar ta fita daga raina. Tun ma kafin a sallamemu, muka sallami kanmu don bamu ga fuskar zama ba a wajen. Muka dafa abinda zamu dafa muka koma daki abinmu.
Yinin ranar nan cur, haka suka wuni a gidannan suna hayaniya da iface-iface kamar kananun yara. Da rana suka zage suka shiga kicin, kada ku sha mamaki idan kuka ji nace muku har uwar, suka dafa abinci, aka soya nama, su kaji, drinks. Muna daki aka kira mu aka ce muje mu ci abinci, muka fita. Ganinsu gabadaya a zaune suna cin abincin yasa muma muka dosana muka zauna, muka zuba namu muna ci, hankalinmu yana kan talabijin da take ta faman aiki.
Mu muka tattara kan kayan muka je muka wanke, suna rarrashe a tsakiyar carpet din dakin suna hira. Ba wai kuma normal hira ba, a’ah, hira ta gulma da abubuwan da basu dace ba. Su ambaci wannan matar, su kwashe mata albarka ita da iyalanta, su kira waccan, itama dai su mata nasu kalar yankar kaunar.
Bayan la’asar aka sayo musu tsire suka baje a tsakiyar falo suna ci, bayan nan suka kure gidan da kidan Ladi mai Kidan Kwarya, suka sha casun su kamar su kadai ne a duniyar.