A ZATO NA COMPLETE

Tunda garin ya waye bamu ga giccin Yaya a gidan ba, amma naji dadin haka. I mean, ta yaya zai kalli surukar shi tana irin wadannan abubuwan? Bana tunanin zai kara kallonta da mutunci. Sai dai again, ban sani ko hakan ta saba faruwa dama can ba.
Sai yamma likis sannan ta fito da shirin tafiya, dan siririn gyalenta a kafada kamar wata budurwa. Lokacin muna kicin muna dafa abincin dare, suka shigo kicin din. Da yake kicin dinsu hade yake da store, suka shige ciki. Babu kunya babu tsoron Allah suka dinga jidar mata kaya, kifin gwangwani, naman gwangwani, madarar gwangwani, kai tulin kaya kamar wani provision store ne suka shiga. Sai da suka cika mata leda shake da kaya, sannan ta bar gidan.
Kai kawai nake girgizawa, ina gyadawa cike da tsananin mamaki daya daure min jijiyoyin da suke sarrafa magana a jikina. Nayi tur da wannan rayuwa, ko wa ya fada musu rayuwar auren hauka ce, kuma abin wasa ce? Da har uwa zata dinga zuwa gidan diyarta, tayi bushashar da taga dama, ta kwashi kaya ba tare da izinin mai shi ba ta kara gaba kamar wani abin wasa? Ita daya kamata ta musu gyara, idan taga sun dauko hanya irin wannan ta tsawatar musu, amma ita ce take dora su akan wannan hanyar? Lallai suna bukatar gyara kwarai a cikin lamarinsu.
F.W.A
☆⋆11⋆☆
Kafin yinin ranar Lahdin nan ya kare, gabadaya naji na gama takura da zama a gidan. Na riga na saba da hayaniyar hostel, can hayaniya ce mai cike da nishadi, ko ta tsakanin roommates, classmates, ko abokai. Na riga na saba da rashin shirun can, duk lokacin da naga damar fita, zan dauki hijabi ne in fita kawai, ba kamar gidan Yaya ba. Nan da kofar gida sai ka nemi izini kamar wata matar aure, hayaniya kuma daga ta zage-zage sai ta gulmace-gulmace, don haka ji na nake yi kamar wata fursuna.
Zuwa ranar laraba da Baba ya turo min kudin registration dina, ji na dinga yi kamar wadda take yawo a sararin samaniya don murna. Dungurungum na ki shiga aji na tafi banki na biya kudin makaranta. Aka bani rasiti na tafi ofishin hall admin dake cikin hostel din yanmata na asibitin koyarwa na Shika na kai mata. Bayan ta dudduba files da sauransu dai, tayi assuring dina zuwa ranar Juma’ah zasu bani dakin saboda sai sun bincika wanda bai cika ba. Nayi mata godiya tare da mata sallama, aji daya na samu ranar, daga haka muka wuce gida.
Washegari ranar Alhamis data kasance ranar public holiday, bamu tashi daga barci da wuri ba, muna ta warware gajiyar da muka kwasa cikin wannan satin don lectures dinmu sun fara yin zafi yanzu.
Can da rana, Janan ta fita zata raka wata kawarta da take can cikin unguwar bakin titi. Ina zaune a falo, su Haleemo, Raheemah da Adi na zaune suma suna kallo, aikin da suka saba yi kenan. Yayin da nake wasa da wayata. Babu wanda yake magana a cikinmu sai su da suke hirarsu jifa-jifa. Abinda yake takura ni kenan. Na tsani zama kusa da mutanen da ba zamu yi hira dasu ba, meye amfanin zama a waje dayan to idan ba za ayi hira ba?.
Aka fara kwada sallama daga can waje, duk muka kalli kofar muna jiran a shigo, duk cikinsu babu wanda yayi kokarin tashi. Na mike na fita wajen, ina bude kofar na ci karo da Ummah tsaye. Nayi tsalle na fada jikinta, tayi yar dariyarta mai cike da haiba ta dora hannunta a bayana tana shafawa.
Cikin tsananin murnar ganinta nake gaidata, ta amsa fuskarta na bayyana murmushi sosai. Tace “Na’ilah, idonki kenan ko?”.
Na sadda kaina kasa a kunyace, rabon da inje Kaduna har na manta, sai dai a waya kawai muke gaisawa, to yanzun ma a wayar mun kwana biyu, nace “Ummah kiyi hakuri don Allah, kin san al’amuran makaranta ne suka yi yawa wallahi”.
Tace “ba wani nan, ke dai kawai kice zumuncinki yayi karanci ne!”.
Na fara girgiza mata kai da sauri, “Allah da gaske fa Umma…”, sai lokacin na tuna a kofar falo fa muke tsaye. Da sauri na matsa gefe daga cikin falon ina cewa, “Ummah shigo don Allah”.
Ta shigo ciki tare da cire takalminta, fararen kafafunta da suka sha lalle jawur gwanin sha’awa suka bayyana. Muna shirin wucewa, Janan ta fado falon. Tana ganin wadda take gabanta ta tsaya cak, “Ummah na?”. Sai kuma tayi tsalle ta dafe ta, na matsa gefe ina kallonsu cikin burgewa.
Hannunta ta kama ta fara ja kamar wata karamar yarinya, ni kuma na bi bayansu. A falo babu kowa haka muka tarar dashi kamar ba yanzu-yanzu na bar mutane suna kallo ba. Ga kuma talabijin din tana aikin yi. Gabadayanmu sai da muka dan dakata, sannan Janan ta wa Ummah jagora zuwa dakinta. Ummah tace “ni fa ba zama zanyi ba, yanzun nan zan koma Kaduna direba yana jirana a waje”.
Ta turo baki cikin shagwaba, “amma dai kin tsaya ko ruwa ne ki sha ko? Sannan ku gaisa da mutanen gidan”.
Ummah tace “suna nan ne? Naji gidan shiru”.
Tace “ina zasu je? Yanzun nan da suke kallo anan falo fa, kila sun gaji da zaman ne suka koma daki”. Ummah ta lalubi kujerar roba daya da take dakin ta zauna akai, Janan ta fita da sauri zata dauko mata ruwa. Gefen katifa na zauna, Ummah tana tambayata karatu da kuma yanayin damina daya fara shigowa, nace lafiya lau.
Babu jimawa Janan ta dawo dakin hannunta dauke da gorar ruwa mai sanyi, Ummah tana sha ko rabi bata yi ba ta mike tsaye, muma duk muka mike.
Janan tana turo baki ta kamo hannunta ta rike, “yanzu Ummah na maimakon ki jira sai yamma tayi sannan ki tafi?”.
Umma tayi dariya tana rungumota jikinta, “Janan kenan, nasan idan kika ji na shigo Zaria ban leko nan ba ba zaki taba bari in samu lafiya bane shi yasa yanzun ma nazo”.
Ta kara turo baki, “ni ai dama nasan kin daina so na yanzu shi yasa!”.
Ni da Ummah duk muka dara, tace “yanzu idan na daina sonki wa zan so Janan??”. Bata amsa ba sai baki data kara turowa.
A kofar dakin Raheemah muka tsaya, Janan ta tura kofar, amma gam, a kulle. Tasa hannu ta dan kwankwasa, nan ma shiru, babu ko alamun motsin mutane. Da ace ba kofar fita daya bace a gidan, duk inda zaka je dole sai kabi ta babbar kofar falo, da sai ince ko ta wata hanyar suka bi suka fita daga gidan. Amma suna zaune fa a falon tazo, daga zuwa bude mata kofa ta shigo har sun bace kamar masu tafiya akan iska? Shin hakan yana nufin da gangan suka buya kenan??.
Ummah ta kallemu tana dan murmushinta na manya, duk da haka zaka karanci damuwa da rashin jin dadi a cikin idanunta. Tace “da alamu ko barci suke yi, kada ku tashe su. Bari kawai in tafi, watarana idan na dawo in Allah ya yarda sai mu gaisa din”.
Janan ta daga baki zata yi magana, nayi saurin girgiza mata kai alamun kada tace komi, nasan ce mata zata yi bai ci ace sunyi barci ba yanzu, hakan kuma shi zai ba Ummah damar sanin da gangan suka shige daki suka rufe mata kofa duk da dai ina zargin da kyar idan bata harbo jirgin ba. Janan ta kama bakinta ta datse, muka saka Ummah a tsakiya muka fita.
Sashen Yaya Jameel ta tsaya, nan kuma sai da muka kwashe kwararan mintuna uku muna buga kofa, har mun fara tunanin kila basa gidan ko kuma barcin rana suke yi, mun fara tunanin mu juya kawai, sannan muka ji alamun ana taba kofar alamun za’a bude. Anty Sarah ta bude kofar tare da dan fitowa waje, alamun bata da niyar barin wanda yake buga mata kofar ya shiga ciki.
Sai dai tana ganin Ummah, ta fara fara’a da nan-nan da ita, “su Ummah ne? Ku shigo daga ciki mana! Sannu da zuwa Ummah, sannu, ya hanya?…”, ta fara jera mata sannu har ta zauna akan kujera. Ko zama bata yi ba ta fada kicin dinsu da sauri.
Ni da Janan kam falon kawai muke bi da kallo, da alama ta canza kayan daki akan wadanda muka sani da. Wannan wasu irin saitin royal kujeru ne purple da gold, gaskiya sunyi kyau ba karya. Ga kamshi da sanyi mai ni’ima da yake tashi, irin mai warware gajiyar nan. Dama can Anty Sarah ba daga nan ba indai ta fannin tsabta ne, babu na biyunta.