A ZATO NA COMPLETE

Ta fito daga kicin din hannu niki-niki da tarin kayan motsa baki akan wani katon tray, ta ajiye a gaban Ummah ta hau zuzzuba mata. Sai bayan data zuba mata komi sannan ta zauna a kasa a gefenta tana gaidata cike da girmamawa, Ummahn ta amsa.
Tace “ai kuwa yanzu suka fita shi da Mimah”.
Ummah tace “ehh, na hadu dasu a babban gida (main house dinsu), Hajiya babba ce bata ji dadi ba kwana biyu dama shine nazo na dubata kuma sai nace bari in biyo a gaisa, kwana biyu”.
Anty Sarah ta sadda kanta kasa tana dan murmushi, “wallahi kuwa Ummah, muna ta cewa zamu leka ku, bamu samu dama bane”. Daga ji kasan ta fada ne kawai, amma duk da haka dai tafi wadda ta rufe kofar dakinta ma gabadaya.
Ummah tace “dama haka ne, bari mu wuce mu”. Tace “Ummahn tun yanzu? Ba zaki bari mu sauke abinci ba, yanzu aka dora”.
Ummah tace “Allah ya amfana, amma nagode”. Ta mike, da sauri Anty Sarah ta koma kicin din, sai gata ta dawo da leda a hannunta, ta juye duk snacks din data kai a ciki, ta mikawa Janan. Daga nan muka mata sallama, ta biyo bayanmu har bakin kofa, ta wa Ummah Allah ya tsare hanya, ta maida kofarta ta gamtse. Ni da Janan duk kai muka jinjina kawai, muka takewa Ummah sawu har inda direban daya kawota yake jiranta.
Janan ta bude mata gidan baya ta shiga, ta dora mata ledar wajen Anty Sarah akan cinyarta.
Kafin direba ya ja motar su tafi ta kalleni, “yata Na’ilah, yakamata ki daure watarana ki zo mana weekend mana?”.
Na yi murmushi a dan kunyace, “in Allah ya yarda Ummah, zamu zo”.
Ta gyada kai, “to madallah, a maida hankali kan karatu dai. Allah yayi muku albarka”. Duk muka amsa da ‘ameen’. Direban yaja suka tafi. Sai da Ahmad maigadi ya maida kofar ya rufe bayan sun fita daga gidan sannan muka juya. Har muka shiga cikin falon babu wanda ya furta uffan a cikinmu.
Muna shiga falon muka ci karo da Adi da Raheemah a zaune abinsu, suna kallo. Wato da gaske dai suna sane suka gudu daki? Haushin abin ya cika ni, naji kamar in rufe su da duka su duka. Duk da ba ni suka wa abin ba, amma zafin da naji sai naji kamar ni ce naje gidan Yaya, matarshi ta rufe kofar dakinta don kada mu gaisa.
Duk da yadda naso danne zuciyata, hakan bai hana tsakin da nake ta dannewa ya fito ba. Daidai lokacin da zamu wuce su.
Adi ta wani tashi a fusace ta rike kugu, “ke malama waye kike ja wa tsaki a cikin dakin nan? Kin ga sa’an ki anan?”.
Na tafi zan zagayeta ni da Janan, tayi saurin kamo wuyan hijabina ta janyo ni, na dawo muna fuskantar juna ni da ita ido da ido, tayi kasa-kasa da nata idanun cikin masifa, “wato yarinyar nan naga alamun wuyanki yayi kauri da yawa irin zama a gidan mutane yayi miki dadin nan. Ke har kin isa in dinga miki magana ki maida ni yar iska?”.
Na kalli tsakiyar idanunta, ina kara nuna mata nima ba kirkin nan gare ni ba fa, nace “ai banyi zaton dani kike ba ganin cewa ni din ba yar iska bace. Maganar kiba kuwa da kike cewa nayi, gwanda ni ina girmama wadanda nayi kibar ta dalilinsu, ke kuma me kike yi?”.
Ta fara hura hanci, dama gasu tubarkallah kamar kofofin wando, tana daga murya, “kan abu ta kazar abun nan!! (ta kawo zagi ta narka). Lallai yarinya kin daukowa kanki ruwan dafa kanki!. Ni zaki daga wannan tsantsaman bakin naki ki zaga kamar wata sa’ar wasanki? To wallahi na rantse da Allah yau ko ni ko ke a gidannan, sai naga wanda ya daure miki gindi!!”.
Wani abin ban dariya shine, gabadayanta bata wuce sa’ar mu ba, abinda nafi tunani kenan tunda ko a tsayi ma na fita. Na kyalkyale da dariya, ina watsa mata wani kallon kaskanci tun daga sama har kasa, duk iskancinta sai data rusuna. Ina shirin maida mata amsa daidai da ita, Janan tayi saurin kama hannuna taja ni.
Adi ta fara ihu, “idan ba tsoro ba ki tsaya mana ki gani?! Wallahi da sai na nada miki na jaki, yadda ko uwar data kawo ki duniya ba zata gane ki ba!!”.
Janan dai ta samu ta ja ni daki, ta maida kofar dakin ta rufe, amma duk da haka bamu fasa jiyo zage-zagen da Adi take yi ba, har Salama data fito itama ta sanya baki itama tana nata kalar zagin da gori. Wai anzo musu gida an zaune, an ki tafiya saboda sanyin AC da naman kaza, ni abin ya ma so ya bani dariya.
Na tsaya a tsakiyar dakin ina ajiye ajiyar zuciya daya bayan daya da sauri-sauri. Ta kalleni, “haba Na’ilah! Sau nawa nake fada miki ki daina biyewa wadannan mutanen? Kin san cewa ba ajinki bane ki zauna kuna sa’insa dasu ba ko?”.
Na harareta cike da fushi, “wai sai ki dinga magana kamar baki wajen lokacin da take sauke min kwandon zagi da dibar albarka!”.
Tace “ko ma menene dai, rashin tankawar yafi tankawar dai. Meye alfanun musayar kalamai, meye a cikin hakan?”.
Na watsa hannuwa sama frustrated, “koma dai menene. Allah ne ya rufa mata asiri bata kai ga daga hannunta a kaina ba, da wallahi sai na baje shegiya yau a gidannan!!”.
Janan ta girgiza kai kawai, ta fada bandaki tana furta “Allah ya shiryeki ke kam!”. Nace “ameen”, cike da izgilanci.
Sai dana huce sannan na zauna a gefen katifa. Sakon text din mysterious daya shigo wayata a lokacin ne ya kara sauko da zuciyata kasa sosai. Na hau karanta sakon ina kara maimaitawa kamar mai harda, daga karshen sakon nashi ya rubuta ‘talk to you soon babe!’,
Shin hakan yana nufin mun kusa yin waya dashi? Nayi tsalle na sake dira akan katifa ina dan ihun murna, Janan da fitowarta daga bandaki kenan ta kalleni baki a dage, “ke kuma lafiyarki lau kuwa? Yanzu-yanzu kina fushi, yanzu kuma kina ihun murna again?”.
Na harareta cike da wasa, fuskata na dauke da murmushi.
Washegari Juma’ah, muka shiga asibiti. Muna fita ajin karfe goma na yiwa ofishin hall admin tsinke. Nan ta bani lambar daki da teller, sai dana fara zuwa bank na biya kudin sannan na sake dawowa wajenta nayi clearance. Dakin mu uku ne, ka’ida mutane biyu ne a kowane daki, amma kasancewar wannan karon muna da yawa shi yasa suka maida shi uku per room. Ni duk bayanan da take yi ba jinta nake yi ba, ban damu ko mu hudu ko biyar zamu zauna ba, bukatata kawai in samu dakin.
Tana miko min makullin dakin, na karba na mata godiya na bar ofis din.
Dakin na fara zuwa na gani, wadanda suke zaune a dakin basa nan lokacin. Na sanya key na bude dakin, na kare mishi kallo sannan na maida dakin na rufe na koma class.
Lokacin period ta biyu ya ma kusa cika, don haka na samu wasu seats da aka tanada a gaban classes na zauna ina jiran su fito. Kafin su fito na ciro wayata na turawa Yaya text din abinda ya faru. Babu jimawa ya turo min da sakon taya murna da tambayar yaushe zan koma cikin hostel din gabadaya? Nace mishi sai ranar Lahdi, nasan duk abinda zanyi Janan ba zata bari in koma gobe asabar ba.
Ina nan har suka fito, na tari Janan a hanya muka dauki hanyar barin asibitin kasancewar mun gama da ranar. A hanyar nake fada mata yadda muka yi da hall admin da kuma ranar da zan koma hostel din. Daga ganin yadda ta turo baki nasan bata yi na’am da maganar ba, don haka na canza maganar kawai zuwa wata.
Yau ma kamar yawancin ranaku, gidan babu kowa muka same shi. Muka tura kofar dakin Janan muka shiga, kayan jikinmu muka fara ragewa muka dauro alwala muka zo muka tada sallah.
Da yamma wajen karfe hudu da rabi muna tsakiyar falo a kwance muna kallon ‘Baaghi’ a tashar Zee World. Meat pie din da Anty Sarah ta miko mana ne daga dawowarmu muke ci da lemun fanta na pineapple a kusa damu.
Gardama muke akan tsakanin jarumi Tiger Shroff da Hrithik Roshan wa yafi wani iya rawa?.