A ZATO NA COMPLETE

“ina fada miki Hrithik shine oga, ni gani nake duk duniya babu kamar shi ma. Kin san dai idan fannin rawa ne, babu wanda zai iya gwada mishi ko wanene kuwa, kada ma ayi zancen physique, halitta, kyawu, and his eyes! Ya Allah, how I love his eyes!!”. Na fada dreamily ina kara zooming hoton shi dake cikin wayata ina kara nuna mata idanunshi da suka fito sosai a daukar da aka mishi.
Janan ta kada idanu sama, “nasan da haka, amma ki duba, Hrithik ya fara tsufa yanzu, Tiger shine jarumi mai tasowa yanzu, sannan idan halitta ce, shima fa Tiger ba baya bane, ga iya lankwasa jiki da acting”.
Na mike zaune sosai, sautin muryata ya fara yin sama, “ni fa komi zaki ce, babu abinda zai canza min tunanina, Hrithik ne nawa. Sannan wa yace miki Hrithik ya tsufa? As in kin kuwa ga yadda yarintar shi take kara fitowa yanzu?”.
Ta daga baki kenan zata musa, sai ga sautin, “idan kun gama musun naku, zaku iya taimaka min da wadannan kayan?”.
Da sauri muka daga kai zuwa inda muka ji sautin maganar. Yaya Bilal ne tsaye a tsakiyar falon ya nade hannu a kirji. Sanye yake da suits ash color, ya sanya tie baki mai ratsin ash color akan white linen shirt din daya sa a kasan suit din. Cikin yan sakannin dana yi ina kare mishi kallo, naji ina raya ‘wannan shine ainihin misalin wanda yarintar shi take kara fita kullum’, a cikin zuciyata.
Da sauri duk muka tashi muna mishi sannu da zuwa. Ya amsa mana yana dan murmushi, “wato maimakon ku zauna kuna debate ko quiz akan karatu, sai ku zauna kuna gardama akan mazajen mutane ko? In anyi magana kuma sai ku ce duk duniya kun fi kowa yin karatu ko?”.
Janan tace “wallahi Yaya ba haka bane, yanzun ma hira ce kawai, arashi ne aka yi kai kuma kazo a daidai lokacin”.
Yace “whatever, kuzo ku taya ni dauko kaya a waje”. Ya juya ya fita, muma muka bi bayanshi. Doguwar riga baka kirar kasar Saudiya ce a jikina, dama gyalenta yana kan kujera don haka na dauke shi na dora shi a saman kaina.
Kayane zube a kofar falon, kayan miya ne, vegetables, su doya da irish potato. Ahmad yake ta daukosu daga cikin mota yana ajiyewa a kofar falo, bakin kofar falon nan ne iyakar da Yaya ya musu. Ba’a barinsu su wuce nan.
Muka fara daukar kayan zuwa kicin sai da muka gama gabadaya. Yaya ya zauna akan kujera a falo yana cire takalmin kafarshi, Na dauko ruwa mai dan sanyi a cikin firjin na dora akan karamin tray na roba da cup, na kai gabanshi na ajiye.
Janan ce ta tsiyaya ruwan ta mika mishi ya karba yana furta “thank you”.
Sai daya kusa shanye ruwan gorar gabadaya, ya ajiye kofin ya koma jikin kujerar ya jingina. Ya cewa Janan “gabadaya kayan can ku raba su uku, kashi daya ku mika gidan Jameel, dayan ku zuba su a cikin wani abun za’a kaiwa Ameerah, sauran ku ajiye su na nan ne”. Muka ce “to”.
Yace “ina Raheemah ne?”, muka kalli juna ni da Janan, itace tace “bata nan!”.
Ya karkata kanshi gefe daya kamar cikin mamaki, yace “ina taje?”. A lokaci daya muka ce “bamu sani ba!”.
Yayi shiru kamar cikin tunani kafin ya girgiza kanshi a hankali, ya tashi tsaye, “shikenan, kuje”. Muka wuce kicin abinmu.
Muna gama aikin daya sanya mu, muka dora girkin dare. Sai gab da magriba sannan suka dawo gidan. Raheemah ce ta leko kicin din, muka mata sannu da zuwa, ko amsawa bata yi ba ta fara jero mana tambayar “yaushe baby ya dawo? Ya tambayi inda nake?”.
Janan ce ta amsa mata, ni kam juyawa nayi ina juya miyar da muke yi, tace “tun dazu dai, kuma ya tambayeki muka ce kin fita”.
Taja wani dan siririn tsaki ta juya ta fita, muna jiyota ita da Adi a falo tana tambayarta me zata ce mishi idan ya tambayeta inda taje? Adin tana cewa “meye na wani rikicewa don ya dawo baki nan? Kawai ki fuske ki ce mishi wajen Momcy kika je mana!”.
Raheemah din tayi ajiyar zuciya, “baki san abinda muke ciki bane kwanannan, a saman ruwa muke dashi wallahi!”.
Adin taja tsaki tana cewa “sai kiyi kuma, na tabbata ko tambayarki ma ba zai yi ba”. Daga haka suka shige daki.
*
Washegari na hade kan kayana tsaf waje guda, nayi wanki da guga da sauransu. Ranar Lahdi Yaya ya bada mota da yamma, Is’haq direban gidan wanda yake musu aikace-aikace ya kaimu hostel ni da Janan. Sai ranar muka hadu da roommates dina, daya musulma ce yaren Ibira, sunanta Murjanatu, dayar kuma Esther Christian ce. Janan ta taya ni hade kan kayana waje guda muka shirya su, daga nan ta min sallama ta tafi. Na rakata har waje ta hau bus ta tafi, sannan nima na juya na koma hostel.
F.W.A
☆⋆12⋆☆
“Ok, spill the beans, me yake faruwa dake ne?”.
Janan ta tambayeni. Fitowarmu daga labour ward kenan da yammacin ranar Laraba, mun tsaya a wani karamin gidan cin abinci dake nan mini market din asibitin. Na fasa lemun Dudu na jefa abin zuka a ciki ina kallonta cike da alamun tambaya, “ban gane ba, me yake faruwa dani?”.
Tace “na fahimci tun shekaranjiya kamar jikinki a sanyaye yake, wani lokacin ana miki magana amma ba kya ji, ko kinji sai in ga kamar ba kya wajen saboda kinyi nisa a cikin tunani. Wani abu yana damunki ne? Ko kuma baki da lafiya ne? Kin gaji da zaman hostel dinne?”.
Nayi murmushi jin tambayarta ta karshe, na girgiza mata kai, “ko daya, kawai dai…”, ta dago kanta da sauri tana kallona cikin sauraren jin mai zan ce.
Na kawo ajiyar zuciya na sauke tare da girgiza kai, “na kasa fahimta ne ni kaina wallahi, kwana biyun nan sai in ga kamar Umar yana min kauce-kauce, amma ban tabbatar ba”.
Ta kalleni a nutse bayan ta taune egg roll din data kai baki ta hadiye, ta kora da lemun la Casera. Tace “me yasa kika ce haka? Ko kuma ince me kika gani?”.
Nace “na farko kusan sati daya kenan rabon da in kira Umar ya daga, daga farko ya fara biyo baya, ya cikani da maganganu marasa kan gado akan wai aiki ne yayi yawa, to yanzu yau kwana uku kenan rabon daya daga kirana ko kuma ya kirani ma. Sannan baya maido min da replying din message idan na mishi. Ke duk chats dinshi babu inda ban bishi na mishi magana ba, amma a banza, na fara damuwa”.
Tace “haba, kada ki wahalar da kanki a banza mana, kamar yadda yace, zata iya yiwuwa aiki ne ya sako shi a gaba!”.
Nace “shine kuma zai kasa daga wayata balle messages dina? Gaskiya sai dai wani abu daban, amma ba wannan ba. Ko lokacin da suka yi posting dinsu, abubuwa ai sun fi haka tsanani, amma a hakan yake samun lokaci ya amsa kirana har ma yazo ya ganni, balle yanzu”.
Ta gyada kai, “haka ne kuma. Amma ki kara bashi lokaci dai, baki san abinda yake faruwa dashi ba, zata iya yiwuwa wani abun ne daban”.
“to shikenan!”. Na fada ina karasa juye sauran lemun daya rage a bakina, na jefa robar cikin kwandon ajiye shara na kalli Jan data gama jefa nata itama, nace “muje muyi sallah a hostel ko? Karfe hudu yanzu zata yi, kuma kinsan hudu da rabi ya kamata mu koma”.
Duk muka mike muna daukar jikkunanmu, muka dauki hanyar hostel. Hostel dinsu yana da nisa da ainihin cikin asibitin, tafiyar kusan mintuna goma sha biyar ce. Muna isa alwala kawai muka yi, muka yi sallah, muka koma ward din da aka kaimu wannan satin.
Muna zaune a reception, Janan tana rubuce-rubuce, ni kuma ina gyara wasu files. Karan shigowar kira a wayata ya katse mu, abu na farko daya fara fado min rai kawai shine Umar. Na rarumo wayar da sauri, a raina ina raya kalar dibar albarkar da zan mishi. Sai dai duk wasu alwasai na sai suka koma can bayan zuciyata, sakamakon ganin mai kiran ba Umar bane, Maryam ce.