A ZATO NA COMPLETE

Bayan nan zamana nayi ina kallonsu suna karyawarsu a nutse, sai daya gaji da ganina sannan ya tambayeni lafiya? Na bude baki ni kuwa nace mishi ban karya ba.
Ya yanko burodin gami da tsiyaya shayin daya sha hadi, yaje yanko kwai amarya tasa hannu ta kame, ta wani langabar da kai tana mishi magana kasa-kasa, ban san me tace mishi ba, na dai ga ya zare hannunshi ya miko min biredi da shayin, na sa hannu biyu na amsa.
Waje na koma, na zauna na shanye. Na dauraye kofin. Daya daga cikin al’adar Mama kenan da na dauka, sam bata barin kwano mai datti. Hatta da cokali idan tayi amfani dashi, a take a wurin take wankeshi.
Ban kara waiwayar Baba da Amaryarshi ba, na wuce makaranta abina.
Karfe sha daya na safe muke tashi daga Islamiya a lokacin, daga can na kan wuce gidan Kakannina, iyayen Mama. Malam Bako Kakana, babban malamin allo ne da yayi suna a ciki da wajen garin Gashua. Yana da tarin dalibai yara da manya da suka kasance a ciki da wajen garin Yobe baki daya. Kullum na tashi daga makaranta, wajenshi nake wucewa inje ya taya ni biya karatuna, ya kuma dora min nashi wanda muke yi, watarana acan nake tsayawa har lokacin komawarmu Islamiya da yamma yayi, bana komawa gida sai dai in koma makaranta daga can.
Ranar ma can na wuce. Bayan munyi karatun, anan nake jin cewa wai ya je ya samu Babana akan maganarshi da Mama. Wai Baban yayi fir yace wai shi bai kori Mama daga gidan ba, ita taga damar tafiya, anan nasan cewa lallai sake aure ya kan sa mutum ya canza halaye.
Ban taba jin Babana ya fadi abinda ba shi kenan ba, sai a lokacin.
A daren ranar da dare Mama ta koma gida. Tun daga wannan ranar, ko in ce tun daga ranar da kafar Ramata ta taka doron kasar gidanmu, bamu sake samun farinciki da kwanciyar hankalin da muka samu kafin tazo ba, har yau dake motsi…
Karan alarm din dana saka ne ya tashe ni daga barcin daya daukeni. Jiya barci ya daukeni ban cire headphone din dana saka a kunne na ba, ban san ma yadda aka yi na cire shi ba, na dai hango shi a kasan gadona. Na kai hannu kasan filona na zaro wayar, dusu-dusu nake ganin komi saboda barcin daya cika min ido. Naga karfe hudu da rabi.
Na kan manta in cire alarm din da yake tashi na sallar asuba duk lokacin da nake fashin sallah.
Kashe alarm din nayi, na koma na sake kwanciya. Sai karfe shida alarm dina na biyu ya sake bugawa. Nan na samu na mike da kyar ina layi. Cikin awa daya, nayi wanka na hada abin kari. Yeah, idan zaku kira indomie da bakin shayi breakfast, to abin kari.
Lokacin Aylah itama ta tashi.
Babu wata kwalliya da na tsaya bata fuskata da ita, daga mai, hoda, da janbaki, bana kara komi. Sai a lokutan da basu cika faruwa bane nake saka jagira da kwalli.
Na janyo stool gefen gadona na zauna na karya, ina gamawa na janyo uniform dina farare tas na saka.
Dogon wando ne fari, da riga wadda ta kai har gwiwata, na daura farin dankwali a kaina bayan na cikuikuye dogon sassalkan bakin gashin kaina na daure da ribbon, sai na dauko karamar farar hijabi data tsaya a saman kirjina na saka.
Na dauki agogon hannu ruwan kasa mai haske na daura, a jikinta naga cewa bakwai da rabi ta kusa yi. Cikin sauri na dauki gyale mai yalwar fadi na yafa a jikina. Na dauki purse, wayar hannu da littafin da nake shigar da duk wasu bayanai na ilimin dana dauka a ranar da naje asibiti, cikin sauri na zura bakin toms a kafata, na yiwa abokiyar zamana sallama na fita har ina hadawa da dan gudu.
Ina zuwa, bus din da take daukanmu zuwa Kongo tana zuwa, don haka na bi jerin mutanen dake layi suna shiga ciki, bayan na biya kudin mota.
Karfe takwas da yan mintuna na sauka a inda na saba sauka. Daga nan acaba na hau, zuwa cikin unguwar Gyallesu, wani karamin public health centre nake zuwa aikin TP na. Karfe takwas muke farawa mu gama karfe daya zuwa biyu. Kowa dai yasan yadda dalibai suke da son yin latti, musamman a irin wannan lokacin da kasan cewa babu wanda zai kulle maka aji, ko ya hana ka attendance.
Duk da lattin da nayi, sai da na riga Janan isa. Ita wannan dama ba’a maganarta idan ana zancen latti, sam bata dana biyu.
Karfe sha daya da rabi muka tashi. Muka fita daga wajen ni da ita a gajiye, kuma cikin sanyin jiki. Babu ranar banza da ba zaka je asibitin nan baka ga abinda zai tayar maka da hankali ba.
Ranar an kai wata mata mai ciki asibitin. Kwanaki uku kenan da aka yi mata scanning, aka ga cewar dan cikinta ya rasu. Maimakon a yi inducing dinta, sai mijin ya ciccibeta suka koma gida. Wani abin karin haushi da ban takaici shine, mijin nata likita ne, duk da ba zan ce likitan ainihi ba tunda shago ne yake dashi babba da ake sayar da magunguna.
Tun shakaranjiya take nakuda, bai kaita asibiti ba sai ya kira unguwar-zoma. Ana ta kai da kawo dai, har jiya bata samu ta haihu ba, shine yau da safe suka tarkata ta zuwa asibitin. Ana maganar a dauketa a kaita Shika, domin a mata tiyata a cire cikin, rai yayi halinsa.
Abin gwanin ban tausayi da takaici. Ga ta da yara kanana wadanda basu gama mallakar hankulan kansu ba.
Har muka je inda muke hawa acaba, abinda muke tattaunawa kenan ni da Janan.
Ta kalleni tana canza muryarta zuwa alamun roko, “don Allah sis, kizo muje gida mana. Sai ki koma da yamma, kinji?”.
Na harareta, “tab! Allah Ya kyauta wallahi. Ni kin ma ga tafiyata!”.
Nayi saurin sa hannu ina kiran daya daga cikin yan acaban da suka yi jerin gwano, suna jiran fasinjoji.
Da sauri ta riko hannuna, “please, kinji? Don Allah!. Wallahi kwana biyun nan gidan babu dadi. Dama a wajen Yaya Bilal nake samu na dan ji sauki wasu lokutan, idan yana gida. To shima kwanannan sai a hankali. Tun jiya da yamma ya rikice, ko kallona baya yi wallahi. Yau da safe dana gaida shi, ko amsawa ma baiyi ba. Kuma ya hana ni yawo, balle inje wani wajen. Don Allah, muje ki dan debe min kewa, kinji?”.
Gabadaya tausayin ta ya lullube ni. Wani irin bahagon zama suke yi da matar yayanta. Wani lokacin sai kayi kuskure kace irin zaman kishiyoyin nan ne da suke zabga dan banzan kishi suke yi.
Ba tare dana sake tunani ba, na gyada mata kai. Tayi tsallen murna tare da rukunkume ni.
Napep muka tara, bayan na ba dan acaban da muka kira hakuri. Unguwar PZ muka nufa, wadda bata da nisa da wajen da muke zuwa TP din.
Gidan Yaya Bilal, inda Janan take zaune, babban gida ne sosai. Daga nesa idan ka hango shi zaka yi tunanin irin family house dinnan ne. Sai dai su biyu ne suke zaune, shi da kaninshi Jameel, sai kuma matansu.
Kowacce tana da part dinta, masu fadi da nisa da kowannensu, ta yadda idan daya taga dama, zata kwashe watanni bata ga yar’uwarta ba.
Sashen gidan Yaya Bilal ake fara tardawa idan aka shiga gidan. Shima can din ya kasu kusan parts uku, duk da sauran biyun duk a kulle suke, dayan ne Janan take zaune ita da Raheema matar Yaya Bilal.
Shekaru biyu da suka wuce ne suka yi auren, basu ma cika da yin shekara biyu ba. Har yau Allah bai basu haihuwa ba.
Abu ne da naji kus-kus suna tashi akan cewa wai, wai Yaya Bilal din baya haihuwa. Saboda matarshi ta farko ma, Ameerah, wadda suka kwashe shekaru kusan shida a tare, auren saurayi da budurwa, bata taba haihuwa ba itama.
A hankali muka yi sallama cikin falon gidan, bamu ji motsin kowa ba, ko na TV babu, balle na mutane. Janan ta ja ni zuwa dakinta, ta koma kicin ta dauko mana ruwa da lemu.