A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na dan matsa can gefe kadan saboda hayaniyar mutane na daga kiran, maimakon muryar Maryam sai naji ta Aliyu. Babu kunya wai gaisheni yake yi, “Yaya Na’ilah ina yini?”.
Mamaki ya kama ni, tunda na dawo babu wanda ya neme ni a gidan, daga iyayen har ‘ya’yan. Kiran Aliyu a yanzu yana nufin abu daya ne,
Na daure na amsa da “lafiya lau Aliyu, ya kuke?”. Ya amsa da lafiya lau, tare da fara kame-kamen tambayar ya karatu na da sauransu dai. Daga karshe dai ya dire a ainihin dalilin da yasa yayi kiran daga farko.

“Kati zaki turo min, subscription dina ya kusa yayi expire!”. Wani lokaci sai in dinga mamakin ko ajiye ni yayi a matsayin personal bank account dinshi, da zai dinga cirar kudi a duk lokacin da yaga dama?
Sai dai Allah bai halicceni da riko ba, sannan bana rikon mutum inyi amfani da hakan idan yana bukatar abu a wajena in wulakanta shi. Bugu da kari ina son ‘yan’uwana, ina kuma iyaka bakin kokarina wajen ganin na kyautata musu, na hidimta musu, matukar ina dashi ina musu iyaka bakin kokarina. Ba yabon kai ba, ina hana kaina ko cikina in ciyar da nasu cikin ko wata bukata tasu.
Su sun san da haka, ina zaton shi yasa suke amfani da wannan damar suna taka ni yadda suke so.

Nace mishi “har katin nawa kake so kuma?”.
Yace “na dubu daya da dari biyar ma ya isa”.
Na girgiza kai, ni kaina wannan watan ban yi subscribtion ba, kodayake Allah ne yasa Janan ta mana ni da ita. Nace “zan turo maka zuwa anjima, yanzu muna cikin ward sai mun fita”.
Yace “babu damuwa, Maryam ma na bidar katin dari biyar”. Babu ko godiya ko karin bayani, ya maidawa Maryam wayarta sai itace ta min godiya sosai. Daga nan muka kashe wayar.

Saboda haka muna fita daga ward din da misalin karfe shida na yamma, na tsaya a kasan ginin na sayi kati na tura musu. Zan yiwa Janan rakiya kamar yadda na saba yi mata, tace “yau dai an hutar dake, ga Almu na can yazo daukata”.
Na kalleta ina daga mata gira cikin tsokana, “shi yasa tun dazu baki yaki rufuwa, masoyin usul yazo gida!”.
Janan ta kai min duka a hannu tana yar dariya, “ni bana son sharri irin naki fa!”.

A haka muka karasa jikin motar Almun Jan, silver Matrix 56 ce, daga ganinta ko dai sabuwar yayi ce ko kuma sabuwa ce dal, yadda take ta sheki da walwali. Yana ganinmu yayi kasa da gilashin motar yana murmushin shi da kullum baya barin kan fuskarshi.
Al-Mustafa kyakkyawan namiji ne, fari, dogo, mai dan jiki. Yana da kirki, haka gabadayan yan’uwanshi suke, wadanda muka sani kenan. Mazauna garin Kaduna, a takaice ma a unguwar NDC unguwar kaji, unguwar su Ummah ainihin gidansu yake. Yayi degree dinshi anan Jami’ar Kongo, yanzu haka lauya ne mai zaman kanshi anan Kaduna din. Soyayyarsu da Janan ta samo asaline tun daga zamanin da take sakandire, suka kulla soyayyarsu mai tsafta, gashi har yanzu suna tare, kuma ana son juna. Ba shi kadai ba, hatta da yawancin yan gidansu sun sanni, na sansu saboda yawan zuwa Kaduna da nake yi, kuma muna yawan zuwa can gidan ko kuma su kannenshi su zo mana. Daga ganinsu kuma Janan ba zata samu matsalar zama dasu ba, saboda suna da kirki da sanin yakamata.

Na gaishe shi a nutse, har ya hada da yar tsokanar daya saba min idan muka hadu, muna ta dariya. Daga karshe dai Janan ta shiga gaban motarshi ya tasheta yana kallona, “to Na’ilar Janan di ta, in shaa Allah a yau dinnan zan wuce Kaduna, sai dai in ce sai Allah yayi mana dawowa kuma”.
Na gyada kai ina dan murmushi, “haka ne, to Allah ya tsare hanya. A gaida mutanen gida”.
Yayi murmushi, “in ce musu me? Wadda ta guje su shekara da shekaru babu waiwaye tana gaida su?”. Ya fada cike da tsokana.
Nayi dariya sosai, “ni wannan korafe-korafe naku dai, in Allah ya yarda hutunmu na gaba zan samu inje Kadunar nan dai, ko kwana biyu ne in muku hakanan”.
Yace “inaa, ai rike ki zamu yi sai kin karas da hutunki sannan zamu sake ki”.
Na girgiza kai ina murmushi, nace “to ai shikenan, yadda kuka ce haka za ayi. Ku gaida gida”. Na musu sallama na wuce don nasan idan na tsaya zamu iya kaiwa har magariba anan muna hira, abin kamar a jinin shi yake, idan kuna hira dashi sam baka sanin lokaci yayi, kafin ka ankara sai dai kaji ka kwashe awanni dashi kuna hira. Ko kuwa yanayin aikinsa ne?.

Har na karasa hostel ban ji daga Maryam ko Aliyu ba, hakan yana nufin katinan sun shiga kenan. Idan naji kiran waya ko please call me bayan na tura kati, hakan yana nufin nayi kuskuren lamba kenan, dana tura kuma zan ji su dif, sai kuma bukatar hakan ta sake tasowa. Maryam ce ma ke kokarin kira lokaci zuwa lokaci haka nan a gaisa.

Akan katifa dana nade ta da zanin gado yellow mai dauke da kwalliyar Malam buda min littafi da wasu kyawawan furanni na zube, da uniform dina da komi har takalmin toms baki da yake kafata. Dakin babu kowa, da alamu basu dawo ba ko kuma sun shiga makotan dakunanmu. Yau ba karamar gajiya muka nada ba, yadda majinyata suka dinga karakaina a ward din da aka tura mu yasa bamu samu mun zauna ba ko da wasa. Na lumshe idanuna a hankali, ina jin gajiyar jikina na neman rinjayata barci ya daukeni. Da sauri na tashi zaune.
Kayan jikina na hau cirewa, na rataye su a jikin kusa dake jikin bango, na daura zanin atamfa tare da dora wata T-shirt baka akai, hula na dora akaina na fita tare da kulle dakin. Can kasa na sauka, da yake a sama muke. Sai dana tsaya a tap na debi ruwa, na daura alwala sannan na ciccibi bokitin ruwana na koma sama.

Murjanatu na tarar a dakin, na mata sannu kawai. Ita kadai take hadamu da ita tunda nazo dakin, wani irin girman kai ne da ita, tunda ta ganta da wata akwalar 406 data fara cin duniya, gani take yi kamar ita din wata shegiya ce. Ni kuma naga meye abin dagawa akan haka? Akwai masu motoci da suka ninka nata a kyau da tsada da ake zaman lafiya dasu a cikin hostel din, wadanda iyayensu suka fita kudi ma. Ni fa ganina nake daidai da uban kowa, yadda kake sanya sutura mai tsada kayi kyau, haka nake saka mara tsada inyi kyau, har ma a kasa banbance mu. Abinda zaka fini kawai in damu, shine yawan maki, a test, assignment, exam ko result, wannan shine kawai. Itama don ta ita ne da bamu gaisa ba, sai dai ni ba’a zaman gaba dani. Ko sannu sai ta hada mu da kai, in yaso zabi ya rage naka, ko ka amsa, ko kar ka amsa, matsalarka ce, ni dai na fita hakkinka. Esther ce muka fi mutunci da ita dama.

Kafin a kira sallah na dora jollop din macaroni, ana kiran sallah na rage wutar karamin gas din dana saya na tada sallah ta. Murjanatu tana zaune a gefen wayarta tana hira da saurayinta har na gama sallah ta na zuba abinci, tunda nazo dakin na kula sallah bata dameta ba ko kadan. Yau da asubahi dana tasheta sallah, cewa tayi period take yi. Sai da rana ta fito gade-gade, tana kallonta suna kallon juna, wai ta kalli gabas ta tada sallah. Na girgiza kai kawai dana tuno abin.
Tayin abincin na mata ta girgiza kai kawai taci gaba da wayarta, nima na girgiza nawa kan na saka cokali na fara ci. Ko loma uku banyi ba Esther ta shigo dakin, nan ta dauko nata cokalin muka zauna muka ci muka yi nak, har da kari. Na sauka kasa na wanke plate din, na sake dauro alwala na dawo sama.

Kan sallaya na koma na zauna ina lazumi har aka kira sallar isha’i nayi. Karfe takwas saura na dauki dan karamin littafin da nake daukar bayanai idan mun shiga ward, textbook akan matsalar da mata ke fuskanta yayin da suke dauke da juna biyu, sai kuma biro da pencil na sauka kasa. Common room naje na zauna, ba jimawa aka fara hasko diramar da nake zuwa kallo kullum. Ko bayan an gama anan na zauna can wani lungu inda babu hayaniya sosai, na cigaba da bita da karatuna har karfe goma tayi. Na mike na koma daki.
Yanzu kuma Murjanatu ce bata dakin, babu mamaki daya daga cikin samarinta ne yazo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button