A ZATO NA COMPLETE

Yace “yanzu dai bari in barki ki karya, nasan baki karya ba kika fara waya da ni. Bayan kin gama cin abincin zan kira ki mu dora daga inda muka tsaya, ki huta lafiya Baby na!”. Daga haka ya tafi.
Na bi wayar da kallo kamar shine a gabana, ina nanata kalmar ‘baby na!’ a cikin kaina kamar wata bakuwar kalma da ban taba jin kamarta ba sai yanzu. Gabadaya sai naji cikina ya cika, bana marmarin komi. Don haka na koma kan katifa na kwanta ina kara maimaita hirarmu da Malam Muhammad M.B a cikin zuciyata kamar wani shirin film da yake matukar kayatar dani, ina zabga murmushi kamar wadda ta fara zarewa.
Amma dan saurara, wani hanzari ba gudu ba., me yasa muryarshi take min kama da wani wanda na sani? Ban tabbatar ko waye ba, amma naji kamar na taba jin muryar nan, inda na taba ji dinne na kasa tunawa.
Ban san iya lokacin dana dauka a cikin wannan hali ba na tsananin bege, sai dana ji an daka min duka a cinya. Nayi firgigit! Na mike zaune ina sosa wajen. Esther dake gefen katifata a zaune dangargar ta kalleni tana murmushi, “Babe, tunanin meye kike yi ne haka? Hala oganki ne?. Ta fada cikin harshen turanci kamar yadda ta saba magana dashi.
Nace mata “nothing o…”.
Tace “na lie… Kada kiyi tunanin ban ga yadda kike ta murmushi ba kina dariya lokacin dana zo fita”. Na zaro ido ina kallonta, da gaske har fita tayi ta dawo ban sani ba?.
Ta kyalkyale da dariya ta dauki wata bakar leda da ban kula da ita ba, ta miko min, “dama kina ta soyewa ta ina zaki ji motsin mutane bayan kinyi nisa a duniyar da daga ke sai shi? Na tabbata za’a iya ciccibarki a lokacin baki ma sani ba!”.
Harara kawai na jefa mata cikin murmushi. Na daga ledar, kamshin masa ne ya fara bugo ni tun ma kafin in ga masar. Sai a lokacin na tuna da cewa jiya da dare kafin mu kwanta na fada mata idan zata je siyan masar yau da safe ta tashe ni koda ina barci ne, don marmarin cin ta nake yi sosai.
Nayi murmushi ina kallonta, “nagode kwarai Esther, ta nawa ce kika sayo?”.
Tace “ban san ko ta nawa kike bukata ba, sai na sayo ta dari biyu”.
Nace “tayi, nagode fa”.
Tace “babu damuwa!”.
Tashi nayi na dauki purse dita na bude na bata kudinta, na kara mata godiya, sannan na sauka kasa naje nayi brush na koma dakin. Bowl na dauka karama ta plastic na juye miyar da aka daure a cikin leda, na fara cin masar.
Ina cikin ci ne na dauki waya na kira Janan, finally, abinda muke ta jira, mysterious dina dai ya kira waya. Nan muka sha ihun murnarmu da maida yadda aka yi. Wani labarin ma ai sai ta shigo ranar Monday sannan za ayi shi baki da baki.
Yinin ranar wannan gabadayanshi, Allah ne kadai yasan farincikin dana yini dashi, wata irin far’ah dana rasa dalilinta, nishadi dana rasa dalilinshi. God, I’m so whipped, totally!!.
Yini aka yi ana ruwa duk da ba mai karfi bane, amma yanzu da nake kudundune cikin bargo a dakina da dare, sanyin da ruwan saman ya haddasa da kuma kamshin ruwa da jikakkiyar kasa da yake tashi, da kuma tsananin taushin muryar Mysterious dake ratsawa ta cikin dodon kunnena a daidai wannan lokacin, sai naji babu wata damuwa a raina. Babu kowa, kuma babu komi a wannan lokacin sai ni sai shi kawai. And nothing matters!.
Tuni mun riga mun sabarwa junanmu jin muryar junanmu a kowace rana. Muryar dayanmu zamu tashi da ita, texts zasu mana rakiya duk inda zamu je a yinin ranar, haka kuma zamu ji muryar juna kafin mu kwanta da dare.
Da asuba tun ma kafin alarm dina ya buga, Muhammad zai kira ni ta waya, nan kira kawai zai yi in tashi, to idan na gama ne zamu yi wayar minti biyar zuwa goma, sai muyi sallama. In shiga wanka in shirya, in karya, in fita. Kafin in karasa ward ya turo min text mai cike da kalamai dadada da zasu sa in yini ina kallon wayata cikin murmushi, ina kara karanta shi over and over, sai in tura mishi amsa. Kafin yamma ta fadi at least zamu yi musayar messages sau uku ko fi, sannan da dare dole ne sai ya kira ni kafin in kwanta barci, watarana ma muna cikin hirar barci zai daukeni sai dai ya kashe wayar in yaji shiru.
Ni kaina nasan cewa na canza, kamar wani abu yayi snapping a jikina ne. Duk wasu makamai da katangu dana sa a jikina, daya bayan daya Muhammad ya bisu ya sassare, kamar basu taba wanzuwa ba.
Wani abu ne da bai taba faruwa dani a tarihin rayuwata, da shekaruna dai-daya har ashirin da hudu a duniya ba. Ban kuma taba zaton zai farun ba. Amma yanzu daya faru, sai nake jin ina zargi da tuhumar kaina, me yasa tun farko ban bar kaina nima naji dadin wannan abu ba? Na dinga takura kaina, ina matsawa kaina? Kodayake, komi yana da lokaci, kuma kamar yadda Janan take yawan cewa, ‘idan lokacin ki kamu da so yayi, baki da yadda zaki yi, kina so ko ba kya so, zaki fada tarkon ko, kin sani ko baki sani ba!’.
To yanzun ma ina tunanin abinda ya faru kenan, lokaci na ne yayi. Na kamu da soyayya, soyayyar Muhammad mai zurfi. Zurfin da ya kai naji ina so inyi kugi da karaji, wanda duk duniya da mutanen cikinta zasu ji cewa ina cikin zazzafar kaunar mutumin da ban taba sakawa a cikin idanuna ba!.
* * *
“Kyawunta ace wannan azumi da zai zo, wani mutumin kirkin zai zo ya dauki dubu ko hamsin ce ya baka, ya hada ka da buhun masara, gero, sukari ko rabin buhu ne! Kai ai da kakar ka ta yanke sa’a!! Sai ka nemi inuwa mai ni’ima kawai ka fuske, ka yini tun safe har dare a kwance Malam, babu ruwanka!!”.
Wani kwandastan mota da muka hayo daga asibitin Shika zuwa kasuwar Samaru yake cewa. Duk cikin motar aka saka dariya.
Wani mutum daga baya yace “wannan duk mafarki ne kake yi, wanda baya zama gaskiya. Abu mai yawa da zaka samu daga hannun manyan nan shine kwanon masara ko gero, ba’a hada maka guda biyu ma. Sai ka samu wani mai tsoron Allah shine zai kawo wata lalatacciyar dari biyu ya dora maka yace kayi nika. Ai yanzu wannan alherin a tsakanin masu kudi kawai ake yi, ka dauka ka kai gidan mai kudi, shima idan ya tashi yin nashi sai ya maido maka. Su kuma talakawa sai suje su nemo da karfinsu”.
Wani ya cafe zancen, “ai sai dai kawai Allah ya kara rufa mana asiri. Wata irin rayuwa ake yi ta danniya da rashin tsoron Allah, mai shi ya dannewa mara shi, masu kudin namu kuma basa taimakon talakawanmu. Kowa kanshi ya sani ba wani abu ba, Allah dai yasa mu dace!”. Duk muka amsa da ameen.
Har motar ta tsaya a bakin kasuwar, da yawanmu muka fita daga ciki, wasu suna ta tururuwar shiga, da alamu ranar da ake zabgawa yau ta gama dakar su.
Ni da Janan muka tsallaka titi muka shiga kasuwar. Kasancewar Azumi yana ta gabatowa, ana tunanin nan da kwanaki biyar masu zuwa ma za’a tashi dashi. Shi yasa nace bari in shiga kasuwa in dan yi sayayya da sauran kudin da nake dasu kafin in cinye su.
Mun shiga mun danyi saye-sayen mu, muka fito hannu riki-riki da kaya. A bakin titi muka tsaya, Jan zata tsallaka ta hau bus zuwa PZ ni kuma in matsa gaba in hau wadda zata maida ni asibiti. Kallon motoci, masu mashina, kekuna da ma masu tafiya akan kafafu da keken guragu nake yi suna ta karakaina, kowa harkar dake gabanshi ce ta dame shi.
Janan ta fara daddabata da sauri, nayi saurin juyawa na kalleta, wata mota da take wucewa ta gabanmu wadda dan banzan go-slow din da ake yi ya saketa, nace “lafiya?”.
Tace “waccan motar bata miki kama data Umar ba?”.
Na kara bin motar da kallo wadda zuwa yanzu ta bace min, yanzu da tayi maganar sai naga irin tashi ce, amma kuma garin Zaria mai fadi, ba lallai ace shi kadai yake da irin wannan motar ba. Ko yanzu da zamu baro asibiti naga wata nurse ta fita a cikin irin motar tashi, wadda har kala bata banbanta su ba. Balle kuma wannan motar dana hango kamar mata da miji ne a ciki? Sannan bugu da kari, Umar yana Kaduna ba Zaria ba.