A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Dana juyewa Janan wannan bayanai, sai ta gyada kai, tace “haka ne, mantawa nayi”. Muka samu ababen hawan suka ragu a lokacin, ta tsallaka da sauri tana min bye-bye, sannan ne nima na juya na shiga bus.


Ranar Juma’ah da wuri na fita zuwa cikin asibiti, kasancewar da wuri na tashi. Ranar tun daga cikin hostel muka fara waya da Muhammad har na shiga cikin ward, sannan muka yi sallama dashi akan cewa zai kira ni kafin ya tafi masallaci.

Har karfe goma na safe babu Janan babu alamunta, hankalina yana bakin kofa, da naji alamun za’a shigo sai inyi sauri in kalli kofar cikin tsammanin itace, sai in ga wani daban. Ganin karfe goma tana shirin wucewa yasa na lalubo wayata daga cikin aljihun wandon uniform dina na kirata cikin faduwar gaba. Hakan bai taba faruwa da Janan ba. Duk son makararta, Janan bata yin fashi, don haka ne naji na damu.

Wayarta tayi ta kara tana katsewa, a karo na kusan uku ne ta daga. Da sauri na fara jero mata tambayoyi, “wai ya ne har yanzu baki zo bane? Baki tashi da wuri bane ko kuma yau kinyi shawarar kin zuwa ne?!”..
Daga farko shiru aka yi, kafin daga baya inji muryar da ba ta Janan ba tace “uhmm, Janan din bata ji dadi bane”.

Naji gabana ya fadi, nayi salati na sanar da Ubangiji, nace “lafiya, me ya sameta? Waye kuma?”.
Mai maganar yace “Asthma dinta ne ta tashi, sannan Bilal ne”. Na kalli wayar cike da mamaki, kwata-kwata muryar bata yi kama da tashi ba, a takaice ma dai muryar bata yi kama data mace ba balle namiji. Amma sai nafi kyautata hakan a matsayin sharrin network kawai.

Nace “Subhanallah! Kuna gida ne?”.
Yace “a’ah, muna asibitin Delicate dake bayan gidanmu, kin san shi?”.
Nace “ehh, gani nan zuwa”. Na kashe wayar da sauri na maida ta aljihu.

Kayana na dauka a gaggauce, na tunkari office din matron din ward din. Na kwankwasa ta min izinin shiga. A gaggauce na mata bayanin abinda ake ciki, nan tace in tafi kawai babu komi, har ma ta kara da ‘ki dubata. Sai ranar Monday idan jikin nata ya warware’, na mata godiya na fita a sukwane kamar wadda zata tashi sama.
Wata irin wahalalliyar asthma gareta, bata cika tashi ba, amma duk ranar data tashi sai ta jikatar da ita. Shi yasa naji hankalina ya kasa kwanciya, ko tunanin komawa hostel in canza kayan jikina banyi ba. Allah ya taimaka na samu abin hawa da sauri kasancewar ranar Juma’ah ce, kowa yana kokarin ya je inda zai je kafin lokacin masallaci yayi.

~Phewwwwww!!!!!

F.W.A

☆⋆14⋆☆

Halin dana sameta a ciki ya sanyayar min da jiki, gabadayanta ta fita daga hayyacinta don ma sun ce wai a hakan ma tayi dama. Yayan da Anty Sarah kadai na tarar a asibitin, a cewarsu wai Raheemah bata jima da barin asibitin ba. Na zauna a gefen gadon tare da shafa gefen fuskarta cike da tausayi, har ta dan fada, gashi yanayin numfashinta bai gama daidaituwa ba har yanzu.
Muna zaune a hakan har rana tayi, Yaya yake ta shiga da fita daga ofishin likita zuwa inda aka kwantar da ita din. An samu tayi barci, bayan anyi mata allura har aka samu numfashinta ya daidaita.

Da lokacin tafiya masallaci yayi, Yaya ya tafi akan cewa zai turo Raheemah tazo ta zauna damu, sai dai har aka fito daga masallacin, har muma muka yi tamu sallar bamu ga alamunta.
Lokacin daya dawo ina kan sallaya a zaune, Anty Sarah kuma tana zaune akan farar kujera tana jan carbi, ya ajiye ledar take away a gefen gadon, yace “ga abinci kuci, likitan yace zamu iya tafiya gida da ita idan ta tashi”.
Anty Sarah tace ta koshi, nima nace na koshi da yake cikina a cike yake.

Karan text daya shigo wayata ne yasa na maida hankalina ga wayar, na duba naga daga Muhammad ne. “Hey baby!”, abinda ya turo kenan. Na kara maimaita text din cikin mamakin kalmomin, motsin da Jan ta fara yi ne yasa na wancakalar da wayar gefe na nufeta da sauri. Yaya ya taimaka mata ta zauna akan gadon, gabadayanmu sannu muke jera mata tana amsawa a hankali.

Yaya ya dauko madarar ruwa ya fasa tare da mika mata, ta amsa ta sha kamar rabi ta maida mishi sauran, yace “har kin koshi?”, ta gyada mishi kai.
Anty Sarah tace “dama ba lallai ta iya cin abinci yanzu ba”.
Yaya ya umarcemu da mu hada kan kayanmu, ya miko gyalen Janan na yafa mata. Da taimakona ta sauko daga kan gadon, ina tallabe da ita a jikina muka fita daga asibitin zuwa wajen da Yaya yayi parking din motarshi. Ya bude mana gidan baya duk muka shige ciki. Bayan ya gama clearing din komi a asibitin, yazo ya shiga motar ya tayar muka tafi.

Yaya Bilal ya kashe motar a ainihin inda suke ajiye motocinsu, farko-farkon shiga gidan, daga nan tafiya ce zaka yi kadan daga bangaren damar ka da zata sadaka da wani zagayayyen karamin garden, grass carpet ne shimfide a wajen, wajen yana da fadi sai kuma bishiyoyin mangwaro, gwaiba, gwanda, ayaba, da sauran kayan marmari dai. Daga gefen garden dinne aka shimfida doguwar hanya da interlocks, kanana masu kyau, itace zata sadaka zuwa bangaren Yaya Bilal. Wadda kuma tayi barin hagu itace zata sada ka da bangaren su Anty Sarah.

Kan Janan yana kan kafadata, wani barcin ne yake kokarin daukarta. A hankali na tasheta, muka fito daga motar. Anty Sarah ta mana fatan Allah sauwake, ta wuce sashenta muna mata godiya. Rabin jikin Janan yana jikina, na tallabota muka wuce saboda har yanzu jikinta babu karfi sosai. Yaya Bilal yana binmu a baya hannu rike da makullin motarshi da kuma ledar take away din da yayi.

Gabadaya mutanen gidan suna falo, wannan karon a zaune suke kawai suna hira sabanin kallo da suka saba yi a yawancin lokuta. Raheemah ce ta fara ankara da shigarmu falon, ta mike tana zuba sannu da zuwa cikin alamun borin kunya, kannenta suma suka mike, “ah.., har kun dawo ashe? Yanzu muke cewa mu tashi mu koma fa! Sannunku, ya jikin?”.
Muka amsa musu ciki-ciki, Yaya ya umarce ni da in taimaka mata Janan zuwa dakinta, don haka na gewaye su muka wuce zuwa dakinta. Bansan Yayan yana bayanmu ba sai dana ji karan sake bude kofa bayan na maida na rufe.
Na kwantar da ita akan katifarta, na ja abin rufa na rufa mata daga kafafunta zuwa rabin jikinta, tuni barci yayi awon gaba da ita. Yaya ya miko min ledar hannunshi, yace “ki samu ki zauna kici abinci haka nan, ki zauna ki huta kema”.

Na karbi ledar, kaina a kasa, wata irin kunyarshi naji ta lullube ni wanda na rasa dalilin hakan. Nace “to, nagode, Allah ya amfana”.
Ya girgiza kai a hankali, wani irin kallo a cikin kwayar idanuwanshi da suka sanya naji jikina ya dauki wata irin kyarma, ikon Allah! Ko dai bani da lafiya ne nima?! Yace “ni ne da godiya Na’ilah! You’ve no idea how grateful I am right now!”.

Subhanallah!! Me ke shirin faruwa da ni ne? Jin fitar sunana daga bakinshi ya haifar min da jin wani irin abu a cikin raina, shin ko mai yasa hakan? Hakan bai taba faruwa dani ba! Sannan muryar Yaya Bilal, yau naji tana min kama da wata murya hallau, matsalar na kasa tunawa ko a ina ne na ji muryar.
Ban san lokacin daya juya ya bar dakin ba, sai karar rufe kofa naji.
Na bude ledar na fito da take away din ciki, guda biyu ne da lemukan fanta suma guda biyu, don haka na dauki daya na ajiye, dayan kuma na barsu a cikin ledar na fita domin in mikawa Anty Sarah nata.

A falo Yaya Bilal ne a tsaye kikam, kamar wani tsohon soja. Su kuma suna lafe akan kujeru kamar wadanda aka kama sun nannagawa sarki garinsu karya. Daga yanayin fuskar shi da take a cune da yadda bakinshi yake kumfa, zaka san cewa fada yake musu, fada kuma bana wasa ba. Tunda nake dashi ban taba ganin fadan shi ba sai yau. Janan tana yawan cewa Yaya Bilal yana da fada, duk da cewa baka sanin fadanshi sai ka mugun tabo shi sannan, to da alamun yau dai an tabo shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button