A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ni dai na kada kai na fita. Yau kofar gidan na Anty Sarah a bude take, abin mamaki, na tura kofar na shiga. Tana kicin. Yanayin gidanta da ka shiga kicin zaka fara tararwa, sai falo da kuma bedrooms. Ta dago ta kalleni lokacin dana shiga, nace “kofar a bude take, shi yasa na shigo kai tsaye”.
Tace “babu komi, ina tsammanin Mimah ne yanzu shi yasa, ya aka yi?”.
Na mika mata ledar hannuna, “dama abincin da Yaya ya kai ne na kawo miki”.
Murmushi naga tayi wanda ya bani mamaki, tace “da kin barshi wallahi kun ci, kin ga abinci ma nake shirin dorawa yanzu”.
Nace “a’ah wallahi, ai guda biyu ne ya kawo”.
Tace “to shikenan, na gode. Ya Janan din?”. Nace “ta koma barci”, daga haka na juya na fita daga gidan.

Har na koma can, Yaya fada yake yi, “… In fada muku gaskiya ba zan dauki wannan cin mutuncin ba! An fada muku ita yar aiki ce? Ko kuma bata san ciwon kanta ba? Waye bai san tana da asthma ba, da zaku barta tayi aikin da zai tado mata shi?!”. Ya dire maganar yana sauke numfashi cikin bacin rai.

Raheemah ce ta samu ta iya magana duk cikinsu, “kayi hakuri, hakan ba zata kara faruwa ba. Ita ce tace zata yi ai…”.

Tun ma kafin ta karasa ya katseta, “ke kuma saboda rashin hankali sai kuka barta ko? Na fa san abinnan ba tun yau yake faruwa ba, ina sane, iyaka gudun ruwanku ne kawai nake so in gani. Wallahi Tallahi, kunji rantsuwar da nayi, ba zan yi kaffara ba! Idan makamancin haka ya sake faruwa, gabadayanku sai kun bar min gidana. Kuma daga yau, duk wadda take son yin girki, ta shiga ta girka abinda zata ci ban yi mata iyaka da komi na gidannan ba, amma kun gama cin abincin Janan. Ba zata kara muku girki ba, haka ko tsinke ta tsince a gidannan da sunan shara ko gyara Allah zamanku a gidan nan ya kare! Kun dai ji na fada muku!!”. Ya wuce dakinshi fuuuu! Kamar kububuwa tare da maida kofar dakin ya gamtso kamar tashin duniya. Mu kuwa duk muka bi bayanshi da kallo baki a dage.

Maimakon hakan ya dan zame musu darasi, su dan saduda koda na dan lokaci ne, inaa. Tunzura su ma yayi.
Adi ce ta fara jan tsaki, “mtswww, aikin banza! Yo mun taba matseta muka ce dole sai ta mana girki ko aiki? Kashi zamu bata idan bata mana aikin bane? Har da za’a zauna ana zagin mutane akan wata banzar bazara, gidan banza dana wofi! An fada musu mu bamu da gidan iyaye ne da za’a zo ana zaginmu ana mana gori?”.

Salama ta cafe maganar, “ke ma dai kya fada. Aikin banza dana wofi, da dai ace bamu da gidan uba ne da sai muji haushi, to mun gode Allah muna da gidan uba, kuma ba a inda ba’a son zamanmu muke zaune ba! An fada mishi mu mabaratan abinci ne??”.

Raheemah kuma tana ta kokarin sanya su suyi shiru a dan tsorace, “don Allah kuyi shiru mana!”, ko kuma tace “don Allah kuyi a hankali kada ya jiyo ku ya sake fitowa!”. Na girgiza kai kawai, wato shi dai mai rai ba’a taba iya mishi. Allah ya kyauta.
Na barsu anan na koma daki. Har yanzu Janan barci take yi. Na duba cikin kayanta na ciro doguwar rigar leshi mara nauyi, na dauki kayan na shiga bandaki na sanya na fito, na sake zama a gabanta.

Har bayan sallar la’asar bata tashi ba, bayan nayi sallah na zauna naci abincin da Yaya ya kawo mana, na maida sauran na rufe dana koshi. Ina nan a zaune naji karan buga kofa, na tashi na bude. Ga mamakina Anty Sarah ce a tsaye da kwando a hannunta, na mata sannu tare da bata hanya ta shiga cikin dakin. Tace “har yanzu bata tashi ba?”.
Nace “wallahi har yanzu, kila an hada mata da allurar barci ne”. Ta gyada kai idanunta akan Janan din, “Allah ya bata lafiya”. Nace “ameen”.

Ta min nuni da kwandon data ajiye, tace “ga wannan idan ta tashi sai taci, ba yawa”.
Nace “Allah ya saka da alkhairi”. Ta amsa tare da tashi ta fita, na bi bayanta na maida kofar dakin zan rufe. Su Raheemah suna falon a zaune har yanzu, ta wuce ta gabansu. Ina tunanin basu cika shiri dasu ba, kila ma hakan ce ta goge mu, ko kuwa wani abu daban? Naga kwana biyu kamar ta dan sassauto.

Sai wajen karfe biyar sannan ta farka, jikinta ya dan yi karfi ba kamar dazu ba. Na taimaka mata zuwa bandaki tayi wanka da ruwa mai dumi. Bayan ta fito na zuba mata abinda Anty Sarah ta kawo, wani irin abu ne tayi da kifi ban ma san sunanshi ba, kamar ta soya kifin, kamar kuma dahuwar ruwa ce, ga veggies da abin yasha sai tashin kamshi yake yi kuwa. Na zuba mata ta samu ta dan ci, tayi sallar azuhur da la’asar da aka yi tana barci. Na ballo magungunanta da aka rubuto mata ta sha, ta zauna a gefen katifa ta dauki wayarta da tun dazu sai gajiya nayi na sakata a silent saboda yadda ake kira.

Ummah ta fara kira, taje umara kamar shekaranjiya naji Janan tace ta tafi. Bayan sun gaisa ta tabbatar mata da lafiyarta lau yanzu, ta miko min wayar muka gaisa da ita. Bayan munyi sallama ne ta amshi wayar ta kira Ya Almu. Ni kuma na dauki wayata ina game.

Bayan sallar magriba Yaya Bilal ya sake shigo mana da abinci, chips ne da sauce da gasasshiyar kaza, nan ma sake zama yayi ya zuba mata dogon sharhi akan aikin gida, ya fada ya kara maimaitawa, daga wannan rana kada ta kuskura ta sake cewa zata yi kowani irin aiki ne in dai na gidan ne.

Ashe wai gyaran gida ne suke yi saboda matsowar azumi, wanda ake tsammanin ranar litinin ko talata za’a tashi dashi. Ita ta fara dauko maganar ayi aikin tun daga farko ranar Alhamis bayan ta koma gida, shine sun shiga can cikin gidan, wani daki da suka maida dakin tarkace kawai, zasu gyara shi da niyar da azumi za’a dinga taruwa acan ana sallar tarawihi, suna fara aikin suka fara zamewa daya bayan daya har suka barta, wannan kura data shaka ita ce fa ta tado mata asthma. Allah ne ya taimaka da asubahin washegarin yau, Yaya Bilal daya dawo jiya da dare, ya leka dakin kasancewar bai samu ya ganta ba daya dawo, shine fa ya sameta a cikin mawuyacin hali. Da Allah kadai yasan abinda zai faru.

Bayan mun ci kaza da chips munyi nak, kwanciya muka yi tun wajen karfe taran dare don ba karamar gajiya muka yi ba daga ni har ita.
Ta kalleni lokacin da nake ta faman buga keyboard din wayata ina turawa Muhammad sako, tun wayar da muka yi da safe bamu yi wata ba har yanzu, haka tun text din daya tura min lokacin da muna asibiti bai sake tura wani ba, nima ban sake tura mishi ba saboda ban samu kaina ba sai yanzu. Bayan na tura mishi ne, idanuna suka sauka akan conversation dina da muka sha yi da Umar, rabon da in ga text dinshi a wayata kusan sati biyu kenan, haka ma kira. Tun ni ina yi da tura text, har na gaji na hakura kawai na koma gefe ina jiran ya sake waiwayata.

Janan ta dafa goshina, tace “ke ma fa kamar baki da lafiya, jikinki zafi sosai”.
Na kai bayan hannu na ina dafa wuyana, “lafiya ta lau Jan, ina tunanin yanayin nan ne, ko kuma mura. Kin san yadda murata take”.
Muna hira kadan-kadan da ita dai har barci ya kwashe mu.

*

Washegari ma haka Anty Sarah ta kawo wa Janan abin kari, bayan fitarta muka koma gefe ni da Janan muna gulmar kirkin da tayi kwanannan.
“Allah da gaske dama can tana da kirkinta, kafin zuwan Anty Raheemah kenan. Tana zuwa kwata-kwata sai ta hau kulle kanta a gidanta, ina tunanin jinin su ne bai zo daya ba”. Cewar Janan tana shan romon naman kan sa data kai mana.

Ni kam na kasa cin komi, sai sandwich daya na samu naci wanda tayi filling da sauce din kwai da sardines na gwangwani, ga cucumber a ciki, shima rabi, sai shayin dana hado mana da nake ta kurba. Tashi nayi bakina salam babu dadi, ga wani shafal da nake jina kamar babu laka a jikina ko kuma idan aka hure ni zan fadi, gefen kaina bugawa yake yi tun karfinshi idan nayi dan motsi, jiya da zazzabi na kwana a jikina, ga wani jiri da nake ji idan na tashi, daurewa kawai nake yi muna hira da Janan, amma Allah kadai yasan yadda kaina yake sarawa. Ita kam jikinta da kwari tubarkallah, kamar ba ita bace tasha jinyar nan jiya ba. Da safe su Raheemah sun leko sun mata sannu da jiki suka kara gaba. Kamar ma unguwa muka fita, don mu kadai muka yini a gidan, sai bayan isha’i suka dawo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button