A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Na girgiza mata kai, “ki daina bada hakuri akan laifin da ba ke kika aikata shi ba Jan. Haushina daya, daya bari son zuciya ya rinjaye shi har ya iya juya min baya, amma kanshi ya yiwa ba wani ba. Na kuma gode Allah da yasa na ga hakan da idanuna, basu dinke ni a baibai ba. Da muka zo muka yi aure a haka, inyi yaya?”.

Janan snorted, na bita da kallo cikin mamaki, tace “wai ke don Allah kina tunanin Umar yana da sha’awar kuyi aure?”.
Na bita da kallo mai dauke da alamar tambaya, amma dai duk da haka na amsa mata, nace “ehh mana, me kike tunani ne, daukar lokacin da muka yi a tare a banza zata tashi ba tare da munyi aure ba?”.
Tace “abinda nafi zargi kenan!”, zanyi magana tayi gaggawar katseni, “ki duba fa, ba fa yau kuke tare dashi ba, amma bai taba tado miki maganar aure ba. Idan ma kin tado sai ya hau miki kame-kame, baki taba zargin ko baya son auren bane?”.

Nayi shiru cikin tunani, ban taba yin wannan tunanin ba. Nafi kyautata zaton ko rashin maganar aure da baya min, baya so ne in hada karatuna da aure, yafi so sai na gama sannan ya fara maganar, don haka ban taba kawo zargin wani abu ba. Don haka na girgiza kaina kawai.

Tace “ko ma menene, ki godewa Allah daya nuna miki hakan tun kafin zance yayi nisa. Samari irin su Umar su kan yi iyaka bakin kokarinsu wajen ganin sun cimma burinsu akan macen data burge su. Ina tunanin dalilin daya tsayar dashi kenan, ko kuma sun yi tsubbace-tsubbacen da suka saba sun shawo kanshi”.

Na girgiza kai, “babu boka babu malam a cikin wannan lamari, ina tabbatar miki Umar a cikin hankalinshi yake”.
A nutse na warware mata dalilin daya haddasa fadan da muka yi dashi last time, har ma wasu fadan da muka yi akan matsala irin wannan, wanda bata taba jin hakan ba sai yanzu.

Ta kama baki cike da tu’ajjibi, tace “kin gani ko? wato da yaga cewa ta bangarenki babu sa’a, shine ita kuma data kai kanta yace bari ya biye mata. Kila a dabararshi idan ya gama da ita sai ya dawo kanki? Ko kuma wani shiri gare shi na daban?”.

Nayi shiru kawai ina kara juya lamarin a cikin raina. Har yanzu kaina bai gama yayewa ba, mamakin abin bai sakeni ba. Dama ana haka a duniyarmu? Kina sane, kana sane, ku take sanin, ku yaudari kanku ku yaudari wasu? Ina jin labarin snatching da dama, mafi yawa a labarai ko a gidajen radio ko a fina-finai, ban taba zaton yana faruwa da gaske ba, sai gashi yau ya faru a gaban idona, a kaina kuma.

Duk yadda naso in jurewa abin, kasawa nayi. Ji na nayi kawai hawaye na bin fuskata. Janan take ta bubbuga bayana tana bani kalamai masu kwantar da hankali, har naji zuciyata ta dan yi sanyi, amma nasan cewa na dan lokaci ne.

A hankali na mike, jiri yana kwasata, na shiga bayi. Tsaye nayi a gaban babbar mirror dake manne a bangon bandakin ina karewa kaina kallo. Idanuwa sunyi luhu-luhu, sun kuma yi jawur, daga ganina babu tambaya kasan kuka na gama shaka. Ko yanzun ma wasu hawayen ne suka ciko min idanu. Me na yiwa Umar a duniya dana cancanki wannan yaudarar daga gareshi? Ko kuwa Haleemo zan ce? Shin wai, ta yaya ma har suka hadu suka kulla wannan cin amana? Tun yaushe kuma??

Wato dai kaji tsoron dan Adam. Kuma kaji tsoron mutane masu halin shiru-shiru, sai yanzu nake gane gaskiyar Jan da tace halinta yafi na sauran muni. Lallai na ga misali akan kaina.
Na ciza lebena na kasa ina danne kwallar data ciko min ido. Ba zan kara zubda hawaye akan su ba, they are not worth it!. Na wanke fuskata kawai na daura alwala na fita. Katifa kawai na hau na kwanta, na ji wayata tana kara da vibrating, ina dagawa naga Umar ne yake kiran. Na jinjina kai kawai cikin rashin abin cewa, lallai rashin ta ido irin ta dan mutum tayi yawa. Wayar na dauka kawai na kashe nayi jifa da ita can bayan katifar, na sake komawa na kwanta.
Janan duk yadda taso ta ja ni da hira, kasawa nayi. Haka nan ta hakura tayi shiru. Har barci ya dauketa idanuna biyu, ina ta saka da warwara har barcin ya daukeni nima.

Washegari haka na tashi da matsanancin zazzabi da ciwon kai a jikina. Da kyar na iya yin sallar asuba, na koma na kara kwanciya na kawo bargo mai nauyi na rufawa jikina, amma hakan bai hana ni rawar sanyi ba. Har wajen karfe takwas na safe ina cikin wannan hali.
Janan tana zaune a gefena tana kallona cike da alamun damuwa rubuce a fuskarta, tun da asubahin take bin kaina akan in shirya mu tafi asibiti, amma na ki tashi. Yanzun ma abinda take ta fama dani kenan, “don Allah ki tashi Na’ilah, jikin ki kara rikicewa yake yi”. Ta fada cikin alamun lallashi da kuma roko, kai kawai na girgiza mata alamun a’ah, na kara jan bargo na rufa.

Ta kura min idanu, akwai alamun takaici da kurar da ita da nake yi rubuce baro-baro akan fuskarta. Tace “shikenan, kiyi duk abinda kika ga dama, an fada miki na damu ne?”.

Ta ga dai bani da alamun motsawa, sai ta kara matsowa kusa dani, cikin sanyin murya, cike kuma da nuna tausayi tace “haba Na’ilah! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, amma ki kasa yarda da abinda Allah ya tsaro miki? Akan namiji! Haba Na’ilah!! Akan namiji zaki zauna ki kashe kanki? In fada miki gaskiya? A banza zaki kashe kanki idan ma haka ne, mantawa zai yi dake, dama can bai daukeki a bakin komi ba. Yanzu haka ma kila ya riga da ya manta dake, kila yanzu haka suna can suna kwasar soyayyarsu babu abinda ya dame su yayin da ke kina nan kin saka bakin cikinsu a cikin ranki, kina nema ki kashe kanki a banza!”.

Na samu na girgiza kaina da kyar, murya na fita da kyar, ina ganinta dishi-dishi, nace “ba akan Umar bane!”.
Ta fusata, “to akan waye idan ba shi ba? Ke karamar yarinya ce da za a dinga bin kanki akan rashin lafiyarki wai? Idan kina so in yarda ki taso mu tafi asibiti yanzun nan!”.
Nace “mura ce kawai ba wani abu ba, zuwa anjima zai sauka, ki daina damuwa”.
Ta hau girgiza kai, “wannan kafar kai taki ban san irinta ba wallahi, Allah ya kyauta miki!”.
Na lumshe idanuna kawai saboda yadda nake jin sunyi min nauyi. Janan kuma ta saka ni a gaba tana kallo. Wani wahalallen barci ya daukeni kenan, naji alamun taba kofa alamun an fita. Ba’a jima ba aka sake bude kofar aka dawo.

Jin tashin murya ba daya a dakin ba yasa na bude idanuna da kyar.
Yaya Bilal ya kalleni fuska babu yabo ba fallasa, sai dai can cikin kwayar idanunshi, akwai wata kwantacciyar damuwa dana tabbatar ba rashin lafiya ta bace ta haifar da ita ba. Wannan, ko kuma dai idanuna ne suke min gizo kawai.

Ya dauke kallonshi daga kaina ya maida kan Janan dake tsaye a gefenshi, “me ya sameta?”.
Tace “zazzabi ne da ciwon kai, tun jiya da dare, amma bata son mu je asibiti. Kuma zazzabin karuwa ma yake yi maimakon ya ragu”.
Ya sake maida kallonshi kaina, duk da halin da nake ciki kasa daukar kallon shi nayi. Wasu irin sakonni ne suke fita daga cikin idanun nashi, bana tunanin shi kanshi ya san suna fita. Ga… Dan saurara! Wasu irin sakonni nake nufi? Anya kaina bai fara motsi ba kuwa? Ni wacece din shi da zan ce yana turo min sakonni ta idanunshi? Wow! Dama naji ance zafin zazzabi yana sa mutum ya dinga sambatu kila ma har da ganin hallucinations. Babu mamaki abinda nake gani kenan nima yanzu.

Maganar da Yaya yake yi ce ta dawo dani daga rants din da nake zabgawa a cikin kaina, yace “bari in kira Dr. Zubair in gani, Allah yasa yana kusa”. Ya juya ya fita daga dakin wayarshi a hannu yana dannawa. Janan kuma ta dawo gefena ta zauna, hannu ta kai tana daga goshina zuwa wuyana, ni kaina nasan ba karamin zafi jikina ya dauka ba, har wani tiririn zafi nake ji a jikina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button