A ZATO NA COMPLETE

Ba ayi cikakkun mintuna goma da fitar Yaya ba sai gashi ya dawo. Yace “bismillah dakta, shigo”.
Janan ta tashi da sauri ta dauki gyale ta dora akan kayan barcinta. Ni kuwa dama kayan barcin dana saka doguwar rigar cotton ce mai dan gajeren hannu wanda ya tsaya min a damtsen hannu.
Yaya ya fara shigowa dakin, wanda nake zaton shine likitan daya kira ya biyo bayanshi. Ya ajiye dan karamin akwatin daya shigo dashi, ya bude ya fara ciro abubuwan gwaji da sauransu. Yana fiddo komi ya fara aikinshi.
Cikin awa daya sai gani manne da drip a hannu, da tulin magungunan malaria, har ma da typhoid.
F.W.A
☆⋆16⋆☆
Ana sa min ruwan barci mai nauyi ya daukeni. Lokacin dana motsa har an cire ruwan, da alamun rana tayi sosai ko kuma ma lokacin azzuhur yayi saboda Janan dana hango akan abin sallah.
Jikina yayi karfi sosai fiye da lokacin dana tashi dazu da safe, na lallaba na tashi zaune. Cikin ikon Allah babu jirin da nake ji da kuma ciwon kan. Janan da taji motsina ta juyo, murmushi ta saki a hankali, “har kin tashi?”. Na gyada mata kai.
Ta tashi ta matso inda nake, “sannu, zaki iya tashi tsaye ko sai na kama ki?”.
Nace “zan iya, jikina yayi karfi yanzu”.
Tayi dan murmushi, “well, ai dole. Ruwa da kika sha!”. Na murmusa kawai ina girgiza kai. A hankali na mike tsaye, karfin jikin nawa ba sosai bane, haka nan na lallaba na shiga bandaki. Sai da nayi wankan ne ma naji jikina ya danyi karfi ma, nayi brush tare da dauro alwala na fito. Janan bata dakin, na zauna na shafa mai tare da bude wardrobe dinta na ciro wata buba ta wani jan yadi mai taushi na saka. Da yake haka na taho shekaranjiya zikal dina, kayanta nake amfani dasu. Don ma yanayin jikinta da nawa kusan daya ne, abinda zan nuna mata kawai cikar kirji, amma bayan haka babu wani bambanci mai yawa a tsakaninmu.
Na shimfida abin sallah na tayar da sallah, bayan nayi na jero nafilfili, na zauna ina jan casbaha. Janan ta shigo dakin, na bita da kallo tana ajiye wani babban flask, fita ta sake yi ta dawo da gorar ruwa da faranti da cokali. Sai data ajiye sannan ta kalleni, “taso ki ci abinci, ki sha magani”.
Sai da tayi maganar abinci sannan naji cikina yana juyawa, ba musu na tashi na cire hijabin jikina na ninke ta da abin sallar. Tun kafin in zauna kamshin kifi ya cika min hanci, naji yawun bakina ya guda. A kasa na zauna muna fuskantar juna, ta turo min plate cike da faten doya. Anyi garnishing dinshi da green beans, peas, alayyahu, hanta da aka yanka kanana, ga kifi da dafaffen kwai a gefe. Ina yin loma daya na lumshe idanuna, kai na hau girgizawa, “ramgwadi! Gaskiya yau ba karamin baje basira kika yi wajen girkin nan ba, meye sirrin?”.
Ta kalleni, “ke yanzu nace miki ni na dafa wannan abincin yarda zaki yi? Yanzu na amsa shi wajen Anty Sarah”.
Na bude baki cikin mamaki, watakila lokacin da yan kirki suke kan Anty Sarah bamu taba sa’ar cin karo dasu ba sai a wannan lokacin. Iyaka sanina da ita, wannan baya daga cikin halayen dana santa dashi. Amma zata iya yiwuwa dama can hakan take, kila sanin hakan ne bamu taba yi ba.
Nace “ta kyauta sosai, nagode”.
Ta kai cokali daya bakinta, “ta shigo ne taga yanayin jikina fa sai ta ganki da drip a hannu. Dazu kuma sai ta turo Mimah tace in je in amsar mana abinci”. Na gyada mata kai. Har muka gama cin abincin babu wanda ya sake yin magana. Bayan mun gama, Janan ta kauda kayan can gefe, ta dauko magungunan ta fara balla tana miko min. Da kyar na iya watsa su a baki na hadiye. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa naki tashi dazu da safe zuwa asibiti yana nufin allura da magunguna, ni kuma bana son allura da magunguna.
Janan ta harareni lokacin dana hadiye kwayar maganin karshe da kyar, na fara kakari. Tace “dazu ai da ana tsira miki allura a jiki ko a jikinki”.
Nace “kema kin san saboda bana cikin hankalin kaina ne, amma ina ji ina gani in zauna a tsira min allura? hauka nake?”.
Ta kwashe da dariya, na harareta, “muguwa kawai!”. Gwalo ta min kamar wata karamar yarinya.
Tashi tayi ta dauki kwanukan ta fita. Na lallaba na lalubo wayata daga bayan katifa inda na jefata jiya. Nasan anyi ta nemana babu kakkautawa, musamman ma Muhammad. Na kunna wayar na tsaya tayi loading kafin na bude ta, nayi gaskiya kuwa. Sakonni daga Muhammad sun fi cikin kwando, tambayarshi daya, lafiya? Na hade fuska lokacin dana kula daga cikin sakonnin akwai na Umar, ko kara kallonsu ban yi ba na goge su gabadaya. Na tafi dungurungum nayi blocking dinshi daga wayata.
Komawa nayi daya bayan daya ina karanta sakonnin shi. Duk karantawar da zan yi, zuciyata kara narkewa take yi cike da begen shi, Allah ya sani, a kullum kaunar bawan Allahn nan kara yado take yi a sassan zuciyata. Ban sani hakan ko abu mai kyau bane ko kuma akasinsa. Kafin in gama karantawa jikina yayi wani irin sanyi, daga cikin kalaman shi kawai, babu tantama zaka karanci tsananin kulawa, tsantsar so, da kauna mara iyaka a cikinsu. Jikina yayi sanyi saboda babu mahalukin daya taba nuna min kwatankwacin irin wannan so, kauna da kulawar da wannan bawan Allahn yake nuna min. A duniya yanzu waye yake damuwa kawai don ya kira wayar wani daga dare zuwa safe ya ji a kashe? Sai Muhammad. Sai daya kai ga tambayar ko dai wani laifi yayi min ne, a cikin sakon. Ina gama karanta shi na lalubo lambar shi na danna kira, ban ma san me zan ce mishi ba. Sai dai cewa aka yi line busy, alamun yana waya. Don haka naci gaba da karanta sauran sakonninshi, nasan idan yaga missed call dina zai kira.
Janan ta dawo dakin da waya a kunnenta, daga yanayin yadda take maganar da Yaya Bilal take wayar. Hankalina yana kan sakonnin M.B da nake ta nanatawa, kamar wani karatu. Don haka sama-sama nake jin muryarta a kaina. Bayan ta gama ta zauna a gefena, tace “Yaya ne ya kira yana tambayar ko kin tashi nace eh. Yana Funtua shi da Anty Ameerah, wai ya kaita wajen sunan kawarta,” ta fada tana tabe baki, ni kuma na dan murmusa saboda yadda ta bani dariya, “yace a duba ki da jiki dai kafin ya dawo”.
Nace “babu komi wallahi, ai na warware”.
Tace “yauwa, na ma tuna! Ummah tace tana so ta duba ki itama”. Ta ciro wayarta ta kirata, bayan sun gaisa sun yi yar hira, Janan ta miko min wayar na amsa, na gaisheta cike da girmamawa kamar tana gabana. Tace “Janan dai ta goga miki, daga zuwa jinya sai kema ki buge da jinya?”, ni da Janan muka yi dariya sosai. Mun jima muna hira da ita, Ummahn su Janan ta iya bi da mutum cikin sanyin kalami kaji ka saki da ita, akwai lokuta da dama da zamu fara hira da ita cikin dari-dari ko rashin sakin jiki, amma cikin dan kankanin lokaci zan ji na saki da ita sosai, inji na hau hira da ita sosai. Wasu lokutan sai daga baya zan zauna ina mamakin hakan. Munyi sallama da ita tana ta zuba mana addu’o’i kamar yadda ta saba, na kashe wayar na mikawa Janan.
Kwanciya tayi rigingine tana kallon ceiling din dakin, ni kuma na lalubo game din candy crush a wayata ina bugawa. Shiru ya ratsa dakin na dan wani lokaci, can naji tace “Nan da sati biyu Yaya zai tafi umarah shima”.
Na kalleta cikin mamakin dalilin da yasa ta fada min, nace “and?”.
Ta kalleni tana wani yin kasa-kasa da idanu, “don Allah kizo ki taya ni zama kafin ya dawo!”.
Na zaro ido, “wa? Ni?? Ki rufa min asiri in mutu maza su kaini ba mata ba! Ana zaman lafiya, da hankalin kaina, anya kina ma so na kuwa?”.
Ta harareni, “yo meye na wani zaro ido? Wuta nace ki zo ki taya ni zama?”.
Na koma na kwanta ina dariya, “lallai ma, zama a gidan nan naku ai sai wanda ya shirya, ni kuma ban shirya ba. Jira nake goben nan tayi, idan na cira kafa na bar nan gidan sai kuma baba ya gani. Idan da son rai na ne ma, har in bar Zaria ba zan kara zuwa nan ba!”.