A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Tace “inaa, kema kin san wasa kike yi coz you are stuck with me babe, babu yadda zaki yi dani. Sannan gobe babu inda zamu je sai jikinki ya kara yin kwari sannan, maybe zuwa talata?”.
Na kalleta ina dan murmushi cike da jindadi, “babu wani hutu da nake bukata don ni nan garas nake ji na, amma kuma wa zai ki hutu koda na kwana daya ne musamman daga wannan asibitin?”. Itama tayi murmushi.

Karan da wayata tayi ne yasa na kalli hannuna duk da kida na musamman ne, na riga nasan mai kiran. Na turo baki cikin shagwaba, ban san dalili ba, duk lokacin da nake tare da Muhammad, na kan ji ni kamar wata yarinya karama, kamar wata sabuwar halitta.
Cikin shagwabar na daga, yana ta magana nayi shiru, yace “haba baby na, come on, talk to me mana. Nayi laifi ko? Am sorry!”. Nayi shiru ina jinshi ya cigaba da cewa “haba baby na, baki so in ji daddadar muryar nan taki ne? Come on…”.

Na turo baki kamar yana gabana, “ba kai bane ka ki daga wayata dazu ba?”.
Ya saki murmushi mai sauti, “tuba nake gimbiyata, ina amsa wata waya mai muhimmanci ne. And you are the one to talk, idan maganar gaskiya ake yi ai nine ma yakamata ace nayi fushi. Na ga tun jiya nake kiran wayarki a kashe. Baki ji warin kunar da zuciyata ta dinga yi bane?!”.

Ban san lokacin dana kwashe da dariya ba, nace “oohh, da gaske?”.
Yace “sosai ma, da yadda nayi ta kiran sunanki. Duk baki ji ba?”.
Na sake yin wata dariyar ina girgiza kai cikin wani irin matsanancin farinciki, nace “ban ji ba gaskiya!”.
Yace “nayi tunanin gabadaya mutanen Zaria sun ji!”. Na cigaba da kyalkyala mishi dariya.

Mun jima sosai muna kwasar hirar soyayyarmu, har na rasa tracing din lokaci. Lokacin da muka yi sallama dashi, bakinshi yana furta I miss you’s da I love you’s. Zuciyata fara kal, kamar farar takarda.
Janan da tunda na fara wayar take kallona baki a dage, ta kalleni tana murmushi, “anyi nisa a lambun soyayya!!”.
Nayi dariya ina birgima a tsakiyar dakin, “baki san komi ba Jan… You’ve no idea. Ya Allah, I love that man!!”.
Dariya ta saki, ta taso ta rungume ni, ban san dalili ba, amma nima rungumeta din nayi. Tace “na taya ki murna, dear. Congratulations!”. Nayi murmushi.

F.W.A

☆⋆17⋆☆

Yinin ranar a daki muka yi shi. Bayan munyi sallar la’asar, Janan ta kunna mana film din X-Men a wayarta muka fara shi tun daga farko. Babu abinda ya dinga tada mu sai sallah da cin abinci.

Bayan isha’i, Janan ta tado ni muka fita waje, a cewarta kafa zamu dan wasa musamman ni da babu inda na fita tun yau. Ban damu ba, na dauki hijabi ta na saka muka tafi. Garin tun da yamma tayi yayi alamun hadari, ga wani irin zafi da aka yi kamar zai kona mutane. Sai dai zuwa yanzu ya dan yi sanyi, iska mai sanyi yake bugawa a hankali.
Muka taka ni da ita har bayan layin su, can wajen irin masu suyar wara da doya da fulawa dinnan don Janan tace abinda take son ci kenan yanzu.
Matar inyamura ce, sana’ar hannu take yi tun karfinta, safe, rana, dare, babu hutu balle kakkautawa. Shi yasa wajenta kullum cike yake da kwastomomi da kuma ma’aikatan da suke kama mata aiki.
Saboda yawan mutane yasa bamu samu mun siya da wuri ba, lokacin da muka tsaya a gabanta, ta kallemu cikin murmushi. Ba laifi mun dan saba da ita, saboda a yawancin lokuta a wajenta muke sayen buns da eggroll da rana. Ta kalli Janan tace “kwana biyu kun dauke mana kafa!”.
Ni da Janan murmushi kawai muka yi muka gaisa da ita. Ta kulla mana wanda muka saya a cikin leda, muka amsa muka mata sallama muka juya.

Cikin rashin sa’a kafin mu karasa gida ruwan sama ya sauka mai karfi, muka daga kafa cikin sassarfa muka kara sauri. Duk da haka kafin mu karasa gida, jikinmu ya jike sharkaf! Har digar ruwa muke yi. Da sauri muka karasa cikin falo, a dan corridor dinsu kafin a shiga falo muka tsaya domin mu dan kafe kada mu bata musu carpet din falo da lema.
Muna tsaye anan sai karan turo kofa muka ji, muka juya muna kallon Yaya daya shigo shima yana linke umbrella din daya shigo da ita. Muka zaro idanu mu duka a tsorace muna kallonshi, nayi zaton a gidan Anty Ameerah yake yau, ko kuwa ba acan yake ba? Aka fara kallon-kallo tsakaninmu dashi.
Ba Janan kadai ba, ni kaina sai da naji zuciyata tana tseren tashin hankali.

Ya hade fuska kamar yaga wasu mala’ikun daukar rai, “daga ina kuke?!”. Ya tambaya murya a cune.
Janan ta fara kokarin ja da baya a tsorace, cikin in’ina ta fara cewa “um… nan.. ne baya!”.
Ya daga murya, “ina ne nan bayan exactly?! Ba na hana ki fita waje da dare ba? Ban da rashin hankali kawai sai ku kama kafa ku fita daga gida da dare babu tunanin komi, kuna ganin hadari kuma! Ku duba yanda ruwa yazo ya muku duka, musamman ke da kike rashin lafiya! Karatun da kuke yi kenan dama? Idan fa jikin ki ya kara rikicewa?”. Ya maido tambayar kaina. Na dan yi tsalle a tsorace, na koma bayan Janan na lafe kamar ita zata kare ni daga fadan shi.

Allah ne ya bata kwarin gwiwar iya daga baki don ni gabadaya jikina rawa yake yi, tace “kayi hakuri Yaya, abinci muka fita muka sayo”.
Yace “abincin waje a gidana? An hana ku dafa abincin ne? Waye ya hana ku?!”.
Janan tayi saurin girgiza kai, “babu ko daya wallahi, kawai mun ji marmarin awara ne, shine muka fita muka sayo. Bamu yi zaton ruwan zai same mu a hanya bane amma kayi hakuri…”.
Ya dan sauke ajiyar zuciya alamun ya dan sauko, yace “to shikenan, amma kada ku kara”. Muka hau gyada kawuna kamar wasu kadangaru.
Yace “to ku wuce kuje ku canza kaya kafin wani abin ya kama ku”. Bamu jira ya sake cewa komi ba, muka bar wajen a sukwane.

Sai da muka shiga daki muka maida kofar muka rufe, sannan muka sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya, kafin muka kalli juna muka kwashe da dariya.
Bayan mun canza kayan jikinmu, mun shanya wadanda muka cire, muka cigaba da kallonmu muna cin awarar.

*

Washegari bamu tashi da wuri ba saboda mun san cewa ba asibiti zamu je ba. Da muka yi sallar asuba, Janan ta wa wata sister Mairo matron dinmu text akan cewa ba zamu samu damar shigowa ba saboda rashin lafiya, bayan ta turo mata da amsa akan babu damuwa Allah ya bamu lafiya, muka koma gefe muna dariya kafin muka koma barci. Sai wajen karfe tara na safe muka tashi. Janan ta fita kicin zata dora mana abinda zamu ci, ni kuma nayi amfani da wannan damar na shiga bandaki na watsa ruwa.

Kafin in fito ta dafo mana indomie, muka zauna muka ci ta sake daukar kayan ta fita dasu. Ta dawo ta zauna a kusa dani ina duba wasu textbooks dinta, zuwa yanzu naji na warware sosai, kamar ban taba yin wata rashin lafiya ba, amma duk da haka sai da Janan ta takura min ba sha magani.
Tace “ki zo muje ki taya ni in yiwa Yaya doughnut da cin-cin don Allah”.
Nace “nayi zaton ya tafi?”.
Ta girgiza kai, “sai gobe. Abin azumin da za’a fara gobe, yana can babban gida, jiya da yau yayi rabon azumi”.

Na ajiye textbook din ina kallonta, “amma banda abinki Jan, saboda Allah me zai yi da doughnut da cin-cin da azumi?”.
Tace “ya dinga sahur ko shan ruwa mana!”.
Na fashe da dariya ina girgiza kai, “gaskiya Ummah tana da sauran aiki a gabanta wallahi, haka zaki yi aure kije ki dinga soyawa miji cin-cin da azumi?”.
Ta mintsileni a gefen cinya tana dariya, “bana son iskanci wallahi, zaki taya ni ne ko yaya?”.
Na mike ina laluben abinda zan sakaya jikina dashi, “kin san ni bana wuce tayin kayan zaki dangin fulawa”. Muka fita daga dakin muna dariya bayan na dauki karamar hijabi data tsaya a ruwan cikina na sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button