A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ina zaune a gefen gadonta, na dinga jiyo karar sautin kida tana tashi. Na kalleta, tana tsaye a gaban wardrobe tana nema mana kaya masu saukin nauyi da zamu saka.
Nace “wannan karar fa, daga ina take fitowa haka?”.

Ta dan juyo ta kalleni, kafin ta maida kanta cikin closet din. “babu mamaki su Haleemo ne suke kallo!”.

Na dafe baki, “wai dama yaran nan suna nan har yanzu?”.
Tayi yar dariya, wadda take lullube da zallan takaici, “to dama ina zasu je? Ai suna nan a gidan nan, basu da ranar fita!”.

Ta miko min Skirt dogo na wani yadi tare da riga, na amsa na fara zare kayan jikina, nace “to Allah Ya kara rufa mana asiri!”.
Tace “ameen”.

Ni tunda nake ganin gidan aure da cakudewar rayuwar aure, ban taba ganin irin wadda ta kama kafar ta gidan Yaya Bilal ba.

An saba idan aka yi aure, akai amarya ita daya zikal dinta gidan miji. Sai dai ita wannan abun nata ya bambanta. Koda aka kai amarya, sai kannenta guda biyu suka samu waje suka share, suka mike kafafu a gidan. Marry one, get two free kenan!.

Watanni bakwai da kai amarya, Babbar kawar amaryar ta kaso aurenta, itama taje tabi layin jerin yan’uwanta dake gidan kamar wadda bata da gidan zama. Yanzu dai su ukun duka suna zaune a karkashin kulawar Yaya Bilal ne. Amma yar kanwarsa daya tilo dake zaune dasu, sun kasa riketa balle su kula da ita.

Kullum fata da buri nasu ta bar gidan, bin malamai, asiri, kissa da kisisina, babu wadda basa yi. Allah ne kadai yake kareta a gidan nan.

Tana gama sallatar azuhur, ta ja ni muka shiga kicin domin mu nemi abinda zamu saka a cikinmu. Muna cikin girkin Yaya Bilal ya shigo kicin din, ya amsa gaisuwar da muka mishi a kaikaice.
Ya kalli Janan yana wani cin magani, “ke ina Raheema take ne?”.
A hankali kamar mai tsoron magana, tace “yanzu muma muka dawo, bamu sameta a gidan ba”.
Bai kara cewa komi ba, ya fita daga kicin din. Ko me yake faruwa kuma yanzu? Na saba ganin kallon so da kulawa daga gareshi zuwa ga yar kanwar tashi, yau kuma naga wani abu daban.
Na kalli Janan dake kokarin hadiye kwallar data cika mata ido, cike da tausayi. Haka Allah ya halicceta mai sanyin hali, da sanyin zuciya.

Danwaken fulawa muka kwaba, daidai wanda zai dauki cikin mutum biyu. Duk kokarin da tayi na mu kara yawan fulawar, ki nayi. Saboda nasan saboda wannan lalatattun yaran take so muyi da yawa. Ni kuwa da in dafa abinci da hannuna, kattin banza su cinye, su goge hannu da tissue su kara mike kafa, karshe ni ce zan kwashe kwanukan da suka ci abincin ma, na gwammace in zauna da yunwa.

Muna gamawa, muka juye shi a cikin kula tare da gyara kicin din tsaf, kamar babu abinda aka yi. Janan ta wuce mana da kular daki, ni kuma na dauki plates da vegetables din da muka yanka nima na fita dasu.

A bakin kofar kicin muka ci karo da Salama, kanwar Anty Raheemah. Duk cikin kannenta babu wadda ta fita rashin da’a da rashin mutunci, shi yasa jininmu bai hadu ba, sam.
Ta wani tsaya kerere, ta kama kugu tare da kara babakewa akan hanya. Ko tayi zaton zagayeta zanyi in wuce? Na saki wani murmushin mugunta. Lallai yarinya har yau baki gama sani na ba.
Na tunkareta gadan-gadan. Da dai taga ina shirin bangajeta, sai taja baya. Na ja dan siririn tsaki a cikin raina, ina raya ‘dama kin tsaya kin ga karshen wulakanci!’.

Ta wani daga murya, “ina namu abincin?”.
Na kuwa tsaya cak, na juya na kalleta, “ban gane naku abincin ba? Kin daukeni aikatau din yi miki girki ne dama ban sani ba?”.

Tayi gyatsine, “taya za ayi ki shigo har cikin gidan Yayata, kiyi girki sannan kuma ki k’i ajiye mana?”.

Naji wata dariya na neman subuce min, nace “to sannu hamshakiya! Sarauniya mai girma!! Allah Ya bamu hakuri mu da bamu da gidan Yaya dake aure a gidan mutane, balle muje mu shimfida mulki a inda bai dace ba!. Girki ne, bamu yi daku ba. In kinyi zuciya, ga hanyar kicin nan, ki shiga ki girka wanda yafi wanda muka girka!”.
Na juya na shige daki, tare da maida kofar dakin na rufe. Ina jin sautin maganganu da zage-zagen da take yi. Janan tace “ni dai wallahi da baki biye mata ba!”.

Harara na jefa mata, “ai a haka suke samun damar taka ki kamar wata sakara. Ke dai da kika ga zaki iya, sai kije kiyi tayi. Ni kam, ba zan iya jure rashin kunya irin nasu ba wallahi!”.

Kai kawai ta gyada, don tasan gardama dani ma bata baki ne.

Karfe biyar na mata sallama zan koma makaranta. Zuwa lokacin babu kowa a cikin gidan, muna jin lokacin da suka fita. Daidai bayan tagar dakin Yaya Bilal, na hangi wani abu daya dauke min hankali. Da sauri na kalli Janan, “kai! Kinga kuwa na manta jotter na akan gado, don Allah taimaka ki dauko min ita mana, zan jira ki anan!”.
Babu musu tace “to!”.

Tana bada baya, nayi sauri na karasa wajen. Da sauri na duka tare da yin bismillah, na fara hak’a. Kamar yadda nayi zato, wasu kullin abubuwa naci karo dasu. Da sauri na ciresu, na maida kasar na rufe kamar yadda take.
Ina komawa inda Janan ta barni, sai gata ta dawo. “Ni fa ban ganta ba, ko dai a asibiti kika barta ne?”.

Na daga mata hannun dama ta, “ashe tana hannuna, sha’afa nayi”.
Ta kada idanu, “ke dai shiriritarki tayi yawa wallahi!”.
Muka jera da ita har zuwa inda zan hau bus. Sai da taga na shiga, motar ta tashi, sannan ta juya tana daga min hannu, tare da jaddada min dana isa cikin makaranta, in kira ta.
Dariya kawai nayi na gyada mata kai, wani lokacin haka take, kamar wata overprotective Yaya, ko Uwa.

             *☆⋆02⋆☆*

“Haba Sweety, ni sai ki dinga cewa wai bana sonki saboda Allah! Bayan kin san cewa duk duniya bani da kamar ki!”.
Ya fada daga can daya bangaren na wayar, whinnying kamar wani karamin yaro.

Na kada idanu sama, “To ai kai dinne sai ka dinga wasu irin maganganu da suke saka ni cikin shakku, Umar”. I mean, ta ya mutumin da yake ikirarin saboda Allah yake sonka, kuma ya dinga kokarin dilmiya ka a duniyar ‘sex chat?’. Kullum muka yi waya dashi, da kalar dirty maganganun da zai tare ni dasu, tun ina mishi alkunya, a tunanina zai fahimci zancen ya daina, har na fito baro-baro na fada mishi cewa bana son hakan, amma duk da haka bai fasa ba. Don haka nace mishi naga alamun cewa ba son gaskiya yake yi min ba, akwai abinda ya gani a jikina dai kawai. Nan ma yace ba haka bane, daga nan ya dan rage yin maganganun, note that ‘ragewa’ nace, ba dainawa ba. Ni kuma kullum ya dauko min maganar abinda nake ce mishi kenan.

Yace “to naji, shikenan. Ni dama na kula da cewa ba wani sona kike yi ba, son da nake miki yafi yawa!”.
Nayi murmushi kasa-kasa, da wata ce kam, zai iya samun damar cin galaba a kanta da irin wadannan maganganun har yayi amfani da wannan damar ya samu abinda yake bukata daga gareta, amma banda ni. A tsaye nake kyam! Akan duk wata kalma da na furta, ko abinda na kudurta a cikin raina.

Nace “duk abinda kayi tunani hakan ne, Umar”.
Ina jin dariyar daya saki mai sauti, wadda ta saka ni yin murmushi ba tare dana shirya ba. “Sweety na kenan! Shi yasa nake jin sonki kullum yana kara yaduwa a cikin sassan zuciyata wallahi. Amma yanzu Oga na ya shigo inda muke, zan kira ki anjima in shaa Allah, ok?”.

Na girgiza kai, “babu damuwa ai, sai anjiman”.
Nan muka yi sallama da juna, bayan ya manna min sumba ta jikin wayar. Kai kawai na girgiza, speechless, muka ajiye wayoyinmu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button