A ZATO NA COMPLETE

Sai kuma naga idan ma na koma, ni zan kwari kaina, babu wanda zai ji a jikinsa dai sai ni. Don haka naci gaba da tunani ina laluben mafita. Nasan mafita daya itace in fadawa Yaya, amma gani nake kamar abin yayi yawa. Shi shikenan kullum cikin ji da matsalata, kullum babu hutu?.
Ban tashi daga kwanciyar ba sai da aka kira Sallar azuhur, ashe wani wahalallen barci ne ya daukeni. Wani irin barci mai dauke da wasu irin sarkakkun mafarkai. Na tashi ina mika da hamma, maimakon inji gajiyata ta tafi, sai naji kamar an dauko gajiyar duniya ne an dora min aka. Haka nan na lallaba na watsa ruwa a jikin nawa ya dan min karfi, sannan nazo nayi sallah.
Ina cikin karatu Janan ta kirani. Roko na ta dinga yi akan inje in mata weekend, kai tsaye nace mata a’ah, ta dawo tana magiyar to inje in tayata shan ruwa, nan ma nace a’ah. Ni dai tunda na samu nayi sa’a, Allah ya taimakeni na baro gidan, ai an wuce wurin. Ta gaji tayi fushi ta ajiye wayar. Da yake ba a cikin yanayi mai dadi nake ba, kyaleta nayi kawai.
Yinin ranar haka na yi shi sukuku, can da yamma wai sai ga Maryam, mun gaisa da ita gari-gari, wai in na shiga kasuwa in sayo mata sarka da yan kunne idan ma naga da halin takalmi in karo, naji kamar in hau rusa mata ihu na dai cije nace mata to kawai, na ajiye wayar.
*
Dole kanwar naki haka na dage na kira Yaya zuwa ranar talata, domin duk ta inda na buga abubuwan babu sauki, babu wata mafita. Na zayyane mishi matsalar da muke ciki da Baba, Yayan yayi shiru yana tunani, kafin daga baya yace zai kira shi sai yayi mishi bayani. Na mishi godiya nace to, na kashe wayar.
Allah ya taimakeni cikin satin aka turo mana kudin scholarship da aka saba bamu. Kuka ne kadai banyi ba ranar saboda murna, dama nayi karaf, bani da ko sisi. Haka kayayyakin da suka rage min duk sun tasamma karewa. Yawanci idan aka turo min ina fadawa Baba, amma wannan karon da yake a wuya nake da kowa, babu wanda yaji labari. Kasuwa kawai na fada.
*
Abu wasa-wasa, tun ana yau azumi, har gashi mun zo mun ci tsakiyar shi. Yaya ya samu ya shawo kan Baba da kyar ya turo min kudin, naje na biya. Allah ya taimakeni basu kai ga rufewa ba. Abubuwa zuwa yanzu sun yi min sauki nesa ba kusa ba, ba kamar satin daya gabata ba. Ban bar wannan abin ya dameni ba ko kuma ya hana ni aikata abubuwana na yau da gobe. Allah ya kan jarabci bawanshi ta kowace irin hanya. Zata iya yiwuwa ta kankanin abu, ko babba, ko iyaye, ko ‘ya’ya, ko cuta, ko kuma sauran abubuwa. Na yarda hakan yana daga cikin jarabawata, don haka ban damu ba sosai. Fatana Allah ya bani ikon cinyeta. Nasan watarana idan da rai, hakan zai zamo tamkar ba ayi ba. Don haka nake godewa Allah a kullum, kuma a koyaushe.
Jiya Yaya Bilal ya tafi Umarah shi da Anty Ameerah. Ba’a tafi da Raheemah ba saboda last year da ita aka je a cewar Janan. Bata ji dadin hakan ba, saboda haka sai da suka dan yi rikici da Yayan akan wai yana gwada mata rashin adalci kafin ya tafi. Bayan tafiyar tashi kuma sai abin ya koma kan Janan, tsangawamar yau daban, ta jibi daban. Wai kicin ma suke rufe mata yanzu, bayan da Yayan zai tafi sai daya cika kicin din ya batse shi da duk kayan amfani. Nace ta kira shi a waya ta gaya mishi mana, tace wai bata son ta dinga tada musu zaune tsaye, nace “ai sai kiyi tayi!”.
Kawai sai ganinta nayi da dubu dai-daya har guda goma, wai inji Yaya inyi sayayyar azumi. Abin ya bani mamaki matuka, na karba nayi godiya. Da yake ma hannuna da kudi, cikin wannan satin wata karamar kwangila da Yaya yayi ta fito, cikin kudin da aka samu ne nima ya dan tsakuro min. Na hada su waje guda na ajiye ban tasar musu haikan ba, nasan a hankali a hankali idan na tattala zasu dade min.
Tunda Yaya Bilal yayi tafiyar nan, kusan kullum anan wajena Janan take shan ruwa. Wasu lokutan ma sai mun gama sallar tarawihi sannan take tafiya gida, idan kuma Allah ya taimaketa Is’haq ya shigo ta nan wajajen, sai ya dauketa su tafi.
Kasancewar ba wani dogon hutu zamu yi ba, yasa na yanke shawarar bin Janan Kaduna kawai inyi sallata acan. Don haka na lallaba Maryam ta karban min kayan sallar da aka bani, atamfa da leshi da takalmi kala daya, ta bayar ta motar haya aka kawo min na kai wajen dinki. Tun dai ana saura kwana biyar muyi tafiyar na kira Baba na fada mishi, yace babu laifi.
Shi dama Yaya da yake ya riga yasan Janan, itama wasu lokutan idan muka samu hutu gajere muna zuwa Gashua da ita. Sannan idan Allah yasa yayo ta wajen Zaria ya biyo mu gaisa, suna haduwa da ita. Ya santa sosai har su Ummahn, saboda haka koda na fada mishi acan zanyi sallah cewa yayi hakan ma yafi, tunda yafi kusa. Shima dubu biyar ya turo min wai in samu karamar atamfa in saya in dinka, na mishi godiya sosai kuwa.
Ranar da muka dauki azumi na ashirin da takwas, ranar muka wuce Kaduna. Sallah ta rage kwana biyu ko daya kenan. Itama Ummah a daren ranar zata dawo, yayin da Yaya Bilal kuma sai washegari.
F.W.A
☆⋆19⋆☆
Ranar sallah muka sha kwalliyarmu, da safe muka bi yaran gidan muka je idi. Jiya da dare bamu kwanta da wuri ba saboda hidimar abincin sallah. Mun yi miyar taushe, aka soya nama, kaji, har da su snacks. Da safe da zamu tafi idi muka bar yan aiki suna soya masa ta farar shinkafa. Don haka muna dawowa aka fara rabon abinci, gida-gida.
Ummah mace ce mai mutane sosai, saboda haka yinin ranar mutane ne yara da manya, yan gida ko yan unguwa, suna ta shigi da fici kamar wata hidimar biki ko suna.
Gidansu Janan babban gidane, Alhaji Salisu Makarfi mahaifinsu Janan babban mutum ne kuma dan dangi, tsohon soja ne amma yanzu yayi ritaya. Kafin ya auri Ummah yana da mata wadda ta mutu ta bar manyan ‘ya’ya maza har su hudu, bayan sunyi aure da Ummah kuma ta haifi Janan, daga baya ne ya sake aurar Usaina babar su Harira da suke kira Yaya. Mutum ne shi na mutane, ya kuma rike zumunci sosai, shi yasa iyalanshi suka taso cike da zumunci da kauna ta yan uwantaka, idan kaje gidan baka banbance dan gida dana waje, baka banbance dan daki da dan daki. Yawancin diyan yan uwanshi a gidan suka girma har suka riski lokacin aure wasu kuma tare da nashi diyan suka yi makaranta wanda shi yake biya musu kudin makarantar. Shi yasa kullum baka raba gidan da mutane.
Samarin gidan da suka taso a gidan, ko bayan da suka yi aure, wasu lokutan idan kaje gidan zaka gansu ko a kofar gida, ko kuma a cikin gidan karkashin daya daga cikin bishiyoyin gidan suna hutawa ko suna hira. Da yake babban gidane, akwai part daban da aka ware wanda mazan gidan suke amfani dashi.
Yau ma haka gidan ya wuni, jama’a ta ko’ina musamman yara jikoki.
Muna dakin Ummah da yammacin ranar, yawanci duk kowa ma a dakinta yake. Ummar yara ma suke ce mata, yayin da suke kiran mahaifinsu Baban yara.
Nayi kwalliya cikin leshin da Baba ya bani, Janan kuma atamfa ta saka. Mu kusan biyar ne a dakin, Ni, Janan, Harira da Firdausi diyan Yaya sai wata Umaimah matar Yayansu Haneef. Danta Shamsu yana kan cinyata yana wasa da motar roba ina taya shi, hirarsu suke yi cikin raha, ni kam rabin hankalina yana ga hirar da suke yi, rabi kuma yana kan tunani akan Muhammad. Yace min zasu shiga can cikin wani kauye a Benin field work tun cikin azumi, yace ba lallai mu dinga samun damar yin waya dashi ba, amma fa yana min text kullum. Nayi tunanin zasu samu su fito daga kauyen tunda yau sallah, amma shiru kake ji. Yau ko albarkacin text din nashi ma ban gani ba. Tun safe nake zuba ido akan wayata, da naji tayi kara sai in zabura in wawureta a tunanina shine, sai inga wani ne daban. Wani lokacin har tsaki nake saki a kule.
Na tura mishi text amma shiru ba reply, idan kuma na kira wayarshi sai inji a kashe. Jikina ya fara sanyi. Nayi kewar mutumin nan, ina kan kewarshi. Sati biyu da muka yi bamu waya dashi, ji nake kamar shekaru biyu ne. Ban san cewa nayi mugun sabo dashi ba sai a wannan lokacin.
Janan ta tabo ni, nayi sauri na kalleta, ban san lokacin da Shamsu ya sauka daga jikina ba, sai yanzu na kula da cewa yana hannun mahaifiyarshi yanzu. Ta kalleni cikin nuna damuwa, da baki ta min alamar tambayar “lafiyarki lau kuwa?”.
Nayi saurin girgiza mata kai, alamun babu komi. Nayi kokarin saka bakina cikin hirar da suke yi akan samarin su Harira muna ta kwasar dariya, amma fa lokaci zuwa lokaci idanuna su kan sauka akan wayata cikin fata.