A ZATO NA COMPLETE

Nayi murmushi a dan kunyace nace mishi “you too!”, na kashe wayar da sauri ina dan murmushi. Sai lokacin na kula da yadda garin yayi haske alamun gari ya waye sosai. Allah yasa ina azumi, don haka ban tsaya wani kokarin hada abin kari ba kawai nayi abinda ya kamata na fita da sauri.
*
Wannan karon muna bangaren yara ne. Tunda muka je wani likita, Dr. Habib Na Abba ya sanya min ido kamar yaga wata danyar nama, bibiyata yake tun karfinshi tun cikin azumi. Yanzu ma muna tsaye ni da Janan muna rubutu a register, Janan din ta tabo ni. Na dan daga kai distractedly na kalleta, tace “likitan can fa tunda ya shigo idanuwanshi suna kanki”.
Na daga idanuna a hankali na dubi inda take yi min nuni, aikuwa muka hada ido dashi, na janye nawa da sauri na maida kan littafin gabana ina jan dan siririn tsaki, “na tsani yawan kallo wallahi, haka kawai ka wani saka ni a gaba kana kallo kamar ka samu wata talabijin? mtsww!”, na sake jan wani tsakin.
Tayi yar dariya, “hala har yanzu baku shirya da Muhammadun naki bane? Na jiki yau gabadayanki a wuya kike, kamar wadda take jira a tabota, sai ki hau fada”. Na jefa mata harara ina shirin maida mata amsa daidai da ita, sai naga Dr. Na Abba yana tunkararmu, don haka muka kama baki muka bame kar yaji muna magana a kanshi, har yazo ya tsaya a inda muke muka gaida shi.
Ya ja tunga ya tsaya yana watsawa Janan tambayoyi game da aiki da kuma ward din, duk wannan abin da ake yi idanunshi suna kaina amma. Ji nayi gabadaya na takura, na tsani kallo. Gashi shi kuma yazo ya mana wani kememe bashi da alamun motsawa ma. Don haka na ajiye littafi da biron da nake rubutu dasu, na kalli Janan nace mata “bari in dan fita”, na juya zan bar wajen.
Maganar da yayi ce ta dakatar dani, “haba sister, daga zuwana kuma sai ki tafi sai kace ina korarki? Idan dai saboda nine, yi hakuri ki dawo ki zauna, sai in tafi”.
Na juya ina kallonshi cikin dan murmushin da bai wuce fatar baki ba, nace “ba don kai bane likita, kawai naji ina son fita in dan shaki iska ne”.
Yace “to idan haka ne, muje in raka ki shan iskan mana? Nima wajen na nufa yanzu ai”.
Nace mishi “babu komi likita!”.
Na zagaya kusa dashi muka jera muka fara tafiya. Muna ba Janan baya ya juyo ya kalleni, “to ya sunan malamar?”.
Nace “Na’ilah!”.
Ya maimaita sunan, “Na’ilah! So unique, I like it!”. Nace mishi “nagode”.
Muka cigaba da tafiya yana min kananun hirarraki har muka fita wajen, muka cinye karshen ginin. Ko dai ya fita, ko kuma ya hau sama ko kuma ya koma inda muka fito. Ya tsaya ya ja tunga tare da juyowa ya kalleni hannuwa cikin aljihun fara kal din rigar labcoat daya saka tana ta sheki a cikin ranar da muka tsaya a ciki, ya juyo muna fuskantar juna dashi.
Yace “ni fa son malamar nake, ya za ayi ne?”.
Banyi mamaki ba, don dama nasan ko ba dade ko ba jima sai ya fadi hakan, nace “ni kuma?”.
Ya langwabar da kai gefe, “yanzu duk alamomin da nayi ta jefo miki, kina so kice min baki taba kula ba?”.
Na girgiza kai ina kallonshi, “ko kadan, ta yaya kake so in kula da hakan? I mean, ba tambari bane a goshinka da idan na ganka zan ga hakan kai tsaye ba”.
Ya kyalkyale da dariya, “I like you, kina da ban dariya gaskiya. Ga murmushinki mai kyau”. Na dan saki murmushi kawai.
Yace “nasan ke ba karamar yarinya bace, kin fahimceni tunda ba tun yau kike a cikin ward dinnan ba, amma tunda haka kika ce, zan bi ta hanyoyin daya kamata tuntuni, ko zan iya samun lambar malamar?”.
Na dan girgiza kai ina murmushi, mutumin nan is very charming, da dai ace wani Muhammad bai sace min zuciya ba. Nace “ni fa kayi hakuri likita, an riga anyi mun miji a gida”.
Ya kalleni tun daga sama har kasa yana wani murmushi, “ke din?”. Na gyada mishi kai.
Yace “well then, na makara kenan. Amma shi mutum ai baya cire rai daga rahamar Allah, don haka ba zan saddakar ba tun yanzu…”, ya ciro dan katinshi daga cikin aljihunshi ya miko min, nasa hannu na karba, ya cigaba da magana, “ina fata zamu cigaba da gaisawa haka nan, don maganar gaskiya kina burgeni sosai. Ina fata zaki taimaka min da lambar wayarki?”. Wannan babu musu na karbi wayarshi na zuba mishi lambobina, ya karba yayi saving. Ya dago ya kalleni da dan siririn murmushi akan siraran fatar lebenshi, “sai kin ji daga gareni dear, thank you”, ya kanne ido daya tare da juyawa abinshi ya tafi. Na bishi da kallo, yar karamar dariya na subuce min, na girgiza kai kawai.
Ban yi cikakken minti biyar ba na juya na koma, Janan ta kalleni tana wani murmushi tunda na shiga har na je kusa da ita, na ja kujera na zauna ina kallonta a daddage. Tace “meye kike wani hade fuska? Tambaya ce sai na miki ita, you and the doc?”.
Na kwantar da kaina akan benci, “ni fa babu abinda yake tsakaninmu, ke da kika san komi, ina zan kai Muhammadu na kuma?”.
Tayi murmushi, “ke da Muhammadun nan naki, Allah dai ya mana zabi nagari. Zaki shiga makaranta gobe, ko kuma zaki raka ni ne?”.
Nace “zan raka ki dai kawai, ka samu dan hutu daga wannan wahalar”. Ta kwashe da dariya, “daga dawowa har kin gaji?”.
Na maida kaina na kwantar kawai.
*
Wajen karfe goma muka shiga cikin makaranta washegari bayan mun dauko excuse, da yake akwai sauran abokanmu dake cikin hostels din makarantar, Janan ta wuce department wajen supervisor dinta, ni kuma na shiga cikin makaranta da niyar idan ta gama dashi zata kira ni sai mu hadu da ita a gate mu koma asibitin. Ni sai gobe zan ga nawa supervisor din.
Dakin wata kawata Fatima da muka yi mutunci da ita naje sai aka ce min ai tana sick bay ma bata da lafiya, don haka na karkata na tafi wajenta. Na dan jima a wajenta muna hira da yake jikin nata da sauki, har ma ana za’a sallameta anjima. Janan ta kira ni tace min ta gama yanzu zata fito daga department, don haka na yiwa Fatima sallama da fatan karin sauki, na fita.
A daidai bakin gate naga Yaya Jameel sun shigo shi da Anty Sarah, abin ya bani mamaki da naga ciki a jikinta, dama ciki gareta? Suka wuce ni a mota ni kuma na wuce na fita. Sai dana ganta ne ma sannan na tuno cikin Sailuba itama, nasan cikinta ya tsufa yanzu, haihuwa ko yau ko gobe.
Akan hanya na kirata nake tambayarta, tace ai tana ma cikin asibiti, suna expecting din baby nan da sati daya. Nan muka yi sallama da ita muka kashe wayar.
A bakin gate muka hadu da Janan, muka jera muka fita daga cikin makarantar. Cikin asibiti zamu koma gabadayanmu. Nace mata “baki fada min Anty Sarah tana da ciki ba”.
Tace “a ina kika gansu ne? Ashe baki kula da cikinta ba, kodayake last zuwan da kika yi baki ganta ba sosai, amma naji suna cewa ya jima ai”.
Nace “a sick bay na gansu, naga ma kamar irin dadadden nan”.
Tace “kinsan dogayen mutane dama, yanzu haka idan ba ido kika sanya mata ba, ba lallai ki gane tana dauke da ciki ba”.
Na gyada kai, nace “haka ne, Allah ya raba lafiya”. Tace “ameen”.
Muka samu bus muka hau, tunda muka hau babu wanda yayi magana a cikinmu, da alamu kowa da tunanin da yake damunshi. Ni yawanci akan yadda zan karke rayuwata a gida ne idan na koma kafin inga yadda Allah zai yi dani, ko mai zai faru? Ita kuma Janan ban sani ba, har muka sauka daga bus din dai muka shiga cikin asibitin. Sai da muka fara tunkarar ginin asibitin sannan ta kalleni, murya cike da damuwa tace “ko yaushe matan Yaya Bilal zasu haihu ne?”.
Nace mata “ita haihuwa ai ta Allah ce, idan ya nufa sai kiga an sameta ba zato babu tsammani”.