A ZATO NA COMPLETE

Tace “haka ne, amma ina tausaya mishi wallahi. Shekaru suna ja suna kara wucewa, yakamata ace kamar yanzu dai ya fara ajiye nashi iyalin, kowa a cikin dangi ma abinda yake fada kenan”.
Nayi shiru ina jinta, ni kaina wasu lokutan ina wannan tunanika, sai dai mafiya yawanci ban san akan wani tunani zan tsaya ba. Tsakanin Yaya da matanshi ban san waye bai haihuwa ba zata kuma iya yiwuwa wata kaddara ce daga Allah. Don haka na dafa kafadarta, nace “kada ki damu, in Allah ya yarda Allah zai kawo masu albarka”.
Tace “Allah ya yarda”. Muka cigaba da tafiya ba tare da mun sake yin magana ba har muka shige cikin ward din.
Ko bayan da muka tashi dakina muka wuce da ita, na mana danwake da yake Janan tana matukar son shi, ina cikin yin danwaken ita kuma tana gefe tana yanka mana cocumber, tumatiri da dafaffen kwai Esther kuma tana gefenmu tana taya mu hira, har na gama muka zauna muka fara ci bayan mun zambada yaji kamar na kamun mayu. Bayan mun gama ci muka sauka kasa ni da ita muka wanke kayan muka dauro alwala daga can muka dawo daki muka yi sallah. Tana sallame sallah wayarta ta dauki ruri kamar dama jiranta ake yi, ta daga wayar tayi murmushi tare da nuno min, sunan Yaya Bilal ne yake ta tsalle akan screen din wayar, na taya ta murmushi cike da mugunta.
Ta daga wayar a ladabce tana wani yin kasa-kasa da kai da kuma murya, hakuri kawai naji tana badawa, daga karshe dai ta kashe wayar tare da mikewa tsaye, ko babu tambaya nasan tafiya zata yi don haka nima na dauki hijabina na saka na bita a baya. Kamar kullum, sai dana rakata ta hau bus sannan na juyo na dawo hostel.
Ina dawowa sallah nayi na, dana gama na koma kan katifa na zauna tare da dauko littafaina ina kara reviewing takardun da zan kaiwa supervisor dina gobe, dana gama kuma na dauko textbooks ina kara karatun exams din da zamu yi sati mai zuwa. Har wajen karfe goma tayi Muhammad ya kira ni, na hada kan littafan na ajiye na amshi wayar.
*
Washegari sai da rana Mr. Akafyi ya min waya akan inje in sameshi, don haka na tafi makaranta. Bayan ya dudduba takarduna da sauran gyare-gyaren da zai min, yace inje inyi printing din wata chapter, na sauka kasa da sauri nayi, ina tsaye mutumin yayi da yake babu yawa kuma babu layin mutane, ya gama na biyashi na koma na kai mishi. Abin haushi da takaici, ina kai mishi yace ai ba wannan chapter din yace ba, wata ce daban, meaning na bata lokacina da kudina a banza. Tun farko kuma shi yace ba sai na dinga printing ba, kawai in dinga rubutawa ina kai mishi, gashi yanzu yana kokarin janyo min ciwon kai ta dalilin haka.
Nan na sake sauka kasa na bashi takardun, kusan zaman awa daya nayi a wajen yana aikin typing, ya gama ya miko min. Ina komawa ofishin mutumin aka ce ai har ya tashi, wani dan banzan makoko da kududu ya tsaye min a makoshi, naji kamar in kurma ihu. Takardun kawai na tura mishi ta karkashin kofar ofishin na tura mishi text akan na ajiye su, na tafi. Na kula mutumin da alamu sai na biyo mishi ta bayan gida sannan zamu rabu lafiya dashi.
Ina fita daga cikin department din naji ana kiran sallar la’asar, don haka na tsaya a masallaci nayi sallah sannan na wuce. A bakin gate na tsaya na sayi yoghurt mai sanyi, da niyar dana koma asibiti kafin in shiga ciki zan tsaya in sha saboda tun dazu cikina yake kiran ciroma, dama ban wani ci abin kirki ba yau da safe. Bayan na biya kudin an saka min a leda, na karbi canjin da suka rage min na maida cikin purse dita. Typing din da Mr. Akafyi ya saka ni sun cinye min kudi, nasan sai na sake zama na tsara yadda zan tafiyar dasu kafin in kashe su ban tantance ba.
Na daga kafa da niyar tafiya kenan, naji karan horn a bayana. Banyi tunanin da ni ake ba daga farko, don haka na daga kafa na fara tafiya. Sai naji an sake a karo na biyu, an kuma kara, na dan juya gefen inda naji karan a kaikaice, gabana naji yayi wata irin faduwa lokacin da muka hada ido da Yaya Bilal. Na kalli gefena domin in tabbatar da cewa ni yake yiwa horn, da dai naga alamun da ni yake, don gashi nan har yanzu ni yake kallo, sai na daga kafa a hankali na tsallaka ta inda ya tsayar da motarshi a bakin titi.
Kofar gidan gaba ya bude min, don haka na silala na shiga a hankali kamar wata mai takatsan-tsan. Nace “Yaya ina yini?”.
Yana kokarin tayar da motar ya amsa da, “lafiya lau, daga ina haka?”.
Nace “naje ganin supervisor dina ne, amma cikin asibiti zan koma yanzu”.
Ya gyada kai tana humming, amma bai sake cewa komi ba, kawai motar naga ya ja ya abinshi.
Kamar yadda na kula da motar shi baka rabata da tattausan kida ko karatu, yau ma tattausar kidan wakar mawaki ‘Zayn Malik_Let Me’ ce take tashi. Ina son wakokin mutumin sosai. Na kwantar da kaina akan gilashin murfin motar, kamshin turaren Polo na RL da kamshin fresh strawberries na turara mota da kuma sanyin ac dake tashi a cikin motar, yasa na lumshe idanuna. Wata irin natsuwa dana rasa daga ina take naji tana shigata, naji kamar ana zare min duk wata gajiyar dake jikina. Ban san lokacin da barci ya fara daukata ba.
Sai da wani irin awkard feeling ya dameni a bayan kaina sannan, irin wannan feeling din da zaka ji idanu a kanka, kallo kuma na kurilla. Na tuna wata rana lokacin daya daukoni daga gidanshi, irin wadannan abubuwan na dinga ji har na dinga tunanin ko kuma kawai ina imagining hakan ne.
A hankali na saci kallon inda yake, karaf sai muka hada ido. Yayi saurin janye idanunshi daga kaina ya maida kan titi, sai dai ba’a jima ba muka sake hada wani idon dai.
Wannan karon ni na janye nawa idanun da sauri, na maida su na rufe, ban sake dagowa ba.
Tafiya da Yaya Bilal a rufi daya na mota ba yau muka fara yinshi ba, tun muna SBRS ya sha zuwa ya daukemu muje muyi hutun karshen mako a Kaduna, haka ma bayan mun dawo Zaria. Duk da cewa yawanci tare da Janan muke yin tafiyar, amma akwai daidaikun lokuta da yake rago min hanya daga gidanshi. Amma hakan bata taba faruwa ba, idan ma ta taba ko kuma tana faruwan, ni ban taba kula ba sai a dan wadannan lokuta. Shirun cikin motar yayi yawa, kidan ma ya tsaya cak kamar da can babu shi, it was unsettling.
Cikin sa’a muka karasa asibiti cikin dan kankanin lokaci, da kwatance na kwatanta mishi inda muke, yana gyara parking din motar na fita a sukwane kamar wadda ake mintsila, sai dana maida murfin motar na rufe sannan na leka ta saitin motar ina zuba mishi godiya. Ko jira inji ko ya amsa ko bai amsa banyi ba, na kara gaba kamar zan tashi akan iska saboda sauri.
Na rasa dalilin da yasa Yaya ya kirkiro da wasu irin halaye da bai saba ba sam cikin wadannan kwanakin. Koma dai menene, ni dai ina fata Allah Yasa lafiya.
*
Ranar Juma’ah, har na kwanta da dare kiran wayar Muhammad ya tashe ni, donhaka na daga wayar cikin barcin daya fara daukata, mun kwaso gajiya a asibiti yau.
Maganar daya fara min bayan mun gaisa ne tasa na bude idanuwana sosai, yace “are you ready baby?”.
Nace “ready for what?”.
Yace “ganina mana baby!! Kin shirya gani na gobe?”.
Na tashi zaune sosai akan katifata, nace “da gaske?! Don Allah kada kace min wasa kake yi!”.
Yace “kin san babu irin wannan wasan a tsakaninmu baby, da gaske nake. Kin shiryawa gani na gobe?”.
Na hau gyada kaina da sauri kamar ina gabanshi, “oh God yes, I’m hella ready!!”.