A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Ko rufe baki bai kai ga yi ba, na juya na daga kafa a sukwane na fada hostel. Wani daga cikin security yana tambayata lafiya lau? Me ya faru?? Amma na kasa amsa mishi.

Tunani daya ne zuwa biyu a cikin raina a wannan lokacin, lallai na cika sakara mara tunani. Ta yaya aka yi duk tsayin wannan lokaci da muka dauka muna waya dashi ban taba daukar muryarshi ba, ta yaya idanuna suka rufe ne? Ta yaya nayi sake irin haka? Kuskure ne ko kuma rashin sani??.

‘Na sanki farin sani!…’

‘Sunana M.B!…’

‘Ina aikine da wani kamfanin buga takardu…’.

Of course ya sanni farin sani, Yaya Bilal ne shi fa after all. M.B yana nufin Muhammad Bilal. Yana aiki da kamfanin buga takarda, dama mutumin da yake aiki da daily trust ai dole ma ya sarrafa takardu.
Mai yasa ban taba yin irin wannan tunanin ba, sai yanzu da ta faru ta kare? Babu zancen komawa baya??!.

☆⋆22⋆☆

A kofar daki muka ci karo da Esther ita kuma zata fito. Ta biyo bayana da sauri ganin yadda na wuceta a rikice tana jefa min tambayar lafiya? Amma na kasa daga baki in bata takamaimaimiyar amsa.
Na hade da gyalena da wayata nayi jifa dasu kan katifa, ni kuma na silale na zauna a tsakiyar dakin. Gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shin wai ko dai mafarki ne nake yi?.

Esther ta dafa ni tana dan shafa bayana in a comforting manner, tace “Na’ilah, me yake faruwa ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne?”, na bita da kallo kawai, ban ma san me zan ce mata ba. Kai ko na daga baki ma bana tunanin magana zata iya fita. Don haka na cigaba da binta da kallo kawai.

Wayarta tayi kara, ta duba mai kiran, da sauri ta juyo tana kallona, “sorry Na’ilah, ana jirana a waje. Don Allah kiyi hakuri kinji? Bari inje in dawo yanzu”. Ta fita da sauri.
Bayan fitarta na tallafo kumatuna da duka hannuwana biyu, na kurawa wayata dake yashe a kan katifata kamar ita zata bani amsar tambayoyina. Abin gwanin ban dariya gwanin ban haushi, yanzu ashe duk wannan waya da muke sha da shi, duk tsayin wannan lokacin, dama da Yaya Bilal muke waya? Haba, biri yayi kama da mutum! All those stolen glances idan muka hadu a karkashin rufi daya dashi wadanda daga farko na dauka ko ni ce nake wassafa hakan a cikin raina, kallon daya dinga jefa min ranar nan da nayi rashin lafiyar nan, har na dinga tunanin zafin zazzabi ne yasa nake ganin hakan, dama da gaske ne? Dama duk wannan lokacin, kallona kawai yake yi a dage, yana min kallon wata sakara wadda bata san abinda take yi ba? Da kuma maganganun daya dinga min a jiya, ba karamin godewa Allah nayi ba da bai sa giyar soyayya ta kwasheni na dauki alkawarin da ba zan taba cikawa ba. Yanzu da na amince mishi fa aka sa mana aure ko aka daura ba tare dana taba ganinshi ba? Nasan mutuwata ce tazo kawai.

Hankalina ya kasa kwanciya, duk inda na juya idanun Yaya Bilal kawai nake gani a cikin dakin, haunting me. Naji na fara damben warto numfashina da naji ya fara guduwa, ina warto shi da kyar.
Ban san lokacin dana rarumi wayata ba na dannawa Janan kira.

Ta dauka cheerily, murya cike da tsokana, “hey.., har Muhammadun naki ya tafi ne?!”.

A rikice na hau kiran sunanta ina maimaitawa kamar karatu, “Janan… Janan…!!”.

Nan da nan ta rikice, tace “subhanallahi, Na’ilah me ya faru ne?”.
Nace “Yaya ne! Yaya Bilal ne… Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau ya zanyi da rayuwata? Hasbunallahu wa ni’imal wakil!!”.

Ai sai na kara rikitata, naji alamun motsa kaya daga can inda take, “me ya samu Yayan? Kun hadu dashi ne? Wai meke faruwa ne? Kiyi min bayani please!”.

Na daga baki da niyar yin magana, amma sautin komi ya kasa fita.
“gani nan” kawai tace, kafin inji ta kashe wayar. Na koma na jingina da bango ina lumshe idanuna.

Abin kamar a almara haka nake jin shi. Yau da safe dana tashi, mafarki na farko dana fara tunawa wanda nayi ne akan Yaya Bilal. Maimakon abin ya bani mamaki, sai ma ya bani dariya. A tunanina meye hadin kifi da kaska? Tunanin Yaya Bilal da ni a waje daya, abu ne da bai taba, ina nufin koda wasa bai taba gittawa ta cikin raina ba, ko a mafarki ban taba ganin hakan ba sai a yau din. Shi yasa ko a dazun abin ya matukar bani dariya, saboda babu wani abu daya kamata inyi a wannan lokacin da yafi inyi dariyar.
Amma yanzu da naga abin yana shirin ya zama gaskiya, sai kuma abin yake shirin ya sanya ni kuka.

A yadda nake dinnan, a haka Janan tazo ta sameni. Ta tattagoni jikinta cikin tsananin nuna damuwa, ko bata furta ba fuskarta da idanuwanta sun nuna min hakan baro-baro. Hakan yasa naji jikina yana relaxing, na kwantar da kaina akan kafadarta, totally vulnerable.

Kusan mintunanmu biyar a hakan, kafin ta dago kaina daga jikinta, murya a tausashe, kamar wadda take tsoron idan ta dan kara daga muryarta zata saka ni kuka. Kodayake, hakan ne, ni nasan a yadda nake jina dinnan, zuciyata a wuya, to abu kadan da bai gamshe ni ba a yansu zai iya sa ni fashewa da kuka.

Tace “me ya faru ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne? Me kuma ya jefo Yaya Bilal cikin wannan magana?”.

Na daga baki nace “Janan, Muhammad… Shi.. Yaya Bilal…”. Nan da nan na fara hargitsewa. Tayi saurin taba kafadata, tace “kinga, nutsu kin gane? Yauwa, just calm down. Everything’s good, ok?”.

Na gyada mata kai a hankali, na fara jan numfashi ina saukewa a hankali har naji bugun zuciyata ya daidaita. A hankali na bude baki nace “Muhammad, Yaya Bilal ne! Yaya Bilal ne Muhammad Janan!!”.
Naji wata zazzafar kwalla ta ciko min idanu, nayi saurin kokarin maida ta. Sai da na fadi maganar da karfi ta shiga kunnuwana, sannan naji gaskiyar lamarin yana shigata.

Janan ta zuba min idanu tana kallo, kamar wadda take jira in ce mata tsokanarta nake. To ai ni kaina jin abin nake kamar a mafarki ko a almara. Ni kaina na kasa yarda wai hakan ta faru.

Zuwa can tace “ta yaya?”.
Nan na gyara zama na fede mata biri har wutsiya, ban rage mata komi ba. Tun daga fitata daga hostel, maganar da muka yi dashi har gudowar da nayi. Ban san cewa hawaye nake ba, sai dana sauke aya. Naja numfashi na ajiye, sannan naji lema tana bin kumatuna. Na sa hannu na share, amma ina dauketa wata ta sake gangarowa.

Na dora da, “Me yasa ni? Me yasa Yaya zai yi min haka? Me yasa hakan zata faru dani? Janan ya zanyi?”.

Tace “mafita daya ce, kiyi hakuri ki danne zuciyarki, ki saurareshi kiji abinda zai ce”.

Na tabe baki ina jinjina kai, “tab, lallai ma! In saurareshi ince mishi me? In gaya miki gaskiya ni da Yaya yanzu sai dai hange daga nesa, kai ko daga nesar na hango shi, zan canza hanya ne a sukwane ba tare da bata lokaci ba!”.

Tace “amma kuma hakan ba mafita bace Na’ilah. Kika san ko yana da wani kwakkwaran dalili da yasa yayi hakan ne? Kada fa ki yanke hukunci cikin fushi Na’ilah, daga baya kuma ki zo kiyi dana sani!”.

Nayi wata yar dariya da daga jinta babu digo ko alama ta farinciki a cikinta, sai akasin sa. Nace “wane dalili ne daya wuce ya muzanta ni, ya maida ni sakara? Da ba don nasan Yaya ba sosai, da sai ince baki ya hada da Umar ko wani akan suyi wasa da hankalina. Kodayake, ban san shi ba yanzu anymore!”.

Janan ta kalleni, frowning. Tace “Ni nasan Yaya Bilal sosai, ba zai taba stooping that low to do something like this ba. Kamar yadda nace, da ace baya da kwakkwaran dalili, to ina mai tabbatar miki da cewa da ba zai taba ma bata lokacin shi tsawon lokutan nan ba!”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button