A ZATO NA COMPLETE

Nayi dan murmushi, “Yaya, nasan amfanin wayata ni fa, wasu lokutan rashin caji ne yake sawa idan kun kira kuke ji a kashe”.
Yace “kwarai kuwa, ai da yake duk Nigeria baby garin da ake wa kwauron wutar lantarki kamar nan ko?”.
Nayi yar dariya, “ni ban ce haka ba. Anty Sailu ta sauka ne?”.
Yace “tukuna dai, yanzu haka muna asibiti ma”.
Nan da nan naji gabana ya fadi, nace “lafiya? Jikin ne ya motsa?”.
Yace “a’ah, amma likitocin sun ce tana bukatar zama a asibitin zuwa lokacin da zata haihu domin su dinga monitoring dinsu ita da babyn. Amma so far dai komi lafiya lau”.
Na dan sauke ajiyar zuciya, “Masha Allah, Allah ya sauketa lafiya. Amma nayi fatan ace ina nan yanzu tare daku wallahi”.
Yaya yace “to ya zaki yi? Haka karatun ya gada ai. Ina fata dai idan ta haihu zaki zo ko?”.
Nace “sosai ma! Ai ko muna exams sai na kansileta nazo!”.
Yaya ya saki yar dariya, “ba wani nan. Ke dai kawai kiyi fatan kina free lokacin”.
Nace “to shikenan. Ya su Inna? Kwana biyu ma bamu gaisa dasu ba”.
Yace “a asibiti na baro ta, ni na dan fito yanzu. Amma idan na koma zan kira ki sai ku gaisa dasu”.
Nace “to shikenan, sai ka dawo din”.
Yace “babu dai wata matsala ko?”.
Nayi dan murmushi a hankali, nace “babu Yaya. Sai anjima”. Muka yi bankwana na ajiye wayar.
Aikin da nake yi na komawa, ina yi ina bin kira’ar har na gama. Ina gamawa na fara gyaran wajen da nake. A takaice sai wajen karfe daya na gama komi.
Bayan nayi sallah na fita waje can wajen yar kasuwar su na siyo kayan miya na dawo daki na hada miya na dafa farar shinkafa na ci.
Na dauki system dina na fara aiki akan project din da nake to har zuwa lokacin da Janan ta kira ni, sannan na dakatar da aikin na dauki wayar. Bayan mun gaisa ta watso min tambayar lafiya ta lau dai ko? Na kada idanu kamar ina ganinta, “ehh, ga wanda ya kwana ya wuni cikin tashin hankali da damuwa da rashin barci har da karin ciwon kai, lafiyata lau Jan. Ina fata kinyi kin tashi kin kuwa wuni cikin koshin lafiyata?”.
Janan tayi yar dariya, “ai daga ji ma babu tambaya lafiyarki lau, ba sai kin janyo min wani dogon bayani ba. Ya karatu, ina fata dai kinyi ko?”.
Na dan saci kallon tulin jotters da textbooks dana fiddo dazu wadanda suke jiran in daga su, tare da sauke ajiyar zuciya lokacin dana tuna akwai fa sauran gingimemen aiki a gabana. Nace “ban fara ba wallahi, amma anjima da yardar Allah zan fara tunda dama revising ne kawai zan yi”.
Tace “hummm, nima hakan take. Allah dai ya bamu sa’a”. Nace “ameen”.
Tayi shiru, hesitating, banyi kokarin katseta ba ko tambayar lafiya, nasan tunda naji haka akwai magana da take son muyi, wadda kuma bata wuce ta mutum daya. Sai da tayi radin kanta tace “me zai hana ba zaki saurari Yaya ba don Allah? Ko sau daya ne Janan, ya cancanci wannan damar daga gareki”.
Nayi shiru ina sauraronta, sai data dire aya sannan nace a hankali, “dalilin kenan da yasa kika kira ni dama? Saboda Yaya?”.
Itama ta danyi shiru kafin tace “wai me yasa kike cewa haka ne Na’ilah? Ke kinsan cewa tsakanina dake ai babu wannan abin, wallahi jin ki nake kamar yar uwata ta jini, sai dai shima Yayan ina jin shi a cikin jinin jikina. I just want what’s best for you Na’ilah, shine kawai!”.
Na san duk abinda ta fada hakan take, idan kuma da kunya da kara, bai kamata in watsawa dan uwanta kasa a ido ba, sai dai bana tunanin zan taba iya wannan abu da Janan take kokarin sanyowa, ba zan iya yin wannan karar ba.
Nayi kasa da murya, cikin tsananin son yi bayanin da zata fahimta, wanda kuma ba zata kullace ni ba, nace “Janan… Ke kinsan abinda yake damuna, kin kuma fi kowa sanin yadda nake kin wannan akidar, don haka don Allah don Annabi Jan, ki taimake mu ki daina sako wannan maganar. Kince you just want what is best for me, barin wannan maganar shine mafi a’ala a gareni, don haka don Allah mu daina yin ta kawai. Don Allah kice min kin fahimce ni?”.
Tace “na fahimce ki, sai dai Na’ilah, wannan fa ba karamar magana bace ko kuma maganar wasa da zaki ce a barta kamar bata taba faruwa ba. Yaya ma ba zai taba kyaleki ba in gaya miki gaskiya, shirun da kika ga yayi kawai ya baki iska ne ki hada tunaninki waje daya. Ina ga da kin hakura kun yi magana, kiji abinda zai ce mikin”.
Na fara gajiya da maganar wannan, tun jiya muke nanatata kamar cin kwan makauniya, cikin nuna alamun gajiya da maganar nace “kamar yadda nace miki, kawai mu bar maganar nan. Babu wani abu da zamu tattauna tsakanina da Yaya Bilal, ke kin sani. Ba zan taba mika wuyana a sare shi ba alhalin ina cikin hankalin kaina, haba Janan, idan har kin tabbatar kina so na kuma kina kaunata, bai ma kamata ace kina nema kiyi convincing dina ba koda wasa”.
Itama cikin nuna alamun gajiyawa tace “whatever Na’ilah, ni dai iyaka shawarar da naga zan iya baki kenan. A gani na idan kuka yi maganar, kika yi mishi bayani, zai iya ba zuciyarshi hakuri ya nemi daidai dashi wadda zata iya zama dashi da matan shi tunda ke kin ce baki iyawa. A ganina kenan. Sauran kuma, Yana gareki. Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, sai mun hadu a asibiti gobe!”. Ta katse wayar.
Na bi wayar da kallo. Daga jin yadda muryarta ta dan daga, ranta ne ya fara baci. Ban yi kokarin sake kiranta ba, na maida wayar na ajiye. Bana tunanin wani abu zai iya canza min kudirina, ciki kuwa har da fushin Janan.
Na fahimci kaunar da take yiwa dan uwanta ce ta haddasa hakan, sai dai me yasa ni ba zasu fahimceni ba? Me yasa ba zata yi kokarin fahimtar dalilina ba??!.
Nayi kokari na kauda tunanina daga kan wannan magana na ci gaba da abinda nake yi.
Sai bayan la’asar sannan na fita karatu. Har aka kira magriba ina can, sai masallaci naje nayi salla. Akan hanya na tsaya na sayi doughnut da yoghurt, na koma class. Sai wajen karfe goma na koma daki. Ina komawa ko kayan jikina ban iya cirewa ba na zube akan katifa saboda barcin daya cika min ido.
*
Washegari kuwa garas na tashi, bayan nayi sallah na fara duk wasu al’adu dana saba kafin in fita zuwa asibiti. Jikina a dan sanyaye yake saboda nerves din jarabawa, kodayake nasan kusan kowa ma haka yake ji, an riga an saba. Na shirya a nutse, ban dora abin karyawa ba saboda azumin sitta shawwal da nake yi, zuwa gobe zan gama gabadaya in Allah ya yarda.
Akan hanyata ta zuwa venue din da zamu yi jarabawar, wayata ta fara pinging alamun shigowar message. Ina dubawa naji gabana yana dukan uku-uku, Yaya ne. Kin dagawa nayi, ina tsoron in daga in karanta abinda zai hana ni sukuni bayan ina da muhimmmiyar jarabawa a gabana.
A kalla kafin in karasa venue din, ya kara turo wasu sakonnin kamar guda uku haka. Na tsaya na bada ajiyar wayar wajen securities bayan na kasheta, sannan na shiga ciki.
Seat dina yana kusa dana Janan ne, yadda muka rabu da ita jiya nayi tunanin ko kallon arziki ba zan samu daga gareta ba, sai ta bani mamaki data haskeni da murmushin man nata, ta dan matsa kadan yadda zata bani waje sosai tana cewa “sai yanzu? Wato kema kin koyi makara ko?”.
Na dan saki murmushi a tausashe, duk da yanayin da nake ciki, sai naji raina ya dan yi sanyi, na zauna kusa da ita, “ai kin san zama da madaukin kanwa…”.
Tayi yar dariya, “idan ma dani kike, bani na goga miki ba, can zaki je ki nemo wanda ya goga miki yarinya!”. Muka yi musayar murmushi.
Ba abin mamaki bane ga halayyar Janan, sanyin zuciya irin nata da kawar da kai har kullum shine abinda ya tsananta tsayin abotarmu da ita. Ina girmamata saboda hakan.