A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Sai da ya gama kare min kallo son ran shi, sannan yayi gyaran murya, ya kuma ambaci sunana cikin wata irin murya data girgiza gabadaya sassan jikina. Ban iya amsawa ba, sai daga kai kawai da nayi briefly na kalleshi wanda ko rabin sakan banyi ba na sake sadda kaina kasa.

Yace “Na’ilah kamar yadda na fada miki, ko kuma nake fada miki, takowa nayi musamman domin in baki hakuri. Na yarda cewa abinda nayi was not wise, kuma ba haka yakamata ace na biyowa abin ba. Na fahimci kina fushi, kina ganin kamar kawai ina yi miki wasa da hankaline wanda sam ba hakan bane. Saboda haka ne nake so ki bani izini, in bi ta hanyar data dace. Ina so ki yarje min, in gana da mahaifinki!”.

Nayi gaggawar daga kaina na kalleshi sosai, kamar wadda aka bugawa guduma a ka. Wanda na tabbatar da cewa gurguwar shawara ce, saboda muna hada idanu dashi, I was a goner. Kamar maganadisu, haka na kasa janye idanuwana daga kanshi, ban san me kuma ya hana ni yin hakan ba. Gabadaya sai ma na manta da dalilin da yasa na daga kai na kalleshi har muka hada idanu dashi.
Shi ne ya fara janye idanunshi, sai a lokacin na hau kyafta idanu kamar wadda abu ya fada mata cikin idanu. Dole na saddakar, na ajiye duk wani abu da nake son fada a lokacin na tsaya ina saurarenshi.

Ya cigaba da cewa, “wannan yana daga cikin manyan dalilan da yasa na baro wajen aikina yau, domin ina so ne ace gobe in shaa Allah na hadu dashi munyi magana, mun tattauna an san da maganar mu. Tunda nan da watannin da ba zasu gaza shida ba zaku gama karatu, ina so kafin nan mu samu fahimtar juna a tsakaninmu, ta yadda kina gamawa ba za’a bata lokaci ba, sai kawai a daura mana aure. Ya kika ce?”.

A raina naji wani banbarakwai. Abin dariya wai yaro ya tsinci hakori! Wato shi ana maganar son a san juna, shi ta maganar aure ma yake yi. Kodayake, yayi zancen fahimtar junan ai. Ganin na dauki lokuta ban tanka mishi ba, yasa ya sake cewa “ina saurarenki”, cikin nuna kagara da son jin amsa daga bakina.

Ina so in daga baki ince mishi ni bana son shi, bana son aurenshi kuma bana son zama dashi, amma sam bakina ya kasa motsawa. Don haka na girgiza mishi kai kawai.

Yace “baki son aurena?”. Na gyada mishi kai.

Ya dade yana kallona, har sai da naji na tsargu kafin ya nisa, yace “saboda menene? Na miki tsufa?”.

Naji kamar into kwashe da dariya, wa yake ta wani maganar tsufa a halin da ake ciki yanzu? Balle ma Allah na tuba, wa zai dubi Yaya Bilal a yanzu ya kira shi da tsoho? Ai sai dai mara tsoron Allah.
Don haka na girgiza mishi kai alamun a’ah.

Yace “to idan ba wannan ba, menene? Baki so na?”. Wannan karon ban ce mishi komi ba, a tsaka tsakiya nake. Kowace amsa na bashi yanzu, a tsakiya nake. Idan nace mishi bana son shi, na yiwa kaina karya. Idan na amsa ina son shi kuma, na karyata wani bangare na zuciyata kenan da yake so tun karfinshi ya nuna min bana bukatar shi a cikin rayuwata.

Nan ma ya jima yana kallona kamar wanda yake karanta ta, kafin ya sake cewa “saboda ina da mata ne har biyu?”.

Nan fa ya sosa min inda yake min kaikayi, ba ko sake tunani na gyada mishi kai. Yace “me yasa? Matana zasu hana mu zaman aure dake ne, ko kuma kina tunanin ba zaki samu kulawar da kike bukata daga gareni bane saboda mata na?”.

Ta wani bangaren har da wannan, sai dai wadannan duk sharar fage ne akan babbar matsalar. Wani abin mamaki kuma, sai a lokacin ne naji na samu muryata.

Nace “Babu ko daya, kayi hakuri don Allah. Ba zan iya abinda kake so ba!”.

Yace “amma me yasa? Ina zamu kai son da muke yiwa juna?”.

Nace “ai ana barin halas don kunya!”.

Yace “wace kunya ce za’a bar halas saboda ita? Kada ki ce min wai saboda Ummah ne ko Janan, domin na tabbata su a garesu dauri ne zai tsinkewa mai kaya a gindin kaba. Bayan su kuma ban ga wanda zaki ce zaki zauna jin kunya ba. Idan ke zaki iya kauda kai, ki tuge son da kike min daga cikin zuciyarki, in gaya miki gaskiya ni ba zan iya ba! Don haka tun ma da wuri ki sake tunani”.

Ni kuwa na sake baki kaina a kasa, kunya kamar kasa ta dare gida biyu in afka ciki. Tun da muke da Yaya, da duk sanin dana mishi, bamu taba doguwar magana mai tsayin gaske ba, balle har maganar so da aure ta shigo ciki.

A hankali na fara girgiza mishi kai, nace “ni fa duk ba wannan ba, kayi hakuri don Allah ka rufa min asiri, ka janye wannan maganar a tsakaninmu. Idan kai zaka iya, ni ba zan iya ba!”.

Yace “babu abinda bawa ba zai iya ba Na’ilah, sai wanda kawai yaga damar ba zai iya din ba, sannan wannan magana da muke yi yanzu, babu wani abu da ba zaki iya ba. Zama da nine ba zaki iya ba, ko kuwa zama da kishiyoyin?”.

Na girgiza kai kawai, Yaya Bilal ba zai taba ganewa ba. Ba zai fahimta ba, saboda haka nasan zama yi mishi wani bayani ma bata lokaci ne, don haka nayi shiru kawai.

Ya fara wasu dogayen maganganu akan yadda zai kama min gidana in zauna ni kadai ba tare da takura ba, da yadda zai kula dani. Har dai ya fahimci cewa ba fa saurarenshi nake yi ba, daga karshe dai yace in shiga cikin hostel, zamu sake yin magana.

Ni dama jira nake, na daga kafa da sauri na fada ciki, dama a kagauce nake. Bana so in mishi tsaurin ido ne, in tafi yana cikin yin magana kawai. Har yanzu da sauran mutuncinshi a cikin raina, ina kuma ganin girmanshi.

☆⋆26⋆☆

“Wai ni wasu maganganu ne nake ji suna tashi a cikin ward dinmu game dake da Dr. Na Abba. Da gaske ne?”.

Aisha, kawata take tambayata lokacin da muke kan hanyarmu ta dawowa daga cikin asibiti zuwa hostel a ranar juma’ah. Janan ta wuce gida abinta.
Na girgiza mata kai distractedly, “kin san mutane da son yayata abinda ba shi kenan ba, babu wata maganar azo a gani a tsakaninmu, har yanzu tangarda take yi”.

Aisha ta gyada kai cikin nuna fahimta, tace “seriously, I shall warn you though, ana yawan fadin rashin kyawun halayen mutumin nan fa, duk da nima ba gani nayi da idanu na ba, ji nayi ana fada”.

Na gyada mata kai kawai ina dan murmushi na yake, ba ita bace ta farko ba, ba kuma ba yau aka fara tarana da magana makamanciyar wannan ba, duk dai akan Dr. Na Abba. Cikin sati biyun da suka wuce, a kalla mutane fiye da shida, ciki har da Doctors da matrons, sunyi min magana ko ince sun buga min gargadi game da tarayya ta da Dr. Na Abba. Sai dai wani abu da basu sani ba shine, ni dai ba son shi nake yi ba. Ban kuma taba considering din maganar shi ba a cikin raina koda wasa. Saboda haka ni a ganina bata yawun bakinsu ne kawai suke yi, da kuma bata lokaci. Sai dai ban taba fada musu hakan ba, illa iyaka kawai duk abinda suka ce in tsaya in saurara, idan suka gama in musu godiya a wuce wurin.

Yanzu ma abinda na yiwa Aisha kenan, na mata godiya tare da tabbatar mata da cewa zan kiyaye kamar yadda ta bukata. Tace tayi farinciki da fahimtarta da nayi muka yi sallama da ita lokacin da muka shiga hostel, na haye sama ita kuma ta wuce sama dakinta.

Na saka key na bude dakin, kasancewar yau juma’ah, Esther ta tafi weekend, nasan cewa ni kadai zan dinga kwana a dakin daga yau har zuwa ranar sunday.
Na cire kayan jikina na rataye a jikin kusar da muke rataye kayanmu, na saka riga da wando cotton, na barci. Ba sallah nake yi ba, saboda haka lafiyar katifa kawai na bi na kwanta. Na janyo wayata na kunna, na hau chatting, bugs games, kallo, jin wakoki, har kokarin yin reviewing din project work dina dana kammala nayi, amma babu abinda ya dauke hankalina daga kan abu dayan nan da nake ta gujewa; Bilal Al-Qaseem.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button