A ZATO NA COMPLETE

Yace “ban ce ko daya daga ciki ba, illa iyaka ina so in nuna miki cewa wannan kauce-kauce da kike yi babu abinda zai haddasa mana sai bata lokacinmu da yake yi kawai. Na’ilah, mu fa ba kananan yara bane, bai kamata ace mun dauki magana daya muna ta nanata ba, bayan muna da yadda zamu fuskanci matsalar mu kuma magance ta. Saboda haka yanzu ki fada min, meye matsalar ki game dani? Kin san ina son ki ko?”.
Amsar dana bashi ta fito daga cikin bakina tun ma kafin in tauna ta, kai ban ma san na fade ta ba sai dana ji tana ringing a cikin kunnuwana, da kuma shirun daya biyo bayan na furta ta, da alamun shi kanshi bai yi tsammaninta ba; “nima ina sonka!”.
Kusan sakanni biyar da fadin hakan, kafin naji yayi gyaran murya, ni kam sai aka barni da kyafta idanu, yace “good. To menene matsalar? Na riga na fada miki idan ta matana ne baki da matsala da su, gidan ki daban zan ware miki, ba lallai sai kun hadu dasu ba. Wannan ganin damar ki ne, idan kin so haduwa dasu sai ki hadu dasu, idan baki so ba, sai kiyi yadda kike so. Bayan wannan kuma sai me? Ban takura ki ba Na’ilah, zan jira ki gama karatunki kafin a tado maganar auren, bayan nan zan bar ki kiyi aikinki, ba zan hana ki ba. Sai me kike bukata kuma?”.
Shi a tunaninshi rashin hada mu gida daya kamar wani solution ne, sai dai a nawa tunanin, wannan ba komi bane. Ya hada mu gida daya ko bai hana ba, duk dai yana da mata ne dai, kuma zamu yi sharing dinshi dasu. Na daga baki nace “bani da wata matsala Yaya, kayi hakuri. Nima ba wai ina jindadin wasa da hankalinka da nake yi bane, amma the fact that zan zauna da kishiya daya ma bana so balle kuma har biyu, kayi hakuri don Allah”.
Yace “shi kuma son da muke yiwa juna fa? Kin kasa daukar matsaya daya Na’ilah ki zauna a kanta, daga yau kice wannan, sai gobe ki ce wannan. Kina ganin ina da lokacin zama bin kanki ne? I can’t leave my work da duk wasu harkokina, ina chasing dinki Na’ilah! I just can’t. Don haka idan zaki zauna ki yanke shawarar da zata fisshemu, gwanda ma tun wuri ki yanke. Haba! Na gaji! Na gaji wallahi!! Wai baki da zuciyar tausayi ne? Ko ke baki san kaddara ba ne? Kada ki manta da cewa Annabinmu ma da muke yin koyi da koyarwa shi bai zauna da mata daya ba. Ke a ganinki rashin zama da kishiya zai hana ki rayuwar farinciki a gidan aurenki bane ko me? Kina ina mata da dama suke baro gidan auren nasu babu kishiya ba kome, gasu nan birjik suna yawo akan titi muna ganinsu, amma kuma masu kishiyar suna zaune a nasu gidan salin-alin suna zaman lafiya? Kin kishiya da kike yi kamar izgilanci ne kike yiwa Allah, tunda kin karanta, kin kuma san cewa ba haramun bane a musulunci. Ita kishiyar hauka ce?!”.
Yadda ya hakikance yana fada yasa naji nima raina ya dauko baci, a tunanina idan ba’a lallasheni ba, bai kamata ace za ayi min ihu ba. Nace “da kake maganar kaddara da kuma izgilanci, shi Allah ai baya dorawa rai abinda ba zai iya dauka ba sai dai bawa ya dorawa kanshi. Saboda haka ina ji ina gani ba zan kai kaina wajen wahala ba. Tunda nace ka kyaleni, bana so, ba sai ka kyale ni din ba? Ana dole ne?!!”.
Yace “haka kika ce ko? To ba laifi. Dama ina bin kanki ne kawai saboda kada kice anyi miki rashin adalci ko wani abu, amma tunda ke kunnenki na kashi ne, kuma idanuwanki a rufe suke, ba kya fahimtar komi, to zan biyo miki ta hanyar da baki so. Idan ke kin iya yiwa zuciyarki rashin adalci ne, ni ba zan cuci kaina ba akan wani dalili can naki! Ina ce ba mahaifinki ne da bakinshi yace ba zaki aureni saboda ina da mata ba ko? Kuma ba Allahn daya halicce ki bane? To ki kashe kunnenki da kyau, ki saurareni kiji, maganar neman aurenki yanzu na fara ta, ba kuma zan tsaya ba sai inda karfina ya kare. Zan kuma yi duk abinda zan yi in ga cewa kin shiga gidan da kike matukar ki, don Allah ki kashe kanki ranar da aka kaiki gidana a matsayin matar aure, sai in ga karshen tsana!”.
Nace “Wallahi ba zai yiwu ba, ba kuma zan yarda ba. Ni dama nasan ba sona kake yi ba kamar yadda kake ikirari, in Allah ya yarda sai Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Mugun kudirinka ba zai cika a kaina ba!”.
Yace “zamu gani Na’ilah!”. Daga haka ya kashe wayar.
Naji kamar in fasa ihu, jikina har rawa yake yi tsabar bacin rai. Lallai Yaya Bilal has got some nerves! Har yana da bakin da zai daga yace wai zai aureni ba da izinina ba? Har yana da wannan ikon a kaina?! To ai idan yasan wata bai san wata ba. Zan ga da abinda yake takama dashi kuwa!.
Na share hawayen da suka zubo min, na kara daukar wayata da nayi jifa da ita, na shiga cikin contacts dina. Ina ganin sunan wanda nake bukatar gani, na danna kiran ba tare da bata lokaci ba. Tayi kara daya, biyu, ana uku aka dauka.
.Cike da cheeriness da alamun tsokana da baka taba raba muryarshi da ita, yace “hello, Nas. Ya kike?”.
Na dauki ajiyar numfashi na sauke a hankali, na dan kakaro murmushi duk da nasan cewa ba ganina yake yi ba, nace “hello Doctor, maganar ganin iyayena da kayi ranar nan, ka shirya yi yanzu?”.
Yace “of course Na’ilah! Dama ni ai jiranki kawai nake yi. Yaushe ake bukatar gani na ne?”.
Nace “idan ma a gobe ka shirya, zaka iya zuwa ka gansu”.
Yace “Masha Allah, that’s good. How about in zo anjima sai mu sake tattaunawa akan yadda za ayi?”.
Na dan jinjina kai sama, “yeah, hakan ma yayi. Sai ka zo kenan?”. Yace “in shaa Allah. Gani nan zuwa”.
Nace “sai kazo!”. Na ajiye kan wayar.
*
Kwana uku bayan haka, Janan ta shigo asibiti tun da safe ranar alhamis. Abin ya bani mamaki. A bakin hostel muka ci karo da ita, ni zan fita ita kuma zata shiga. Na kalleta cike da mamaki, nace “lafiya kuwa? Mai ya shigo dake nan da wuri ne?”.
Bata tsaya amsawa ko yi min bayani ba, taja hannuna muka koma daga ciki, can gefe, tace “abinda kika yi kina ganin shine daidai a wajenki?”.
Nace “me nayi?”.
Tace “Yaya Mudatthir ya kira ni dazu tun da sassafe”.
Sai lokacin na fahimci dalilin shigowarta din da kuma tambayoyinta. Nima bamu jima da yin wayar dashi ba.
A yadda muka yi da Dr. Na Abba lokacin da yazo ranar litinin, mun tsaya akan cewa zai je Gashua ya samu su Malam su akan maganar mu. A washegari talata na kira su Fatsu na sanar dasu bakin da zasu yi, zai je ne kawai suyi magana, a san dashi, sannan a tsaida ranar da yakamata magabatanshi su je. Su Malam suka yi farinciki matuka, har Fatsu tana cewa har ta cire rai da zaton zata ga wannan rana, ni dai kawai uhmm nace mata.
A daren ranar jiya bayan Dr. ya kira ni ya sanar dani cewa sun dauki hanyar Kano daga Gashua, Yaya ya kira ni. Tambayata kawai ya hau yi akan wai na tabbatar da cewa wanda na turo mishi na amince dashi? Nace ta yaya zan tura wanda naji ban aminta dashi ba wajen iyayena?. Yaya yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, kafin yace “amma kuma Baba yace wani yaje wajenshi a jiya din, shima duk akan maganar ki ne!”.
Naji an fara min wani luguden daka a kirji, ashe dai Yaya Bilal da gaske yake ba da wasa ba. Amma a zahiri sai na dake, nace “ni fa bansan ko wanene ba, don ni babu wani wanda muka yi magana dashi akan zai zo bayan Dr. Na Abba”.
Yaya yace “to ai shikenan”.
Daga nan muka dan yi hira, na tambayeshi jikin Sailu da har yanzu tana asibiti. Yace dukansu lafiya lau. Sannan muka yi sallama.