A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

To yau kuma da safe sai ya sake kirana, yana tambayar wai dama wanda yaje wajen Baba Yayan Janan ne? Nace “ni fa Yaya na fada maka ban san kowanene ba”.
Yace “kada ki raina min wayo mana Na’ilah. Ni nasan yadda kika sako karatun nan naki a gaba, maganar aure yanzu bata cikin kanki. Tunda naji dama wai kin turo wani gida kai tsaye, nasan da wata a kasa. Don haka ki fada min abinda yake faruwa”.
Nace “to ni Yaya sai dai kuma in karya kake so in maka, amma babu abinda yake faruwa. Kawai na samu wanda hankalina ya kwanta dashi ne, dama can don dai ban samu wanda ya shiryawa auren bane”.
Yace “ina wannan yaron da kuke tare dashi kuma fa, sojan nan?”. Nace “ni tun yaushe da muka rabu dashi?”.

Yaya Mudatthir yace “shikenan Na’ilah, ni dai ina shawartarki da ki bi koma menene a hankali!”. Bai jira abinda zan ce mishi ba ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo cikin yamutsa fuska, me yasa ne yake wani magana yana bani a linke? Sai ban saka maganar a kaina ba, naci gaba da shiryawa ta.

To kuma gashi ina fita naci karo da Janan, itama tana bani tata linkakkiyar maganar.

Nace mata “eh, ina ganin shine mafi a’ala a wajena Janan. Ina ganin kuma hankalina zai fi kwanciya a hakan”.
Tace “ki dai bi a hankali, kada kije ganin neman gira ki rasa idanu. Ki gujewa garwashi ki fada cikin wuta!”.

Na dan jefa mata harara, “ni fa saboda wutar da Yayanki ya hada min yan kwanakin nan, kwalwata bata gane maganganu masu baki biyu. Don haka ki daina bani a dunkule kawai ki fito ki min magana kai tsaye don bana fahimtarki”.

Itama ta harareni, tace “shi wanda kike likewa din, kina da tabbacin zai rike ki kamar yadda kike hange ne? Kin kuwa san waye Dr. Na Abba? Shekarunshi talatin da biyar, aurenshi bakwai Na’ilah! Aure bakwai! Amma yanzu bashi tare da mata ko guda daya sai ‘ya’ya kashi-kashi dake gaban mahaifiyarshi wadanda matanshi suke ajiyewa idan suka rabu. Kin san me yake hada shi da matan har su rabu? Kika sani ko yana da wasu halaye da basu dace bane shi yasa? Kina da tabbacin ke idan kika aure shi a hakan, zaki zauna a gidanshi ne? Wallahi ina jiye miki yin dana sani Na’ilah”.

Nace “na farko ba ni na like mishi ba, idan da wanda ya likewa wani a cikinmu to shine. Sannan nasan da labarin hakan ai, kawai mutane ne da basu rabuwa da tashin zaune-tsaye. Kika sani ko matan nashi ne masu halaye marasa kyau? Idan ma ba hakan bane, wai meye ruwan mutane ne da rayuwarshi iye?”.

Janan ta daga baki cike da mamakina, tace “wai lafiyarki lau kuwa? Kin ma san abinda kike fada ne? Auren mutumin wannan da zaki yi sunan shi gudun gara, kin guji auren mai mata kin fada gidan mai ‘ya’ya. Yo ba gwara auren mai matar da kika sani ba sau dubu akan wanda baki sani ba? Kodayake, rayuwarki ce ai. Kiyi duk yadda kike so da ita. Daga yau na daina yi miki magana game da Yaya Bilal in Allah ya yarda. Kiyi duk abinda kike ganin shine daidai a wajenki, jiki magayi!”.

Ta juya ta wuce abinta, ni kuma na bita da kallo na wasu lokuta, kafin na bi bayanta da sauri ina kwala mata kira.

Da yamma Yaya Mudatthir ya kirani, Anty Sailu ta haifo yaranta maza biyu.

????????????????

              *☆⋆29⋆☆*

“Yanzu yaushe kike tunanin zamu tafi wajen sunan ne? Ina ganin kamar mu tafi Talata ko? Ya kike gani?”.
Janan take tambayata a washegarin ranar da aka yi haka, bayan mun dawo daga masallaci.

Nace “zaki je ne?”.
Ta dan yamutsa fuska cikin nuna alamun rashin jin dadi, “ban gane ba? Kina tunanin ba zan je bane ko me?”.
Nace “kinga, ni fa ba cewa nayi ki hayayyako min bane. Nasan Yayanki da protectiveness dinshi, ban sani ko zai barki kije bane, shi yasa”.

“Wannan kuma matsalar mu ce ni dashi, don’t you think? Kawai ki fada min lokacin da kike ganin yakamata mu tafi!”. Ta fada a dan zafafe, har sai dana kara kallonta cikin mamaki.

Naja tunga na juya ina kallonta tare da kama kugu, nace “ni fa na kasa gane miki ne, tun da kika zo yau kike hade min girar sama data kasa. Na miki wani abu ne?”. Duk yadda naso inyi masking damuwar data lullubeni, na kasa. Janan ita ce mutum daya kacal da duk duniya nake ganinta kamar jinina, kai wasu lokutan ma fiye da jinina. Ita ce kuma kadai nake ganin duk duniya, babu abinda ba zan iya sadaukar mata ba. Sai dai banyi tunanin sadaukarwa zata zo da consequences kamar wannan ba, wannan shine abu dayan da ba zan taba iya sadaukarwa ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin cewa ban biye mata mun raba kai a tsakiyar titi ba, nasan cewa zuciyarta cike take da haushina dankar. Amma na fara kaiwa bango.

Tayi ajiyar zuciya, kanta yayi kasa cike da nuna nadama, “am sorry… Kawai na kasa wrapping kaina akan abubuwan da kike yi ne. Kin san cewa na damu dake, bana so ki aikata abinda zai zo ya zame miki dana sani daga baya wallahi. Why not Yaya Bilal kam? Kinga bayan mun bar nan, babu ruwanmu da tunanin rabuwa, zamu sake zama tif da taya, mu zama yan uwa na hakika”.

Na dan sosa saman hancina cikin nuna alamun gajiya da zancen wannan, kamar ba ita bace take ihun maganar wannan ba zata sake hada mu ba jiya-jiyan nan.
Nace “Janan kenan! Wai ke a tunaninki zan iya jera kafada ne da matan Yaya Bilal muyi kishi dasu? Ki dube su fa ki dube ni, me zan nuna musu bayan bakar fata da tsaurin ido? Yadda yake da mata fararen nan tubarkallah, kamar ka taba jini ya fito, ban san me yake nema a wajena ba”.

Janan ta kwashe da dariya, tace “babe! Wani lokacin shirmen ki dariya yake bani wallahi. You are very shallow, God! To an fada miki farin fata shine auren? Shi kanshi Yayan idan zan iya tunawa, ai ba fari bane. Allah wallahi ina shawartarki ni dai, ki sake zama kiyi tunani. Har ga Allah ba wai don Yaya yana Yayana bane, amma da ace shi wanda kika kafewa din kina son shi, kuma zai iya rike ki cikin mutunci, wallahi da baki kara jin bakina cikin maganar nan ba. Saboda ba karamin bata min rai kika yi jiyan nan ba”.

Nace “kiyi hakuri”, cikin sanyin murya. Jiyan yini nayi cike da damuwar bacin ran dana haddasa mata. Sai dai hakan fa bai yi kusa daya sanyayar min da gwiwa ba. “Amma wa yace miki bana son Dr. ne? Kina tunanin zan iya amincewa da auren wani bayan bana son shi? Kawai zama da kishiya ne baya cikin abubuwan da zan iya yarda Jan”.

“Ke dai kawai ki ce, tsoron matan Yaya kike yi. Kina tsoron kiyi hadaka dasu, ki dinga challenging dinsu, suna challenging dinki, kina tsoron may be, you’ll lose…”. Ta fada cike da confidence, kamar tana da tabbacin abinda yasa nake gudun auren Yaya Bilal din kenan.

Nayi dariya da daga jin ta kasan bata kai zuci ba, nace “Jan kenan. Kin sanni sarai da tarar aradu da ka, sai dai wannan aradun tafi karfina, idan na dauketa tarwatsa ni zata yi. Maganin kada ayi, kada a fara. Gwanda in zauna a inda Allah Ya ajiye ni, kada in kai kaina inda zan hallaka!”.

Da alamun ta fara gajiya da kokarin sanya ni fahimta da take ta kokarin yi tunda zancen wannan ya taso, tayi kwafa, “shi yasa zaki gwammace ki cuci kanki kenan akan ki bi zuciyarki? ‘Cause let’s face it, kina son Yaya Hilal, ni nasan wannan. Yanzu kin gwammace akan wani dalili naki na daban, wanda ba na Allah da Annabi ba, ki tauye zuciyarki da rayuwarki?”.

Na daga kai na kalleta sosai, cikin girgiza kai, “baki san abinda na gani ba Jan, baki kuma dandana abinda na dandana ba, ba zaki taba fahimta ba… Ina kallo kiri-kiri ba zan jefa kaina inda nasan takaicin miji ko kuma na matansa ne zai kashe ni ba, ko kuma duka. Ba zan iya ba!!”. Na kara maimaita mata, don tasan cewa da gaske nake, kuma ba zan canza maganata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button