A ZATO NA COMPLETE

Duk da haushin Janan da naji ya ciko ni, hakan bai hana ni kwashewa da dariya ba, itama Janan ina ji ta saki dariyar. Nace “ji Fatsu don Allah, wai dan dukurkushi. Idan baki son mutum bai kamata ki bata mishi suna ba wallahi”.
Ta dauki zaren da take saka dashi ta jefe ni dashi, “gidanku! Wato ke abin dariya ma ya baki kenan? Bari dai ki ga…”, ta komawa neman wayarta, tana ganinta ta mikawa Janan ita, “yauwa yar nan lalubo min Mudan ki kira shi, ce mishi yazo yanzu-yanzu”.
Dan halas din, kafin Janan ta ma lalubo lambar shi, sai gashi ya kwaro sallama ya shigo. Fatsu ta ware hannuwa kamar wadda zata rungume shi, na hau danne dariyar data taso min despite haushi da tsoron abinda zai je ya dawo daya cika min ciki. Fatsu ta harareni, ni kuma na harari Janan. A raina ina saka kalar rashin kirkin da zan mata idan muka samu muka kebe. Wato da biyu tazo Gashua kenan? Zata yi bayani ne.
Yaya ya samu waje ya zauna, shima dai cike da murmushi da kuma mamakin dabiar Fatsu a daidai wannan lokacin.
Yace “me yake faruwa ne anan?”.
Fatsu ta gyara zama, “dama kiran ka nake kokarin yi yanzu. Kaji-kaji abinda yake faruwa”.
Ta zauna ta zayyane mishi magana da halin da muke ciki da Yaya Bilal yanzu, babu ragi babu kari. Yaya bai ce komi ba tunda ta fara maganar, har ta direta.
Sannan yace, “ni dama nasan da walakin wai goro a miya, nasan tunda ta turo wani akan yazo ya ganmu kamar daga sama, nasan da wata a kasa. Ke yanzu a tunaninki hakan shine daidai a gareki? Ba zaki yi tunani wanda zai fissheki ba Na’ilah?”.
Na turo baki gaba, “to ni Yaya wai nace muku ina son shi ne? Abun ai sai yayi min yawa, wai shege da hauka. Da wanne zan ji ne? Da rashin so ko kuma zama da kishiyoyi?”.
Yaya ya kama baki, “ni kike fadawa haka Na’ilah? Lallai wuyanki yayi kauri da yawa. To bari kiji in gaya miki, idan ke idanunki a rufe suke, mu namu a bude suke tar, kuma babu ta yadda za ayi muna kallonki ki bi hanyar da bata dace ba kin ji na fada miki…”.
Ya hau fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, daga karshe dai ya kare da, “.. don haka tun ma kafin magana tayi nisa, ki sallami mutumin nan. Mu dukanmu hankulanmu basu kwanta dashi ba, balle me ma zaki yi da mutum mai auri saki? Kina da tabbacin zai tsaya ne a kanki? Ga responsible mutum irin Bilal? Dan gidan mutunci da karamci, wanda kuma muka sansu suma suka sanmu?”.
Gabadaya haushi yazo ya dabaibayeni wai me yasa ni ba zasu duba dalilina ba, zasu dinga concluding rayuwata kamar idan nayi auren su ne zasu yi min zaman auren ba ni ba? Na tashi zan wuce daki da sauri ina gunguni har da buga kafa a kasa.
Yaya ya daka min tsawa data gigita ni, tunda nake dashi ban taba jin yayi makamanciyar ta ba, musamman wa ni. Yace “dawo nan ki zauna Na’ilah tun kafin ranki ya baci wallahi!”.
Ba shiri na koma inda nake zaune na zauna, hawayen da nake kokarin dannewa suka shiga zarya akan kumatuna.
Yaya ya kama baki, “ikon Allah! Kuka kuma kike yi? Lallai kin samu waje da yawa. Akan wannan yaro ne kike nema ki bata mana rai, me kika gani a jikinshi?”.
Fatsu tayi caraf ta tare shi, “ni anya ma ba tsaface ta yayi ba? Naji ance wajajen nan sun kware wajen bin malamai”.
Babu wanda ya tanka mata a tsakaninmu, Yaya ya cigaba da cewa “ni ba zan takura ki ba Illo, amma Allah ya gani zamu yi iyaka bakin kokarinmu. Amma tunda ke kina ganin hakan yafi miki, to sai kije kiyi tayi, babu wanda zai sake damunki. Sai dai ko mai zai faru, kiyi kuka da kanki”. Ya tashi yana kakkabe jikinshi ya kalli Fatsu, “ni zan wuce gida Inna, sai da safenku!”.
Tace “to Mudan, a gaida su yan biyu”. Yasa kai ya bar gidan. Ya barni a zaune ina share hawaye.
Yana fita Fatsu ta juyo kaina, “wannan taurin kai naki, ban san daga inda kika kwaso shi ba. Ni dai duk tarihin danginmu babu mai taurin kai wallahi, balle kuma mahaifiyarki. Mace mai saukin kai, hakuri da ladabi da biyayya. Allah ya kyauta miki”. Ta tashi ta hade kan kayanta ta shige daki.
Ni da Janan muka cigaba da zama a wajen, cikin ni da ita babu wanda yayi magana. Har na gama yan koke-koke na na share hawayena. Sai dana gama sannan ta kalleni, tace “kiyi hakuri, banyi zaton abin zai kai haka ba wallahi. Tambayata tayi, ni kuma I was just carried away, amma banyi da niyya ba”.
Nasan halin Fatsu sarai da bugun ciki da iya manipulating, nasan kadan daga cikin aikinta ne. Amma ban tanka mata ba, nima tashi nayi na fada dakin, nayi shirin barci na kwanta abina.
*
Wato tunda nake zuwa Gashua, ban taba zuwan da bai yi min dadi kamar na wannan karon ba. Gabadaya Fatsu da Yaya sun dauke min wuta, kai hatta da Malam sai in ga kamar shima dai ya daina kula ni. Duk da cewa bai fito fili yayi min maganar ba, amma ta cikin hira da nasiha yakan sako zancen cikin dabara irin tasu ta manya. Shi yasa naji gabadaya na takura. Tunda farar safiya muke saka kafa mu bar gidan ni da Janan da muka shirya da ita a washegarin ranar da abin ya faru, ba zamu dawo ba kuwa sai dare yayi. Ta yadda da mun dawo, babu lokacin zama hira, zamu nemi makwanci.
Ranar Lahdi na zagayowa kuwa, yadda kasan na sauka daga kan kaya haka naji lokacin da muka fita daga garin Gashua. Nasan yanzu sai a hankali, sai nayi kokari sosai kafin in samu in shawo kan Fatsu da Yaya. Da wannan kudirin muka isa Zaria.
Cikin yan kwanakin kuwa na samu na shawo kansu din da kyar, duk da cewa har yanzu dai da suna dan tado min maganar musamman ma dai Fatsu, amma dai hakan yafi da.
Bamu yi cikakken sati uku da dawowa ba, muka tafi gida hutun sallah.
*☆⋆31⋆☆*
Komawata wannan karon naga alamun canji sosai a gidan. Misalin yadda na samu Anty Alawiyya cikin fara’a da walwala, tana ta shigi da ficinta cikin annashuwa. Su Ramata kuma ana zaune a kofar daki, an coge daurin dankwalin nan an kawo shi goshi, ana ta zubda ruwan habaici da bakaken maganganu kamar wata jikar mahauta.
Nayi sallama na shiga gidan, hannuna dauke da Auwal da muka hadu dashi a waje, sun dawo daga makarantar islamiya, ya gudu ya baro sauran. Anty Alawiyya ta amsa min sallamar da nayi cike da fara’a, tace “a’ah, mutanen Zaria ne? Sannunku da zuwa, ai bamu da labarin kuna kan hanya”.
Nayi dan murmushi ni kuwa tare da gaidata, ta amsa tare da shigewa dakinta. Na juya na gaida Ramata, yau ko albarkacin amsa gaisuwar ban samu ba, ta cune baki waje daya, ta dauke kai daga kaina ta maida shi gefe. Na tabe baki na ciccibi akwatina na fada daki Auwal yana bina a baya.
Dakin a share a kimtse, abin har ya bani mamaki. Maryam dai ba irin masu son yin gyaran nan bane, saboda haka zuwa in ga daki a share a goge, yana kamshi, abin mamaki ne da tambaya.
Na zuge jakar hannuna na ciro cakuletin dairy milk dana siyo ledar guda saboda yara, na dauki daya na ba Auwal. Ya karba ya fita waje a guje, nasan sauri yake ya tari yan uwanshi ya basu labari. Nayi murmushi ina girgiza kai tare da tashi na hau cire kayan jikina.
Ina nan sai ga Alawiyya da gorar zobo da kunun aya, tace “ga mai dan sanyi ki kora kafin mu gama abinci, yanzu aka dora amma ba mai wahalar damuwa bane”.
Allah sarki, sai naji abin wani banbarakwai. Duk da hakan bai hana ni jin dadin hakan ba, ko ba komi kasan cewa wani ya damu da kai a cikin gidannan, abin jin dadi ne da alfahari.
Na kai hannu na karba cikin murmushi, nace “babu komi ai, na ma ci abinci ai kafin in taho. Nagode sosai”. Bata ce komi ba ta juya ta bar dakin.