A ZATO NA COMPLETE

Bayan kwana uku da kai kudin, na tattara na koma Zaria abina. Na hadu da angona to be, muka fara shirin yadda zamu gudanar da bikinmu. A gefe guda kuma na maida hankalina ga karatun exams din dake gabatomu nan da dan kankanin lokaci.
????????????????????
*☆⋆32⋆☆*
Kwanci tashi kamar yau ne a wajen Allah. Gashi har yau ya rage mana sati daya kacal mu gama da karatunmu gabaki daya. Hakan kuma yake nufin nan da sati biyu masu zuwa zan amarce. Kowa ya ganni a cikin irin wadannan lokutan, ya ga ‘a walking zombie’. Kama ce ba wadda ake zaton gani a jikin amarya ba, amarya daya kamata ta zama mai kazar-kazar, da doki, da komi ma kai, ni kam komi nawa ya zama babu laka a jikinshi. A kowace matsowar rana, ji nake dama kara ranakun ake yi ba rage su ba. Amma babu wanda na ba wannan labari, na kama bakina na dinke babu wanda ya sani. Nasan duk wanda yaji kalar tashin hankalin da nake ciki, wanda babu wanda ya jefa ni ciki sai ni kaina, zai kira ni banza, sakara, kila ma har su kara da wadda bata san ciwon kanta ba. But I know better.
Kullum excuse dina daya, wanda nake kara ba kaina, cewa hidimomi ne suka yi min yawa ba wani abu ba. Zan wartsake, zan dawo daidai, abinda nake yawan ambatawa kaina kenan. Kodayake, naji ance dama yawanci haka amare suke ji idan aurensu yana gabatowa. Don haka it’s normal.
Da Janan muke ta shigi da ficin harkar bikinnan, tayi ruwa tayi tsaki kamar yadda yakamata tayi, duk da cewa itama nata bikin nan da watanni hudu ne masu zuwa. Kasancewar Almunta ya tafi wani course kasar Germany na watanni biyar yasa aka saka ranar auren tasu bayan ya dawo da sati biyu.
Duk wasu shirye-shirye mun riga mun yi su. Rabon IV, daga gida Katsina, zuwa nan Zaria da kuma Gashua, duk wanda yakamata ya samu ya samu. Haka anko, kai da dai duk abinda ya dace, munyi sai sauran abinda ba’a rasa ba.
Yau muka zana jarabawarmu ta karshe a cikin Shika, nan da kwanaki uku zamu yi practicals din exams din, daga nan zamu yi induction, kamar graduating ne a wajen nurses ko kuma in ce oath-taking. Idan muka yi shi, za’a bamu nursing license dinmu, daga nan kuma zamu yi applying internship a inda muke so.
Bayan mun fito daga jarabawar, a gajiye muka koma dakina ni da Janan. Muka zube akan katifa muna ajiye numfashi da maida labarin yadda jarabawar ta kasance mana.
Saboda tsabar gajiyar dana kwasa cikin yan kwanakin nan, ban san lokacin da barci mai nauyi ya kwashe ni ba.
Kafin in tashi har Janan ta dafa mana jallop macaroni, lokacin dana tashi na gansu ita da Esther suna hira. Nayi mika tare da tashi zaune ina binsu da kallo, Janan ta kalleni “ki tashi ki wanko baki ki zo ki ci abinci. Ki gama muje wajen masu dinkin wancan mu gani idan sun gama mu amso”.
Na tashi tsaye da kyar, ina jin jikina kamar an nada min dukan tsiya. Na dauki kettle na fita waje na daurayo bakina, na dawo na zauna a inda plate din abinci yake jirana. Na janyo abincin cikin mutuwar jiki na fara ci, ina ji suka ci gaba da hirarsu akan wajen da zasu je suyi nasu internship din, ita Janan a Kaduna zata yi, ita kuma Esther anan Shika zata yi. Nima dai nasan Shika dinne, don mun riga munyi maganar da Dr., ina karbar license dina zan mika mishi, zai yi applying internship din da kanshi anan Shika din.
Daga baya kuma sai hirar ta gangaro kan abinda zasu yi da abinda zasu saya idan suka dauki albashinsu na farko. Ina daga gefe ina jinsu, sai dai inyi dariya idan sun fadi wani abin daya bani dariya. Ko kuma in girgiza kai da jin absurdity din abubuwan da suke fada.
Ina gamawa, na maida kwanukan gefe. Esther ta jefo min wayata, nayi sauri na cafe. Tace “hubbynki ya kira lokacin da kike barci”.
Na jefa mata harara cikin wasa, “shine kuma sai yanzu kika ga damar fada min? Kina so hankalin mijina ya tashi ne ko me?”.
Ita da Janan suka yi dariya, tace “come on mana, nasan dana baki wayar nan daga tashinki daga barci, ba lallai kici abincin nan da wuri ba. Ko baki ga kokarina bane?”.
Na daga baki zan bata amsa, aka amsa kiran dana dannawa wayar Dr., don haka na rufe bakina tare da kara wayar a kunne.
Tun kafin inyi magana ya riga ni, daga jin shi cike yake da doki da farinciki, “hey, guess what?”.
Yanayin yadda yayi maganar kanshi ma, kasan cewa wani abu ne babba kuma muhimmi ya same shi, don haka naji na saki murmushi ba tare dana shiryawa hakan ba, nace “me ya faru ne?”.
“Tafiyar nan fa ta samu, nan da sati biyu! Oh God!! I can’t really believe this is happening!!”. Ya karasa fada cikin karajin murya.
Naji na balle da murmushi nima kamar lebuna na zasu rabe biyu. Wani course ne asibitin zasu tura manyan doctors na department din su biyar kasar London duk bayan shekaru biyu, course ne na shekara biyu. Yace idan kaci sa’a, idan can asibitin da kaje yin course din suka ga kwazon ka, zasu iya daukar ka aiki kamar yadda suka dauki likitocinsu biyu aiki wadanda suka je waccan shekarar. Idan kuma baka samu aikin a can ba, idan ka dawo, zasu kara maka matsayi da kuma albashi anan. Wannan ba ma shine abin birgewar kadai ba, idan ka tafi can asibitin zasu dinga biyanka albashinka, su baka wajen zama, haka babu ruwanka da biyan kudin makaranta idan kaje. Tsarin shine, idan ka tafi yanzu, zaka yi wata takwas a makaranta kana daukar darasi abinka, a hakan ma kana da albashinka a hannu, bayan ka gama da nan zaka koma asibitin kayi aiki dasu na watanni goma sha biyu. Daga nan kuma sai su yanke shawarar yadda zasu yi da kai.
Yace min yanzu sau uku kenan yana applying ana hana shi, wannan karon ma kwata-kwata ya cire ranshi daga samu, sai kuma gashi yanzu babu zato babu tsammani, ya samu din.
Nace “Masha Allah, Alhamdulillah! Kai amma naji dadi wallahi, Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya albarkaci aikin wannan”.
Yace “ameen ameen amaryata. Ni har na rasa wace kalar murna ma yakamata inyi, ji nake kamar mafarki nake yi!”.
Na saki yar dariya, “right! Kawai ka kalli alkibla yanzu, ta nan kadai zaka nunawa Allah godiyarka. Idan ka bar nan kuma, sai kayi sadaka”.
Yace “haka ne, nagode dear. Bari in tafi yanzu”.
Na girgiza kai fondly, wani lokacin kamar yaro haka yake gudanar da dabi’un shi, wasu lokutan ya baka dariya, watarana kuma takaicinshi ya cika maka ciki kamar kayi me.
Wani tunani ya darsu a raina, nace “to amma ya zamu yi ne? Bikin ma nan da sati biyu ne, kenan hakan yana nufin tare zamu tafi kenan?”.
Ya danyi jim, zuwa can yace “har yanzu ina kan wannan tunanin ne. Yanzu zan shiga gida in sanar dasu, zan kira ki zuwa anjima”. Nace mishi “to ka gaishe dasu Hajiya”. Yace “zasu ji”, ya kashe wayar.
Na bi wayar da kallo, ko menene abin yin tunani a cikin wannan maganar? Na tabe baki tare da daga kafada.
Su Janan da tunda muka fara wayar suka katse hirarsu suke kallona jifa-jifa, suka zubo min idanu, na kallesu cikin murmushi, “dudes, London ta kira mu yanzun nan!”.
Habawa, suka saki ihu da shewa tare da fadowa kaina, sai da muka fadi kasa.
Janan tace “da gaske?!”.
Esther kam, “Oh my God!” Kawai take fada tana nanatawa.
Sai da suka gama ihun murnarsu sannan Esther ta tashi zaune, muma muka tashi. Janan ta sake sarkafo hannunta ta rungumo ni, “Na taya ki murna wallahi dear… Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Yanzu sai kiyi tafiyarki ki barni?”.