A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

Nayi dariya, “sis, maganar fa bata tabbata ba. Ni fa ina assuming abubuwa ne kawai”.

Ta kai min duka a kafada, “maganar banza kenan! Ke yanzu kina tunanin zai tafi ya barki anan har na tsawon shekaru biyu? Wasa kenan. Balle ma, su da ana basu gidajensu acan, ai babu ma wani dalili da zai hana mu zuwa kai amarya kasar London”. Ta kyalkyale da dariya bayan ta gama fadin haka, ni da Esther muna taya ta.

Sai wajen karfe biyar na yamma sannan muka fita zuwa amsar dinkin. Har Esther muka tafi. A hanya Janan take tambayata, “su fa kayan lefen da ba’a kawo ba har yanzu, ya za ayi dasu?”.
Na kalleta, “ke da kika san zamani ya canza, yanzu lefe da zaki ga har ana saura kwana biyar daurin aure ba’a kai ba. Balle shi fa yace kamar haka al’adar gidansu take, sai bayan aure ake kai kayan lefe”.

Janan ta jinjina kai, “haka ne. Mu dai ya taimaka ya kawo kafin mu kaiki, idan haka ne, bamu da damar daukar turamenmu kenan”.

Na kai mata duka ina dariya, “ke fa baki da M wallahi, wawashe min kayan zaku yi kenan?”.
Muna wannan hirar har muka fita waje, muka hau bus zuwa inda muka kai dinki.

Dancing Banana, nan ne wajen da muka kai dinki. Duk da wasu kayayyakin suna can Katsina, Maryam ta kai min su, kai wasu ma suna Kaduna. Wadannan wadanda Ummahn su Janan ne ta bamu, manyan atamfofi guda biyu iri daya, da wani lafiyayyayen yadi ni da Janan din. Da kanta ta kai dinkin, namu kawai tura measurement dinmu ne.
Wadanda muka kawo nan, wanda angon ne ya kawo, tunda ba’a riga an kai lefe ba. Na Katsina kuma, wanda muka fitar ne a matsayin anko.

Kai tsaye wajen wanda yake mana dinkin muka wuce, muka samu ya dinka kala na mutum daya, na dayan kuma ya yanka bai dinka ba. Esther ta fara fuming, dama ita ta hada mu dashi, “yanzu kana nufin kusan sati biyu wai har yanzu baka gama mana dinkin ba? Mike meye hakan wai?”.

Yace “na fa yi kokari, yanzu haka aikin wata na maida gefe nayi wannan din fa. Nayi alkawarin nan da kwana biyu zan gama muku, kin san bama yin haka dake Esther”.

Muna nan tsaye, sai ga Haleemo a gabanmu. Bata ko yi acknowledging dinmu ba, ta hau zazzagawa mai dinki masifa. Apparently, ita ce wadda ya ture dinkinta dake kan layi ya mana namu. Tun yana bata hakuri, har shima ya hau sama ya fara zuba mata tata kalar masifa, mu kam muka koma gefe muna kallonsu.

Ta ja tsaki, “matsalarku kenan dama wallahi, ku kwata-kwata baku san mutumci ba. Su waye suka fito da martabar wannan shagon idan ba mu ba?”.

Yace “ke kada fa ki kawo min rainin wayau nan wajen. Kada ki manta ko wancan dinkin dana miki, baki cika min kudina ba. Wannan ma kika wani ciccibo kaya kika kawo min babu ko sisi, an gaya miki ni din bawanki ne wai?”.

Sai lokacin ta kallomu, ta fara borin kunya, “to ni nace ba zan baka kudin ka bane? Kada ka wulakanta ni a gaban mutane mana!”.
Ni da Janan muka danne dariyar data ke neman subuce mana.

Shi kuwa Mike yayi dan tsaki, “whatever, kin san ni bana irin wadannan tone-tonen. Su ma don dinkin aure ne shi yasa ma na ajiye nakin gefe guda”.
Ta kallemu ido a zare, “aure zaku yi?”.

Nayi murmushi nace “eh”.
Tare da bude jakata na dauko iv na mika mata, ta amsa ta karanta. Tace “to Allah ya sanya alkhairi”. Muka ce ameen.

Bayan mun tabbatar da cewa zuwa jibi zamu dawo mu amshi dinkin mu, muka tafi muka bar su suna cigaba da sa’insar su.

A kofar wajen, muka samu Umar tsaye a jikin motar shi, da alama budurwar tashi yake jira. Muka yi kallon-kallo dashi, muka zagaye shi muka wuce abinmu ba tare da wani yayi magana ba. Janan gida ta wuce, ni da Esther kuma muka koma cikin asibiti.

Muna shiga daki sai ga kiran wayar Janan, wai Anty Sarah tayi yar diyarta kamar Mimah. Na mata fatan samun sauki da barka muka yi sallama.

Ranar juma’ah muka yi induction dinmu, bayan an rantsar damu, mun karbi nursing license dinmu, aka shiga shagalin ciye-ciye da shaye-shaye. Allah kadai yasan irin farincikin da muke ciki a wannan ranar. Duk da cewa convocation dinmu nan da satika biyu ne, amma kuma induction ya ma fi muhimmanci ga nurses nesa ba kusa ba. Yinin ranar guda, kira ne kawai yake shiga yana fita daga wayata, sakonni na taya murna daga yan uwa da abokan arziki.

Da yamma bayan mun gama shagalin, ni da Janan muka dauki hanya zuwa barka. Kasancewar gobe asabar zan wuce gida. Gashua zan fara zuwa inyi kwana biyu, sallama da yan uwa da abokan arziki, sai in wuce Katsina daga can.

Napep din da muka hayo daga bakina titi yayi parking a kofar gidan, muka biya shi, sannan muka fita daga ciki.
Na daga kai na kalli gidan da kallo, yan kadan daga cikin memories dana tara a gidan, suka dinga flooding suna shiga cikin kwakwalwata. Na girgiza kai a hankali, ina kokarin shaking din komi daga cikin kaina.

Ni da Janan muka shiga gidan, bayan mun gaisa da maigadin gidan. Kai tsaye dakin Anty Sarah muka wuce. Da yake yamma ce, babu cunkuson mutane sosai. Muka gaisa na mata barka, ta amsa tare da min godiya. Yanayin yadda take fara’a da tambayata bayan rabuwa, sai kayi tunanin irin mun saba sosai dinnan ne.
Aka miko min diya na amsa, kamar yadda Janan tace, kamar su daya da Mimah babu banbanci. Na kura mata idanu ina kallo kamar in sude ta saboda birgewa. Yadda ta nade cikin towel din da aka nadeta a ciki, kamar irin magen nan sabin haihuwa, very adorable.

Mun jima sosai dasu ana yar hira, ba karamin mamakinta ta nuna ba akan maganar aurena da taji ba. Musamman ma da wani, ba… Bata karasa ba, naji Janan tayi saurin ta katse mata maganar. Na bisu da kallon mamaki, ban tsaya tambayarta wa take nufi ba, duk nayi zaton da Umar take, don haka na share maganar don nima bana son tuni akan irin rayuwarmu da Umar, da irin cin amanar da yayi min.

Ina shirin tashi da niyar yi musu sallama in tafi, kawai naji tashin sautin muryar data matukar rikitar dani. Da sauri na koma cikin kujerar dana fara tashi dabas, wata irin rawar jiki ta ziyarce ni. Ba shiri na fara janyo salati da hailala ina ja ina karawa a cikin raina.

Yaya Bilal da Yaya Jameel suka shigo cikin falon. Yaya Jameel sanye da casual jeans and T-shirt, yayin da kamar kodayaushe, Yaya Bilal yake sanye da shadda ruwan sararin samaniya, rataye a kafadarshi ta dama, brief case dinshi ce, da alamu dawowarshi kenan daga wajen aiki.

Suka samu waje suka zauna, kallon nan daya dana musu, ban sake daga kai na kallesu ba. Falon daga mu, maijegon, sai kuwa wata makociyarsu Ikilima data shigo bayan mun shigo muma.

Ina jin tashin muryarsu suna gaisawa da mutanen falon, nasan nima dole ne in gaida su.
Na daga baki da kyar na gaida su, ba tare dana iya daga kai na kallesu ba. Tashin muryar Yaya Jameel kadai naji ya amsa, hakan yasa naji jikina ya kara yin sanyi.

Ko lokacin da Janan ta karbi diyar daga hannuna da niyar mika musu, ban iya daga kaina ba.

Na yan wasu lokuta, dakin ya dauki shiru, babu motsin abinda kake ji, sai tashin muryar Yaya Bilal kawai da kake ji yana tashi, yana yiwa jaririyar addu’o’in tsari da kariya kala-kala.

A lokacin ne na samu na iya daga kaina a hankali, na saci kallon inda Yaya Bilal din yake zaune dauke da yarinyar. Rabon da in saka shi a cikin idanuna ko kuma inji muryarshi, run rana daya tsare ni a hanya a asibiti da kuma lokacin da muka yi waya dashi ta karshe.
A yanzu da nake kallonshi, yadda ya rike yarinyar nan a hannunshi kan-kam, kamar wanda yake tsoron wani abu ya faru da ita. Tsananin soyayya da zaka gani a cikin idanunshi, tsantsar adoration da wani irin hope, hope wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunshi, ya sanya naji wani matsi a cikin zuciyata har sai da naji kwalla ta cika min idanu. Ba zan iya jurar wannan abu ba, na zabura na tashi tsaye da sauri, har wayata da take kan cinyata ta fadi. Nayi sauri na wawureta tare da sungumar jakata na rataya, na kalli Janan da Anty Sarah da suka bini da kallo cike da mamaki.
Nace “zan tafi ne, Anty Allah ya raya baby, Janan, sai mun hadu ko?”. Anty ta amsa da ameen, Janan kuma ta matso kusa dani da niyar taka min zuwa waje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button