A ZATO NA COMPLETE

Nayi shiru ina sauraron yadda yake maganar a zafafe, daga ji babu tambaya a matukar fusace yake, dani ko kuma wani.
Naci gaba da shesshekata har da jan majina, yace “ni yanzu haka Zaria zan wuce abina, zan je in fara shirin inda za’a sauke ki. Don haka kina da sati daya, daga yanzu zuwa rana irin ta yau, ki gama yanke shawarar yadda zaki yi, aure tsakaninmu dai ya dauru, babu kuma wani mahaluki da zai sanya ni datse shi, don haka you might as well take heart, shawarata a gareki kenan”.
Ya mike yana gyara link din hannun rigar shi, “duk abinda kike bukata, zaki iya kiran wayata, ko kuma ki fadawa Janan, zata fada min. Sai anjima!”.
Yasa kafa ya fita daga fadin haka, babu ko waiwaye.
I was too shock, ko hannu na kasa motsawa balle gangar jikina. Baki a dage, ido a bude akan kofa, haka su Janan suka shigo cikin dakin suka sameni. Wato ni za’a nunawa attitude? Lallai kuwa.
Janan ta fara tarkata mana kayan da aka baza a dan lokacin, likita ya shigo ya kafa min dokar cin abinci da samun barci isasshe. Ni dai jinshi nake yi, ya gama dogayen bayananshi, ya sallame mu muka kara gaba.
Da yake clinic din anan cikin unguwarmu yake, a kafa muka karasa gida.
Zuwa lokacin kowa yaji labarin yadda daurin aurena yazo da canjin yanayi, kuma canjin ango. Nan da nan mutanen da suka yi saura suka rufa a kaina da kalmomin ‘sannu, ya jiki? Ashe abinda ya faru kenan? Sai ayi ta hakuri, Allah ya nufa shine mijin’, wasu kuma har su kara da ‘ai dama naji ance kun yi soyayya dashi, abin ya kwana gidan sauki ma’, da dai sauransu.
Muka samu muka yakice su da kyar muka shige can kuryar dakin Anty Alawiyya, Allah yasa babu mutane sosai.
Na zauna a gefen gado, Maryam ta tafi nemo min abinda zan ci in sha magungunan da aka bani, Janan kuma ta zauna a gefena.
Nace mata “me ya faru da Dr. Ne?”. Babu wanda naji ya sake tado zancenshi, ga yanayin yadda suke nunawa kuma, basu da alamun yi mun bayanin abinda ya faru.
Ta tabe baki, “hmm, mutuminki ba sai suka shanya yan daurin auren ba? Tun ana jira har aka gaji, babu wani dangin ango da aka gani a wajen daurin aure. Yaya Jameel ne da yazo daurin aure ya kira wani abokinshi yaje har can gidan su angon ya tambayo ko lafiya? Zancen da nake miki, ashe bawan Allah ya kwana ya huce a kasar London, ya bar sakon a gaya miki yana miki fatan alkhairi, amma idan kinga zaki iya jiranshi nan da shekaru biyun, to babu damuwa. Amma a halin yanzu ba zai iya daukar hidindimu masu yawa ba, liability yace. Shine su kuma cikin wadanda ya barwa sakon, daga abokai har yan’uwa, aka rasa wanda zai iya tako kafarshi yazo yayi bayani a mutunce kamar yadda aka faro a mutunce. To ana shirin sallamar mutane ne a basu hakuri, Yaya Jameel yace ba za’a yi haka ba, tunda an san da manemi a gida, ai kawai yazo ya biya sadaki, shine fa aka daga daurin auren zuwa yamma yadda Yaya Bilal yazo ya samu daurin auren”.
Na jijjiga kai cikin sanyin jiki, wato har zabata aka yi akan abin duniya, aka kuma kirani liability? Allah kenan. Shi kuma Yaya Jameel, apparently shine makasudin jefa ni cikin ha’ula’in da nake ciki yanzu kenan?.
Janan ta dafa kafadata, “meye na wani abin damuwa anan? Ai in gaya miki ki kwantar da hankalinki Hajiyata, ki je ku kwashi soyayyarku wallahi. Shima Yayan fa ba karamin dace yayi ba, naji ance kusan mutane hudu suka nemi aurenki a take a lokacin”.
Na ciza lebe kawai ban ce mata komi ba. A haka Maryam ta dawo ita da Kulsum, da kwanon abinci a hannunta. Haka nan saboda damun da suke yi min, na tuttura abincin ba don ina so ba. Kafin in gama an kira sallar magriba, duk muka yi harama suka yi.
*
Zuwa washegari gidan ya baje da yan biki, sai yan daidaiku da zasu tafi washegari. Shima Yaya Mudatthir a ranar ya juya. Janan tana makale a gefena, bana lekawa ko nan da kofar gida sai na sha fada da mita kamar itace mijin gabadaya.
Sai da safe dana je gaida Baba, sannan yayi min bayanin halin da ake ciki. A raina nace ‘ihu bayan hari kenan’. Ya nanata min nan da sati daya za’a tafi dani, in shirya, nace mishi to.
Anty Halima taci gaba da zama damu, wani sabon gyara suka fara min ita da Anty Alawiyya babu kakkautawa. Anty Alawiyya ta kan ce, “zama cikin mata biyu musamman hamshakai yadda naji ana bada labarin matan mijin nan naki sai an dage Na’ilah. Don haka ki dage, ki kama kanki, ki taimaki kanki kafin ki zama saniyar ware”.
Abinda bata sani ba shine, maganganun nan nata babu abinda suke kara min sai tashin hankali da taraddadi.
Wasu lokutan kuma haka zata zaunar dani tayi ta min nasihohi da maganganu, salo iri-iri na kissa da kisisina har mamaki take bani wani lokacin. Sai dai bana bin abinda take fada ko daya, kawai jinta nake yi. Mijin da ba’a so, gidan da ba’a so, meye na koyan makaman zama dasu? A ganina fa kenan.
Cikin dan wannan lokacin ban sake ji daga angon nawa ba, babu kira, babu text, babu komi. Wani lokacin ina ji zasu dinga yin waya da Janan, ya tambayeta ya nake, ko kuma akwai wata matsala ne? Haka zasu yi wayar su gama ya kashe, babu ko sakon gaisuwa.
Hakan ba karamin kona min rai yake yi ba, a ganina tun ma kafin aje ko’ina ya fara wulakanta ni, ina ga yaga na shiga gidanshi? Nima sai na shaka fiye da yadda yakamata, nayi watsi da al’amuranshi. Tashin hankalin da nake ciki ma baya barina tunanin wulakancin da yake yi min.
Kwanakin sai suka dinga wucewa kamar a cikin kiftawar ido da bismillah, kafin in ankare, lokacin barina gida yayi.
*☆⋆34⋆☆*
Kafin zagayowar ranar tarewata, sai dana zama kamar wata matar Malam. Kullum ina fama da carbi da doguwar hijabi a jiki ina ja, cikin dare zan tashi tun daga farkon dare har karshen shi, washegari in tashi da azumi a bakina, addu’a daya ce nake yi ina maimaitawa; ‘gidan Yaya Bilal, Allah ka tsareni da shiga wannan gida, Allah kamar yadda ka raba gabas da yamma, Allah ka raba ni da shiga wannan gida’.
Sai dai a kwana na biyar, dole na gama saddakarwa, na fara addu’ar neman ceto da taimako saboda babu alamu ta ko’ina mai nuna cewa zuwana gidan Yaya Bilal zai fasu. Ranakun kullum kara matsowa suke yi, hakan kuma yake kara saka ni cikin tsananin damuwa. Watakila dai karshen farin cikina ne yazo.
Tunda aka daura auren, na fara wasu irin mafarkai masu ban tsoro. Sai inyi mafarkin wata mata, fuskarta a rufe da bakin kyalle ta biyoni a guje da wuka a hannunta zata caka min, watarana sai inga nayi tuntube na fadi ta cimma ni, sai inga hannu ya zuro ya daukeni. Wani lokacin kuma haka zamu yi ta gudu, endlessly, babu kakkautawa. Haka zan tashi jikina sharkaf da gumi da zufa kamar an watsa min bokitin ruwa.
Don haka na dage kwarai da addu’a da kuma azkar, har su sadaka ban bari a baya ba.
Musamman Malam din su Kulsum, yayi rubutu ya kawo min ina sha safe da rana. Haka Anty Halima da Anty Alawiyya ma basu kyaleni ba, daga Gashua Fatsu ta aiko da sassake-sassake da magunguna iri-iri da addu’o’i, na lazimce su. Duk da cewa daga farko kin yin amfani nayi dasu, a wautata meye amfanin su to? After all, dama ba zaman gidan nake son yi ba.
Anty Alawiyya ce ta saka ni a gaba da fada da nasiha don ita Anty Halima cewa tayi ta gaji da lallashina, ta koma gefe ta kyalemu.
Anty Alawiyya tace “ke sakara ce wallahi, kina yin abu kamar wadda bata san abinda duniya ke ciki ba, ko kuma baki je kinyi karatun zamani ba. Don kina da kishiyoyi sai me wai? An gaya miki karshen duniya ne yazo? Ki shiga cikin kishiyoyi, ku buga ke dasu aga wadda zata sace zuciyar mijinta ta hanyar da manyan matan annabawa suka bi suka kwace zuciyoyin mazajensu, sai ki zama zara wadda tayi zarra. Amma ki zauna a gefe kina bata ranki a banza, wannan ai aikin kawai ne. Me zaki karas nan gaba?”.